Namiji sanye da kayan Mata

By A.B.Kaura

Jami’an tsaro a Kasar Senegal sun yi nasarar chafke wani Saurayi Wanda yayi Shigar Mata don ya Rubutawa Budurwar shi Jarabawar Kammala sakandare.

Shi dai wannan Saurayi Dan kimanin Shekaru 22 Dalibi ne a wata Jami’a dake Kasar a saka Kayan Makaranta (Uniform) masu launin Ja, na makarantar da Budurwar tashi ke rubuta Jarabawar Kammala Sakandare ya kuma daura Kallabi Ja don ya rubuta mata Jarabawar Darasin Turanci kasantuwar ba tada kwarewa akan turancin.

Matashin mai suna Khadim Mboup yace tsabar Soyayya da Kauna da ke tsakanin shi da Budurwar ne yashi aikatan hakan Wanda tuni yake tsare tare da Budurwar a hannun jami’an tsaro a yankin Diourbel da ke Kasar, kamar yada Majiyar Smarts News ta sheda mana. Ana sa ran za a gurfanar da shi a gaban Kuliya Gobe Alhamis, 5 ga watanOgustan shekara ta 2021 mai zuwa inda ake tuhumar su da Laifin satar Jinsi da satar Jarabawa.

An dai yi ta yada hotutan Dalibin Sanye da Mayan na Matan a shafukan sadarwa na Zamani.

Jaridar Smarts News ta samu rahoton cewar, an kama Dalibinne ne a ranar Assabar data gabata lokacin da Jami’in da ke duba masu rubuta Jarabawar ta Turanci ya fahimci akwai wani da ba dai-dai ba a irin yadda matashin yasa kayan makarantar a rana ta Uku da fara rubuta Jarabawar Kammala sakandare a MakaraDiourbel.

Hakan yasa yayi gaugawar kai rahoto ga yan sanda wadanda suka chafke shi kamar yadda mai Shigar da kara a Kotun Diourbel ya bayyana.