Mai alfarma Sarkin Musulmi kuma shugaban majalisar koli ta harkokin addinin Musulunci Alh. Sa’ad Abubakar na ukku, ya umarci al’ummar musulmi da su fara dubon sabon watan Muharram shekara ta 1443 bayan hijira daga gobe Lahadi Ashirin da Tara ga watan Zul-hajji, wanda yayi dai-dai da takwas ga watan Ogasta, 2021.

Abubakar ya bayar da umarnin ne ranar Assabar a cikin wani bayani da shugaban kwamitin harkokin addini na majalisar mai alfarma sarkin musulmin Farfesa Sambo Wali Junaidu ya fitar, inda ya ce mai alfarma Sarkin Musulmin ya ce ranar Lahadi ita ce ranar farko ta dubon watan.

“Da wannan ake sanar da al’ummar Musulmi cewa ranar Lahadi takwas ga watan Ogasta wadda tayi dai-dai da ashirin da tara ga watan Zul-hajji, zata kasance ranar farko ta dubon sabon watan Muharram 1443 bayan hijira” inji shi.

A cewar bayanin, an bukaci al’ummar musulmi da su kai rahoton ganin watan a wurin uban ƙasa mafi kusa da su, domin sanar da mai alfarma Sarkin Musulmi.

Ganin watan Muharram din shi ne zai kawo karshen shekara ta 1442 bayan hijira.