Ranar Litinin, 15th November, 2021, a wurin taron Hukumar Bunkasa Tallafin Arziki ta Kasa, a garin Lagos, Ministan Kudi Zainab Ahmed, ta hannun mai magana da yawun Ministar, Olajide Oshundun, ya bayyana ma duniya cewa gwamnatin tarayya zata bayar da wani sabon bashi na N656.1bn ga jihohi 36 na kasar nan, domin saukaka masu radadi na dawo da biyan basosa guda 3 da aka basu can da farko. Sun kira bashin da sunan “bashin cike gurbi”.
A karkashin wannan sabon tsarin, kowace jiha zata samu jimillar kudi N18. 225 bn, a biya 6 cikin wata 6.
Zaa biya bashin cikin shekara 30 kuma ba zaa fara biyan bashin ba sai bayan shekara 2.
Kowace jiha zata karbi kimanin N3, 037, 500, 000, 000.00 kowane wata.
Ruwan bashin 9% ne, wanda ya kama kusan N1, 640, 250, 000, 000.00.
Ana tunanin kowace jiha zata biya kimanin jimillar kudi N19, 865, 250, 000, 000.00.
Zaa cire N55, 181, 250, 000.00 daga cikin kudin kowace jiha a matsayin kudin bashin har tsawon wata 360.
Ni ina da korafi da dama game da bashin, babba daga cikin su shine, bashin baya da wani amfani. Ba mamaki, karanchin shekaru na ne yasa na kasa fahimtar hikimar bashin, amma a gani na, babu hikima, biyan bashi da bashi.
A maimakon wannan sabon bashin, me zai hana gwamnatin tarayya ta yafe masu wani bangare daga cikin wadancan basosan guda 3, ko ta jinkirta masu biya ko kuma ta tsawaita masu waadin biyan. A tunani na, zaifi dacewa a aza jihohin a wani tafarki na tsayuwa da kafafun su akan abun da ya shafi tattalin arziki, ta hanyar rage kudin da ake kashewa wurin tafiyar da gwamnati, a toshe hanyoyin da kudin gwamnati suke bacewa, ayi maganin cin hanci, a bunkasa kudin shiga, a fito da hanyoyi na samun kudi ga gwamnati, a hana jamian gwamnati yin tafiye tafiyen da basu da amfani, da daukar shatar jirage da yin ayukkan da suke da tasiri ga rayuwar talaka kai tsaye.
Wani abun shine, ruwan bashin yayi yawa. Ina laifi ace 1% idan har gwamnatin tarayya da gaske take yi cewa tana so ne ta taimaka ma jihohin domin su fita cikin kangin da suke na matsin tattalin arziki.
Na zura ido domin naga banbancin da wannan sabon bashin zai kawo a jiha ta.
N3bn kowane wata ba kananan kudi bane.
Ina sa rai, nan da dan lokaci kankane, zan ga canji, na hanyoyi da gadoji da flyovers, da tsarin lafiya na kyauta, da tallafin karatu ga dalibai, da ingantattun shiraruwa na tallafa ma alumma, da samar da ayukka, da yin garan bawul ga aikin gwamnati, da samar da tsaro a duk fadin Jihar domin samar da walwala ga alumma kuma dalibai su samu su koma makaranta, wadanda suka shafe watanni a gidajen su saboda matsalar tsaro da ta dabaibaye jihar fiye da shekara 10.

Bello Galadi, tsohon Shugaban Kungiyar Lauyoyi ta Jihar Zamfara kuma Shugaban Bello Galadi Foundation.
Zaa iya samun sa a:
muhammadbel_law@yahoo.com & muhammadbellaw80@gmail.com

22nd November, 2021