Marigayi Malami Buwai yana gaisawa da Marigayi Sani Abacha

Daga Sani Ibrahim maitaya

Tsohon ministan harkokin noma Dakta malami Buwai ya rasu da yammacin yau Litinin bayan yayi fama da doguwar jinya.

Dakta Malami wanda ya yayi ministan harkokin noma a lokacin janar Sani Abacha a shekara ta 1994, ya rasu da yammacin nan ne a garin shi na haihuwa Gusau, babban birnin jahar Zamfara.

Ya rasu ya bar mata daya da ‘ya’ya goma sha biyar, da jikoki guda goma. Daga cikin ‘ya’yan shi akwai Alh. Shehu Malami wani dan kasuwa.

A cewar wani makusancin margayin Alkali Aliyi Dan Daaba, ya ce an rufe gawar margayin ne a wata makabarta dake cikin garin Gusau, bayan sallar jana’izar wadda babban limamin masarautar Gusau Liman dan Alh. Sambo ya jagoranta, kuma ta samu halartar gwamnan jahar Zamfara Bello Muhammad Matawalle, da manyan jami’an gwamanti, da kuma shugabanni addini.