Jaridar ” Smart News Nigeria” (mediasmarts.news) . Zata rik’a kawo mu ku dad’ad’an labarai na nishad’i ,ilimantarwa da fad’akarwa , domin y’an uwa mata .

Wad’annan k’irk’irarrun labaran mun shirya gabatar da su a kowace ranar Jumu’a da misalin k’arfe 3:00 na rana domin taya ku hira da cire muku kewa ,ta hanyar kawo muku rubuce-rubucen marubuta na zamani kama daga hausa har na turanci insha Allah.

wannan jaridarta “Smart News Nigeria” ta shirya tsaf domin nishad’antar da ku, da dad’add’an littatafan marubuta, koyar da sana’o’in mata, Girki, Gyaran Jiki da dai sauran su.

Idan kuma akwai wacce take da shawarwari da zata bamu ko kuma tana gabatar da littattafanta ana iya aika mana ta wannan address d’in email mediasmartsnews@gmail.com

kasancewar mata kanyi zaman kad’aici, ga tunane-tunane barkatai, wannan jaridar ta “Smart News Nigeria” ta ga ya dace a riqa kwantar mata da hankali da debe mu su d’ebe mu su kewa da dad’ad’an littatattafan marubuta masu cike da hikimomi, ilimantarwa, nishad’antarwa, uwa uba kuma da fad’akarwa.