BY AMINU KAURA

Ana tuhumar wani Ali Ibrahim da lalata yarinyar ‘yar shekara 2 a cikin gidansa da ke unguwar Kwacham, a cikin yankin karamar hukumar mulkin Mubi dake jihar Adamawa.

Ali wanda ke sana’ar sayar da itacen girki, ya amsa cewa ya shigar da yarintar a dakinsa, ya kwantar da ita a kan gado ya kuma yi lalata da ita.

Bayanai sun bayyana cewa wanda ake zargi ya yaudari yarinyar wadda ‘yar makwabcinsa ce zuwa cikin dakinsa, inda ya yi lalata da ita.

Ya fadawa alkalin babbar kotun ta 2 a Jimeta cewa, bayan aikata laifin, ya raka yarinyar har zuwa gidansu, inda nan take mahaifiyar ta ta gano wani bakon al’amari a jikinta.

Ali yace mahaifiyar yarinyar ce ta sanarwa jami’an ‘yan sanda, inda nan take suka kama shi suka kuma gurfanar da shi a gaban kotu.

Shari’ar da Helen Hammajoda ke jagoranta, an dage sauraren ta zuwa ranar 27 ga watan Oktoba, kuma mai shari’ar ta ba da umarnin a ci gaba da tsare wanda ake tuhuma a gidan gyaran hali na Yola kafin zuwan ranar, domin cigaba da sauraren karar.