Rundunar sojojin Nigeriya da takwararta ta ƙasar Turkiyya sun yi alƙawarin ƙarfafa dangantakarsu domin magance ta’addanci.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wani da jawabi da Rundunar Sojin Najerita ta fitar mai dauke da sa hannun Daraktan Hulda da Jama’a Na rundunar Sojin Kasa ta Nigeriaya, Burgediya Janar Onyema Nwachukwu, Wanda yace an tabbatar da hakan ne a yayin ziyarar da Jakadan ƙasar Turkiyya a Nigeriya, Jakada Hidaye Bayraktar, ya kai ma Babban Hafsan sojojin ƙasan Nigeriya, Laftanar Janar Faruk Yahaya a shelkwatar Rundunar da ke Abuja.

Jakadan ya bayyana cewa dalilin ziyarar tasa ita ce Ƙarfafa dangantaka tsakanin ƙasashen biyu da kuma taimakawa Najeriya wajen yaƙi da ta’addanci.

Ya cigaba da cewar, ƙasashen biyu duk sun yi fama da matsalolin tsaro, in da ya bayyana cewa kamfanonin ƙera kayan tsaro na ƙasashen biyu sun shiga yarjejeniya domin rage ayyukan ‘yan ta’ adda.

A nasa jawabin, Babban Hafsan sojojin ƙasan Nigeriya, Laftanar Janar Faruk Yahaya ya bayyana ziyarar da cawa wata dama ce ta inganta dangantaka tsakanin ƙasashen musamman ma da rundunar Sojin ƙasa ta ƙasar Turkiyya.

Ya bayyana cewa a ziyarar da ya kai a ƙasar Turkiyya ya kai ziyara kamfanin sarrafa kayayyakin yaƙi na ƙasar.

Janar Yahaya ya tabbatar da cewa ziyarar Jakadan za ta ƙara danƙon zumunci tsakanin ƙasashen musamman domin ƙara himma wajen inganta kayan yaƙi da kuma musayar bayanai a tsakaninsu.