Mai unguwa ne zaune kan kujerarsa, yayin da sauran jama ar fada ke kewaye da shi kan wata ƙatuwar tabarmar ana ta hira da mai da zance.

Tunda suka doso fadar idon mai unguwa ke kanta.

Kanta ɗauke da tiren talla, kunkumin nan an ɗaureshi tamau da gyale, ga fuskarka ta sha kwalliya da fauda buda jaka.

Masifa kawai ta ke ta zubawa har bakinta na kumfa.

“Karime Wallah gobe sai na ci uwar Indo, hegiya kucaka ta rasa wa za ta yi zance da shi sai Hamusu rabun raina! Ke alƙur an ji nake kamar na kifar da kayan tallar nan na je na ragargaji tsinanniya.”

“Yo ke Abuwa tun yaushe na ke gaya miki ki rabu da tsinanniya? Shegen kwashe-kwashe irin naki yasa ki ka kwaso mai ƙwatar miki masoyi. Yo ni ban isheki ƙawance ba ne?”

Kallon sama da ƙasa ta yi mata ta keɓe baki

“Taɓ! Kin manta ita ɗin ƴar waye? Ƴar gidan mai unguwa ce fa! Duk sati ranar juma’a sai mun je cin hinkafa gidansu. Ke ko sau ɗaya aka taɓa dafata gidanku. Shima albarkacin yayanku ya bi doguwar mota ya yi kabo-kabo zuwa burni ya auno muku ita.”

Cikin yanayin jin haushi ta ce

“Shegiya kwaɗayayya, ai ke wallahi kin ji jiki. Dama tunda naga kin liƙe mata nasan da biyu ne, shiyasa duk ranar juma a kike korata idan na biyo miki yawon juma a. Har kike wani cewa sau ɗaya kika taɓa ci a gidan mu. Ke sau nawa na ci a gidanku?”

“Ko sau ɗaya. Amma ai kina zuwa kwaɗayin tuwan biski da miyar ja.”

“Aikin banza! Abunda sai a share mako uku ko hudu ma ba ai ba, duk ranar ko da a ka yi ƴar hali ki ke yi mun, kin yi ta haɗe fuska kenan kuna kumbura kamar Fanken Dudu na bakin kasuwa.”

“Kam bala i! Nice Fanken Dudun Yasin sai na hau kan gandar bakinki na yi luguden leɓe, yar jakar ub…”  Ta sauƙe tiren tallan dafaffiyar gyaɗar ta  ta nufota gadan-gadan za ta cafko ta, da sauri ta matsa can gefe tana faɗin

“Idan na tsaya kenan za ki yi luguden ko? Ai wallahi ke da Indo ne sai na faɗa mata kwaɗayi ki ke zuwa yi gidansu.”

“Idan kin fasa faɗa mata kin raina Talatuwa mai Tafasa!”

“Ko kuma Inno mai Ƙosai ba!”

“Kam bala in can! Innar tawa?”  “Ita dai, ai uwa ba ta fi uwa ba.”

Har zuƙowa ta yi, itama Karime ta dire kwanon tallarta .  “Zo mana! Kada ki ganki haka gaɓa-gaɓa ki ɗauka tsoron ki na ke, Aradu idan ban kwasheki na laftaki a ƙar ba.”

“Kai! Kai!! Kai!! Kai!!! Kunga ƴan nema, me ya haɗaku kuma?”

Abuwa da takaici ya gama cikata, na rashin luguɗen leɓen da ba ta samu ta yi a kan gadar Bakin Karime ba ta ce.

“Ƙiran sunan Inna ta ta yi.” Tana faɗa tana hararar Karimen, kamar wacce idanunta zai zazzago ƙasa don harara. Ga wani ƙarin takaicin ma da ta ƙirata da sunan da ta fi tsana (Gaɓa-gaɓa.)

“Ƙarya ta ke yi Baban Lanti. Ita ta fara ƙiran sunan uwata.”

