Muhammad Sani Takori mni (Baraden Gummi) Marubucin

Daga Muhammad Sani Takori, mni

An yi umurni da ayi yafiya, shi kuma manta lamarin da ya faru, ya danganta ne da yadda yanayi ya bayar. Yanayin Siyasar Jihar mu a kullum sai daɗa zama ya ke yi wani abu mai rikitarwa. Duk da yake kowane ɗaya daga cikin waɗan da lamarin ya shafa yana ɗauke da nasa ƙaron da yake jin ba zai iya yafiyar sa ba, abu ɗaya ne ya haɗa su a gungu ɗaya, wato ƙiyayyar su zuwa ga wani mutum ɗaya.

Tsakanin Mai daraja Yarima da Mai daraja Mahmud Aliyu Shinkafi akwai matsalar cire Mai Martaba Sarkin Ɓurmin Bakura, tabbas wani ƙaro ne da har ya zuwa wafati Mai daraja Yarima ba zai manta dashi ba, domin kuwa wani miki ne da ya shafi dukan Zuriyar Ɗanƙwai.

Mai daraja Matawalle ma ya na da mikin wannan mutumen da ya kasance tamkar sabon baran sa a halin yanzu, wanda a can baya ya taɓa aza kyautar Naira Dubu Ɗari Biyar ga duk wanda ya kawo masa hoton inda Matawalle ke yin Sallah. To sai dai Mai daraja Matawalle ya mayar masa da martani a lokacin Yaƙin neman Zaɓen shekarar 2011 a garin Maradun.

Ko Sanata Hassan Nasiha ya taɓa samun nasa mikin, a lokacin da Maigidan ya yi ƙoƙarin zargin sa da gudanar da aiki maras inganci na kwashe lakar da ta addabi Madatsar Ruwan Gusau, aikin da aka ranto zunzurutun kuɗi har Naira Miliyan Dubu ɗaya, domin gudanar dashi, sai gashi bayan gudanar da aikin, abin ya zamo gara jiya da yau.

Wato babban ƙudurin Maƙiyin da ke goyon bayan wannan lamarin, shi ne ganin an kai Mai daraja Abdulaziz a ƙasa ne. Ɗabi’ar su ba ta yi daidai da karantarwar Addinin su ba. Allah maɗaukakin Sarki ya karantar damu cewa dukkan abin halittar sa ya na da abin da aka ƙudura masa na arziki ko dama, kuma babu mahalukin da ya isa ya tare ko ya hana wannan arziki ko dama zuwa ga wanda aka ƙudura ma ita.

Ƙulle-ƙullen ba akan Yari ba ne ba kurum, waɗansu daga cikin masu waɗannan ƙulle-ƙullen domin gyaran hanyar su ta siyasa a ƙarƙashin makircin wannan Tsohon Uban gidan nasu, babu wanda ya so Matawalle ya zamo Gwamnan Jihar Zamfara, sai dai domin ƙaddara ta riga fata.

Tariyar baya, tun a lokacin Zaɓen shekarar 2011, ya dangantakar sa take da su? Ina iya ɗaukar kowane ɗaya daga cikin su, in kuma bayar da labarin irin ƙiyayya da tsanar su zuwa ga Gwamna mai ci yanzu. Babban abin baƙin cikin wannan lamarin shi ne shi kansa Gwamna ya ƙi ya fahimci wannan abun.

Gurin su shi ne karkatar da tunanin sa daga ci gaba da ayyukan da ya tsara, da ƙudurin yin amfani da kasawar sa ta wannan ɓangaren a kakar yaƙin neman zaɓe na shekarar 2023. Mai daraja Matawalle kada ya manta da aibin sabon baran sa. Ya na biɗar hanyar ɗaukar fansar kayen da ya sha ne a hannun ƙaƙƙarfar rundunar yaƙi ta Mai daraja Matawalle, ba wai a Ƙaramar Hukumar Mulki , ko mazaɓar sa ba, a’a har ma a Rumfunan Zaɓen dake Ƙaramar Hukumar Mulkin Bakura. Ya na da wannan tarihi na kasa cin zaɓe a Ƙananan Hukumomin Mahaifiya da Mahaifin sa.

Ya kamata Mai daraja Matawalle ya ɗauki darasi daga yadda dangantaka ta kasance tsakanin sabon baran sa, da ɗan sa, wanda ya fi jijji da shi kafin yanzu. Allah cikin rahamar sa sai ya albarkace su a lokacin gudun Hijirar su zuwa Abuja. Sai gashi a yanzu sun sake rungumar shi har ma da wani karsashi da soyayya da ɗa’a da wula’a.

Addinin Musulunci ya karantar damu cewa mummuni ba zai amince a sha shi sau biyu a hulɗa ɗaya ba.

Ƙila wannan sharhi nawa shi ne na bankwana a fagen tu’ammali da shafin sada zumunta na fesbuk, sai dai nayi wa mai karatu alƙawalin baka bayanai akan rawar da kowannen mu ya taka, mai kyau ko maras kyau tun lokacin ƙirƙiro Jihar Zamfara. Tun daga rabon ƙaddarori har zuwa yadda aka salwantar da su waɗannan ƙaddarorin. Abu maras daɗin ji shi ne yadda gidaje masu sauƙi kuɗi guda 192 da mu ka karɓa a matsayin kason tamu Jihar daga Tsohuwar Jihar Sakkwato suka yi ɓatan dabo. Dama gidajen mu dake Titin Adeyola Adeku, Tsibirin Victoria, Legas, da gidajen mu na Kaduna. Takardun dake ɗauke da bayanai akan wannan lamari ba zasu gagare ni samu ba. Ka biyo ni, ka kuma saurare ni da kyau. Maciya amana ne suka zamo gwarzayen ka a yau.