Wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton’ masu garkuwa da mutane ne sun kai hari a Makarantar Aikin Noma da Kimiyyar Dabbobi ta Jihar Zamfara (CAAS) Bakura, inda suka kashe wani jami’in Dan sanda, da masu gadi 2 tare da sace dalibai 15 da Ma’aikatan makarantar 6.

Smarts News ta Ruwaito cewa, ‘Yan bindigar sun mamaye Kwalejin ne tun daga karfe 10:47 na dare zuwa 1 na daren yau, suna ta harbe -harbe a lokacin mamayar wanda ya yi sanadiyyar Kashe wani Sufeto na’ yan sanda da ke aiki tare da masu gadin Kwalejin su 2.Rundunar ‘yan sandan jihar har yanzu dai ba ta tabbatar da kai harin ba a hukumance, saboda kiraye -kiraye da yawa da aka yi wa jami’in hulda da jama’a na’ yan sanda (PPRO) SP Muhammad Shehu bai samu shiga ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton, amma majiyoyin mu da ke cikin Kwalejin sun tabbatar da cewa Manyan Jami’an Tsaro ciki har da Kwamishinan ‘yan sanda na Rundunar’ Yan sandan Jihar Zamfara, CP Ayuba Elkana da sauran Manyan Jami’an Tsaro sun isa kwalejin don dawo da zaman lafiya tare da daukar mataki na gaba.

Karin Bayani zai biyo baya;