Sakataren rikon kwarya na Jam’iyyar APC a jihar Zamfara yace jam’iyyar karkashin Jagorancin tsohon gwamnan jihar, Alh Abdul’aziz Yari Abubakar, (Shattiman Zamfara) ta saurari kalaman tsohon gwamnan jihar, Sanata Ahmad Sani Yariman Bakura inda yake cewa an soke Rijistar da akayima ‘ya ‘yan jam’iyyar a kwanan baya.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wani jawabi da aka fitar mai dauke da sa hannun sakataren rikon kwarya na jam’iyyar APC ta jihar Zamfara wanda a ciki yake cewa, “Jam’iyyar APCn a karkashin shugaban cin Hon. Lawal M. Liman, (Gabdon Kaura) batayi mamakin jin wadannan kalaman ba daga shi tsohon Gwamna Ahmad Sani Yariman Bakura ba idan akayi la’akari da irin fadi tashi da yake yi wajen ganin ya tarwatsa Jam’iyyar, ta hanyar raba kawunan ‘ya’yan ta domin biyan bukatar sa, shi kadai” inji Alh. Sani Musa Mafara.

Sakataren rikon kwarya na APCn yace “Kamar yadda Mai girma Shattiman Zamfara kuma jagoran jam’iyyar yasha fada, a lokuta daban daban na cewar, duk Dan jam’iyyar APC da yariga ya yanki rijista akwanan baya lokacin da aka gudanar da aikin a fadin kasa, to ko shakka babu bashida bukatar sake yin wata Rijistar”

“Wadan da ke wannan aiki a halin yanzu, sune masu yiwa dokar Kasa karan tsaye, domin kuwa ba sabon labari bane cewa Babbar Kotun tarayya dake Gusau, Babban Birnin Jihar Zamfara ta dakatar da kowane bangare, wajen gudanar da kowane irin al’amari na Jam’iyya, musamman aiki irin wannan da tuni an riga an kammala shi, har sai ta yanke hukunci kan Karar dake gaban ta gameda lamurran da suka shafi Jam’iyya” a cewar sakataren.

“Yana mai cewa, abin mamaki ne, mutane ‘yan kai kawo irin su Sanata Ahmad Sani Yariman Bakura sunyi fatali da wannan umurni na Kotun, suna kuma cigaba da gudanar da irin wadannan lamurra da Bahaushe ke kira ‘Aikin Banza yi wa Kare wanka’.

A saboda haka ne jam’iyyar take jawo hankalin al’umma, musamman fiyeda mutane 775,000 da suka yanki Katin Rajistar na Zama halattattun ‘yan Jam’iyyar APC, a Rumfunan Zabe 2516 dake Mazabar Kansila 147, a Kananan Hukumomi 14 dake fadin Jihar Zamfara, alokacin da wannan aiki yagudana Kwanukkwa da suka wuce, da sudauki wannan yunkurin da Sanata Ahmad Sani Yariman Bakura ke jagoranta a matsayin ‘ Aikin Baban Giwa’, su kuma kaurace masa, Domin a cewar shi, ba a Rajista guda biyu, kala daya, masu ma’ana daya a kowace irin halattacciyar mu’amala ta Jam’iyyar APC, “saboda ba Jam’iyyar ‘yan 419 bace, irin wadda Sanata Ahmad Sani Yariman Bakura ya saba da yiwa dillanci” inji Sakataren na APC

Haka ma a cikin jawabin, Sakataren na rikon kwarya na jam’iyyar ta APC yace wannan wani yunkuri ne na haddasa babbar hasara ga Jam’iyyar APC da ‘yayan ta a wannan jiha ta Zamfara, kamar yadda aka yi masu irin wannan kutunguilar da zakon kasa a zaben Shekara 2019.