“Ya isa, ku wuce mu je, tun ɗazu Mai unguwa ke hango hayaniyar da ku ke, da ya ke ku ba ku san zuru ba sai an tanka shine ku ka ci gaba ko? Za ku yi bayani ne.”

Jin Mai unguwa ne ya turo ƙiransu duk hanjin cikinsu ya kaɗa, tsoronsu ɗaya kada ya ƙira musu tsabga, don wannan baƙin mugun idan ya riƙe mutum da dorinar nan tashi ba ƙaramin jibgar mutum  ya ke ba.

Nan suka bar kayan tallar suka ranƙaya gaban mai unguwa.

Ɗan aiken ya gurfana gaban Mai Unguwa yana mai dunƙule yatsun hannunshi na dama, yayin da ya ɗaga babbar yatsarshi yana mai jinjina wa Mai Unguwar yana faɗin “Ranka shi daɗe! ga yaran nan na taho da su.”

Ya ƙarashe maganar yana mai nuna su Abuwa da Karime da ke durƙushe can a ƙasa, duk sun yi tsuru-tsuru, kamar wanda su ka kar uwar Mai Unguwa.

Sai da ya ɗan ɗau lokaci kafi ya fara magana cikin isa da mulki  “Menene ya faru ku ke ta sa insa a tsakaninku tun ɗazu?”  Shiru su ka yi ba amsa

Tsawa mahukuncin fadar ya daka musu yana mai nuna su da miƙaƙƙiyar doninarshi ya ce,

“Ba Magana a ke yi maku ba ne? Ko nan ma rashin kunyar za ku yi mana? Ahir ku kula, fada ku ke.”

“A…A…Ab!”

“Ta ce me? Kin bi kin ishemu da in ina.”  “Cewa ta yi wai Indon gidan Mai Unguwa ta…”  “Ƙarya ta ke kwarankwatsa. Sunan Innata ta ƙira.”  “Ƙarya ta ke, ita fa fara ƙiran sunan tawa uwar.”

Duk suka karaɗe wajen da hayaniya, da wannan ta ɗauko zance sai wannan ta katse, musamman ma Abuwa da ta ke tsoron tonon tonon asirinta.

“Kai! Kun raba mana hankali, maganar wa za mu ɗauka cikinku?” Ɗaya daga cikin jama ar ya daka musu tsawa. “Cewa ta yi Inno Mai Ƙosai.” “Ƙarya ta ke yi, ita ta fara cewa  Talatuwa mai Tafasa.”  Sarkin fada ya ce “Yau naga shashanci gurin yara. To ai abun alfahari ne a san mutum asan sana a tasa, naga duk faɗin unguwar nan da Inno Mai Ƙosai ake ƙiranta, ita kuma Talatuwa mai Tafasa. Duk ai sana ar tasu ta gado ne, shine har kuke husuma a kai don an ƙira sunansa?”  Liman da ke zaune gefen hannun damar mai gari ya zuba ma yaran ido, ya kaɗe idonshi guɗa ɗaya na dama, yana nunasu da yatsa ƴar manuniya da ke hannun dama ya ce “Wai wannan kam ba Abuwa bace ƴar gidan Ilu mai Amalanke?”  Sarkin fada ya amsa yana mai jijjiga kai kamar riƙaƙen gadangare “Ita ce fa! Ai fitinaniyar yarinya ce. Waccar  kuma Karime ce ƴar gidan Mudi mai jaki.”  “Ikon Allah! To, mai Ilun yake jira da bai sallamata ba? Duba fa, duk ta ƙere sa anninta a girma.”  “Man liman ai yariyar saurin girma ne da ita kamar wani kaji da na gani a can Binni, cikin garin Jinjin, wai kajin turawa, can garin yahudu da nasara a ke kawo su, haka nan suke gaɓa-gaɓa. Girma ba hankali.”  “To, ai kam gara ya miƙata, tun kafin a fara sata cikin waƙa. Wannan ai abun kunya ne ma a gareshi. Ƴa ta kai har wannan lokacin.”  “Ai kam! Sa ar fa Huwaila ce ta wajena. Yanzu suke shiga shekara na sha uku, amma kaga ita Huwaila ai bata kai ta ba, nan da mako biyu ne ma za a kai ta ɗaki.”  “Ikon Allah!”  Duk ka-ce-na-ce ɗin da ake Mai Unguwa nashi ido, don ya ma rasa ta cewa. Hasalima tunanin  shi daban ne.  “Ke me ya haɗa ku da Indo ƴar gidan Mai Unguwar?”  Ɗago kai ta yi sai hawaye sharrrr! “Ba komai.”  “Da gani ba ki da gaskiya, domin duk wani mai saurin kuka rashin gaskiya ne da shi.”  “A a, dama… Dam…!”  “Dama me? Ke Karime, me ya haɗa su da Indon?”  Gyara zama ta yi, kamar dama jira take. Nan ta ɗauko zance tun daga tushe har zuwa ƙarshe.

