Hamdan Alhazai Shinkafi, wani matashi ne dake karamar hukumar mulkin shinkafi, Wanda ya bayyana ra’ayin shi akan batun zaben cike gurbin Dan majalisar yankin Shinkafi.

Ga ra’ayin Hamdan Shinkafi

Al’ummar jihar zamfara kamar yanda kuka sani idan akwai wata gwamnati wadda yaffi dacewa agareta da tabi doka da oda aduk gwamnatocin da suke a najeriya to ita ce gwamnatin
jihar zamfara, itace wadda yakkamata musamu a sahun gaba aduk fadin najeriya duba da yadda wannan gwamnati tassamu kafuwa a sanadin dokokin kasarnan domin ba za6enta akayiba dokokin kundin tsaren mulki ne suka kawota akan inda take a halin yanzu.

Kamar yanda Al’ummar wannan jiha Mai albarka suka sani Allah yayiwa Dan majalisa Mai wakiltar shinkafi a zauren majalisar dokokin jihar zamfara (HON MUHAMMAD G. AHMAD) Rasuwa tun a ranar Assabar 29 ga watan Yuli, 2021 a sakamakon harin “Yan bindiga Daya rutsa dashi akan hanyar sa ta gusau zuwa Kano don kai Yaron shi filin jirgi don ya wuce makaranta, wanda muke fatan Allah ya jikan sa yayi masa rahama.

Kawo yanzu (kimanin watanni Shida) karamar hukumar mulkin Shinkafi ba tada wakili wanda yake wakiltar ta a zauren Majalisar dokokin jihar Zamfara sakamakon mutuwar Wakilin na mu.

Al’ummar wannan Yanki sunada ƙorafe-ƙorafe da suke son gabatarwa gwamnatin jihar Zamfara amma babu wakili wanda zai isarda saƙonsu zuwaga gwamnatin.

ABUN TAMBAYA ANAN SHINE

A ina matsalar take kuma miyassa Gwamnatin take take Haƙƙin Al’ummar wannan yanki mai Albarka ? Wane Shiri gwamnatin jihar Zamfara takeyi domin gudanar da zaɓen cike gurbi a wannan yanki ? Gwamnatin jihar Zamfara ta manta da mutanen da suke a wannan yanki ne ?

Al’ummar wannan yanki Mai albarka na shinkafi muna bukatar mu samu wakili Wanda zai wakilce mu a zauren majalisar dokokin wannan jiha. Shin wai ma ya akeyi da hakkin al’ummar wannan yanki Wanda ya hana a gudanar da zaɓen cike gurbi domin yiwa Al’ummar wannan yanki mai albarka wakilchi kasantuwar su Ƴan Asalin jihar Zamfara ƴan Najeriya?

Da wannan muke kira ga gwamnatin jihar Zamfara datayi gaggawar shirya zaɓen cika gurbin wannan wakili kokuma muhaɗu da ita a kotu domin nemoma Al’umma wannan yanki Hakkinsu kasantuwar mu Ƴan Asalin jihar Zamfara kuma ƴan Najeriya Masu cikakkar damar samun Haƙƙoƙansu.

Daga karshe muna rokon Allah ya bamu zaman lafiya Mai dorewa a jihar mu ta zamfara ya bamu yalwatuwar arziki Allah yatoni asirin duk Wanda yakeda sa hannu ga matsalar tsaron jihar mu ya kuma zaunar da jihar mu da kasarmu lafiya Amin.