The Suspects

By Sani Ibrahim Mai Taya

Yan sanda a jahar Zamfara, sun samu nasarar cafke wasu mutane shidda da ake zargi da satar Yara tare da kashe su don dibar sassan jikin su.

Idan ba a manta ba a makon da ya gabata jaridar ‘Smarts News’ ta ruwaito labarin wani yaro mai suna Ahmad, Dan kimanin shekaru Tara da haihuwa, Wanda aka tsinci gawar shi a wani kangon gida a anguwar Barakallahu, dake Gusau babban birnin jihar Zamfara, an kashe shi an kuma kwashe kayan cikin shi.

Dalilin hakan yasa yan uwa da jami’an tsaro suka zurfafa bincike da zimmar gano masu hannu ga faruwar lamarin da kuma yadda yake faruwa.

Hakan yasa aka tuhumi yaron da aka yiwa ganin karshe tare da Ahmad a ranar da ya bace. Wanda matsa kaimi akan binciken yaron yasa ya bayyana gaskiyar lamari har ya lissafo masu hannu a cikin lamarin.

Idan ba’a manta ba makwanni ukku da suka gabata, ne Ahmad yayi batan dabo bayan ya dawo daga makarantar Islamiyya, a shiyar gadar baga, dake Birnin Gusau.

Jaridar ‘Smart News’ ta samu labari ta ingantacciyar hanya cewa, yanzu haka rundunar yan sandan na jihar Zamfara na ci gaba da gudanar da bincikar yaran don gano yadda wannan mummunan aiki ke faruwa

Haka ma ‘Smarts News’ ta samu sahihin labarin cewa, tuni gomnan Zamfara Bello Muhammad Matawalle tare da Kwamishinan yansanda CP Ayuba Elkana suka ziyarci wani Ofishin yanki na Yan sanda inda ake bincikar yaran da ake zargi.

Duk kokarin da muka yi don jin ta bakin mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Zamfara SP Mohammed Shehu, abun yaci tura.