Sanannen Dan Kungiyar Zabi Son ka dake jihar Zamfara Alh. Mande Sarkin Tasha Rawayya (Baraden Daza) ya rasu yana da shekaru 110.

Ya rasu bayan Doguwar jinya a Gidan shi da ke garin Rawayya a Karamar Hukumar Mulkin Bungudu ta Jihar Zamfara

Tuni aka yi mai janaiza a bisa yagarkin Musulunci.

Yan uwa da abokanin arziki na cigaba da Turuwa zuwa gidan shi Domin yin ta’aziyya