An tsinci gawar wani yaro da ya bata kimannin kwanaki goma sha shida suka gabata.

Yaron mai suna Ahmad Yakubu Aliyu Ijaba, mai kimanin shekaru Tara da Haihiwa, ya bar gida ne bayan da ya dawo daga Islamiyya a Unguwar su ta Gadar Baga dake cikin Birnin Gusau.

An gano gawar Yaron ne a cikin wani Kangon gida dake unguwar Barakallahu dake Gusau Babban Birnin Jihar Zamfara.

Wakilin mu ya bamu labarto mana cewa, anga yaron ne a cikin kangon gidan, bayan da mai gidan ya shiga da nufin ci gaba da aiki, inda yaga gawar yaron a ciki.

Ganin haka ne mai gidan ya mayar da ƙofar gidan ya rufe, sannan ya kai rahoto ga yan sanda domin ɗaukar mataki.

Wanda hakan ya bada damar aka nemi tantance yaron tare da sanarda mahaifan shi, wadanda tun farko suka sanar da Jami’an Yan sanda batun bacewar Yaron.

Mahaifin yaron ya ce Ahmad ya ɓace ne sati biyu da suka gabata, jim kaɗan da dawowar shi daga makaranta, a shiyar gadar baga cikin garin Gusau.

Ya ƙara da cewa bayan sun samu labarin ganin gawar yaro, nan take suka tafi suka duba, inda suka ga yaron su ne an kashe shi kuma aka KWASHE KAYAN CIKIN sa. Yana mai cewa likitoci sun tabbatar da cewa kwanaki goma kenan da kashe Ahmad.

An dai iske wannan gawa ta yaron, hannuwan sa da kafafu ɗaure, sannan an zura kan shi cikin leda aka ɗaure ta yadda bazaya iya yin nunfashi ba.

Ya zuwa lokacin hada wannan Rahoton ba mu samu jin ta bakin Rundunar Yan sanda ta jihad Zamfara dangane da lamarin, saboda mun kasa samun Mai Magana da yawun rundunar Yan sanda, SP Mohammed Shehu ta wayar tarho.