Wata mai bibiyar lamurran yau da Kullum, Sameerah Bello Shinco, ta bayyana halin da yan gudun hijira suke ciki a jihar Zamfara, musamman a fannin kiwon lafiya da muhalli da abinci da kuma mutuncin su.

Meerah Shinco wadda tayi rubutu akan halin da taga yan gudun Hijira suke ciki wanda ta yiwa taken “KOWA DA BIKIN ZUCIYAR SA!” ta yi rubutun nata ne tana cewa;

“Mutane da yawa suna farin cikin shigowa sabuwar shekara, Ni Kuma labarin da na wayi gari da Shi yafi damuna.

Yan gudun hijira mussaman a jihar Zamfara suna cikin tashin hankali da masifu. Ba abinci, ba sutura, ba matsugunni, ba magani, Kuma ba lafiya.

Da yawansu ganye suke ci suna rayuwa. Ina lillahi wa Ina illaihil rajioon!!

Bama wanan ba, babban abinda yafi daga min hankali shine; wasu kungiyoyi masu zaman kansu sun je wurin mabukatan nan domin su Dan tallafa musu da abinda Allah ya hore, ciki harda musu gwaje-gwaje da suka shafi kiwon lafiya, bayan da akayi kwajin wasu yan gudun hijirar, Sai aka samu da yawa mussaman Mata dauke da kwayar cuts mai karya garkuwar jiki wato HIV.

Bincike daKungiyar “Education for Self-reliance initiative” tayi ya nuna cewar; Yan ta’adda da sukayi garkuwa da su ne suka yi ma matan Fyade suka saka masu cutar ta HIV.

“Sun cuce su, sun saka musu ciwo. Ya Allah ka kawo Mana karshen wanan bala’in. Allah ka isarwa bayin ka da isar ka.” Meerah bayyana hakan.

Shugubar Kungiyar Education for Self-reliance initiative; Hajiya Suwaiba Abubakar Yalli, ta fadawa Jaridar Media Smarts news cewar sun samu labarin halin da yan gudun hijirar ke ciki ta dalilin rohoton da BBC hausa ta fitar a ranar 30 ga watan Disamba na shekarar da ya gabata, a inda take cewa “Jin cewar yan ta’adar sun yiwa wasu daga cikin matan fyade, shi yasa muka je unguwar Saminaka a cikin garin Gusau, domin yi musu gwaje-gwaje kan abinda ya shafi lafiyarsu. Sanan mu taimaka musu da magani. Munyi musu gwajin cutar TB saboda wasu suna fama da tari. Sanan kuma mun musu gwajin kwayar Sida inda wasun su aka same su dauke da cutar.”

Kungiyar wadda ke rajin ganin ingantuwar Ilimi, tayi aikin gwajin ne ta hanyar yin hadin guiwa da Wata kungiya ta kasashe ketare mai aikin bada agaji akan kiwon lafiya da ake kira SFH wato, Society for Family Health a turance, wadda ta bada kwararrun ma’aikata da kayan aiki aka gudanar da aikin gwajin ga yan gudun Hijira. Tana mai cewar yanzu haka ana cigaba da gudanar da aikin.

Daga karshe Hajiya Suwaiba ta ce “tana kira ga gwabnati da ta taimaka ta samar wa bayin Allan nan matsuginin da za a ajiye su, saboda suna cikin mawuyacin hali. Sanan duk da ta san cewar mutane suna taimakawa, amma tana rokon su kara tallafawa da abinda Allah ya hore masu mussaman masu hannu da shuni a cikin al’umma.

Da karshe ta yi kira ga kungiyoyi masu zaman kansu na ketare da su saka hanunsu cikin lamarin nan su taimaka.

Daga karshe ta bayyana shirin da suke da shi na bada kulawa ga yan gudun hijirar, Wanda nemi masu son su aika da taimakon su gan yan gudun hijirar da su tun tubi wadannan lambobi domin bada taimako ko neman Karin bayani 08069105289, 09036568516 ko kuma a masu turo abinda Allah ya hore zuwa wanan asusun ajiya kamar haka: 2081190186 zenith bank, Suwaiba Abubakar Yalli.