Salallami gurin ya ɗauka da. Sarkin fada ya ce “Ikon Allah! Ke kuma haka Allah ya yo ki da kwaɗayin hinkahwa? Yo in ba gidan Mai Unguwar ba, ina ake dafa ta? Shima dai albarkacin dangantakar da ke tsakaninsu da kansilan yankin  Mai Auduga ne yake kawo mishi shi, wataran a turo ƴar Kwafarati wataran ƴar Hausa. Shine har za ki ɗarsa rayinki a kai? Ikon Allah.”   “Kwankwatsi ƙarya ta ke yi mini. Ba haka nan bane.” “Rufe mana baki ja irar yarinya kawa…” Mai Unguwa ne ya katseshi yana faɗin “Ku barsu haka nan, ku kuma kada na kuma jin kun yi hayaniya a tsakaninku. Maza tashi ku tai.”  Jiki na rawa duk suka miƙe, kowa ta sunkuci kayan tallarta. Canza hanya su ka yi, sai da su ka daina hango fadar Mai Unguwa Abuwa ta ce  “Yasin da an dokeni kanki zan rama.”  “Yo ko da ba a dokeki ɗin ba ai kin ɓare baki kamar ɓaure kina ta sharɓar kuka, Tuɓu luɓus kawai, mai kama da kazar masu jajayen kunnuwa.”  Tana kaiwa nan ta sa gudu.  “Hegiya da ƙafa kamar Mazarin tsire. Za mu haɗu da dare a dandali.”

Da ɗai-ɗai mutanen da ke fadar Mai Unguwa suke tafiya, har ya rage saura Mai Unguwa da sarkin fada. Sunkuyowa yayi da kanshi saitin fuskarka Sarkin fadan.

“Kai! Wannan yarinyar ƴar gidan Ilu mai Amalanke nan fa kalar mu ce.”  Zaro ido ya yi, cike mamaki ya ce “Ranka shi daɗe! Wannan ai ta yi ƙarama, duka-duka nawa take.”  “Ka ji shashanci! Ita Abullen ba za ta zauna ba ne idan an kai ta ɗaki ko me ka ke nufi Kallamu?”  “Ahh! Zama kai, daram ma kuwa. Kawai dai gani na yi ta ƙawar Indo ce ta wajenka kuma ƴar autar gidan ka.”  Ɗagowa ya yi, ya na ƙare ma Sarkin fada kallo  “Ahir ka iyar ma bakinka. Ka je ka sami Ilun ka gaya mishi idan bai bada ita Abuwar ba ina ciki.”  “An gama ranka shi daɗe!” Har ya fara tafiya sai kuma ya dawo ya durƙusa yana jinjina  “Amma yallaɓai kana ga ita yarinyar za ta yarda?”  Murmusawa ya yi har sai da jajayen haƙoranshi da suka gama rinewa da goro suka bayyana.  “Yarda kam ai ta riga ta yi an gama. Kai dai je ka sanar ma Ilun. Ita da ke zuwa cin hinkahwa duk sati, ta samu a sati sau biyu ko uku ai kaga ta more, domin da zarar an yi auren nan za a dawo da girka ta sau biyu ko uku a sati don in samu ta zauna.”  Shima dariyar ya yi ya ce  “Kuma fa haka ne yallaɓai! Na wuce ma, da zarar na yi sallar magariba zan wuce can ɗin.”  “To, madalla. A dawo lafiya.”

