Jahar Zamfara tana daya daga cikin jahohin da ke da karamcin masu yin bahaya waje.

Bayanin hakan yana kunshe ne a cikin wani bayani da UNICEF ta rabawa manema labarai a Sakkwato, a lokacin bukin ranar makewayi ta duniya ta shekarar dubu dubu da ashirin da daya.

Bayanin ya baynnan cewa wata ƙididdiga da za’a fitar nan bada jimawa ba ta nuna cewa yin bahaya waje yana raguwa da kashi ashirin da ukku, a yayin da har yanzu yan Najeriya miliyan arba’in da shidda na yin bahaya a fili.

An bayyana cewa akwai jahohi irin su Kwara, da Plateau, da kuma Ebonyi dake da mafi yawan masu yin bahaya waje; yayin da jahohin Abia, da Akwa ibon, da Zamfara ke da karamcin masu yin bahaya a fili.

Hukumar ta UNICEF ta bayyana bukatar dake akwai na kara kokari wurin samarwa yan Najeriya tsaftattun ruwan sha, da tsaftar muhalli, da kuma ɗakunan bahaya a duk fadin kasar nan.

A lokacin da yake gabatar da takarda a lokacin bukin ranar makewayi ta duniya a Sakkwato, wani jami’in hukumar UNICEF mista Ebri Etem Ebor, ya bayyana cewar idan aka magance matsalar yin bahaya a fili, za’a kawo karshen matsalolin amai da gudawa, da sauran cutukka dake addabar al’ummar Najeriya.

Cov/maitaya