Allah Ya albarkaci wasu ma’aurata da samun ‘DA’ ba tare da hannaye ba, sannan yana da kaciyar shi, kuma yana dan da matsala ga kafafun shi waɗanda ke da farutta hur-hudu kowaccen su.

Mahaifiyar jinjirin mai suna Suwaiba Musa, ta bayyana cewa a watan farko da samun juna biyu ta yi ta mafarkin ‘ISKA’ (Aljani) mai ban tsoro, amma daga bisani ta daina.

Shi kuwa mahaifin Yaron mai suna Musa Muhammad ya ce bayan da suka ga wannan al’amari, sun hanzarta zuwa asibiti domin jin ta bakin likita, kuma sun ga likitan amma ya umarce su da zuwa asibitin dake sama da wannan.Da muka tambayi Malam Ahmad Umar kanoma akan abunda wannan lamari ke alamtawa, ya bayyana cewa wannan wani aiki ne na Ubangiji wanda yake aikata yadda yaso, kuma malammai sun yi maganganu kan yaron da aka haifa da kaciya cewa ko za’a sake yi mashi wata ko kuma a’a.

Sannan ya ja hankalin al’umma da idan aka samu irin wadannan ayoyin, a daina yin tururuwa zuwa kallo.

An dai haifi wannan jariri maras hannuwa a ƙauyen Dutsin gari na gundumar Kanoma karamar hukumar mulkin Maru dake jahar Zamfara.

– Sani Ibrahim Maitaya