“A ah! Yau kuma mutanen fadar Mai Unguwa ne a gidan namu?” Malam Ilu mai Amalanke ya faɗa lokacin da ya fito ƙofar gida bayan ɗan aike ya sanar ana nemanshi a ƙofar gida.

“Ranka shi daɗe nine da magaribar fari.” Juyawa ya yi ya kalli gabas da yamma kudu da arewa “In ce dai Sarkin fada makuwa ya yi ko?”  “Makuwa kuma? Mai ka gani?”  “Ji na yi ka ƙirani da sunan manya.”  “Au! Wai da na ce Ranka ya daɗe? Ai ka dace da hakan ne. Ko za mu samu waje na musamman, domin muhimmin saƙo ne ke tafe da ni.”  “To! Allah dai yasa lafiya ba?”  “Lafiya lau ma, sai alkairi.”  “To Madalla. Ina zuwa.”  Gida ya shiga ya ɗauko tabarma ya shimfiɗa a ƙarƙashin bishiyar darbejiyan da ke can gaba da gidan.

Bayan sun zauna, suka sake gaisawa gami da tambayar lafiyar iyalan da kuma harƙoƙinsu.  Shiru ne ya gifta tsakani, kafin Sarkin fada ya katse shirun da faɗin.

“Mai Unguwa ne ya tasani ya ce in zo takanas ta kano, ƙafa da ƙafa in sameka in sanar kuma in yi maka albishir cewar idan ba a yi ma Abulle miji ba yana riƙo. Ya gani yana so.”  Ilu ya faɗaɗa fara arsa ya ce  “Ikon Allah! Banda Mai Unguwa da abunshi ai Abulle ƴar shi ce, ko an bada ita ya ce ya mata miji ai da gudu za a ƙarɓo ta. Wa ma zai ƙi haɗa zuri a da jinin Mai Unguwa? Wanne ɗa ne ko jika za a ba Abullen daga ciki?”   “A ah! Ɗa ko jika kuma? Ba ko ɗaya daga ciki.”  “To, wane ne daga cikin dangin nashi?”  Yana maganar fuskarshi fal annuri.  “Da alama dai ba ka fahimci maganar tawa ba. Shi Mai Unguwar ne ya gani ya ke so, ya kuma buƙaci a bashi auren ita Abullen.”  Cak! Numfashin shi da tunaninshi ya tsaya na wucin gadi.

Jin shirun da ya yi ba amsa yasa Sarkin fada gyaran murya ya ce  “Malam Ilu na tare da ni kuwa?”  “Ina tare da kai Sarkin fada.”  “To, me ka ce ne?”  “Anya ko Abulle ta wajena ka ke magana kuwa?”  “Ita ɗin ce dai, ai duk faɗin unguwar nan tamu ta Mai ludaya ita ake ƙira da Abulle ko Abuwa. Sai Zebu ƴar gidan Iro mai tumaki sai kuma Zinaru ƴar gidan Audu gurgu. Dukda sunayen nasu guda ne Zenabu amma ai da Inkiyar da ake ƙiran kowa.”   “To, amma ai ita Abuwar ba wata babba har can ba ne. Ina laifin Ma ƙaramin ɗan shi Mado da Indo ƙawar ita Abuwar ke bi ko dai wani daga cikin jikokinshi. Amma shi da kanshi ai ya girme mata nesa ba kusa ba.”  “To, shi aure ina ruwan hi da wani girma da tsufa ko shekaru? Zaman lafiya da kwanciyar hankali ake nema ai. Kada ka manta abunda ka ce, ba wanda zai ƙi haɗa zuri a da mai gari.”

‘Da ne da na fahimci maganar a baibai.’

“Haka ne. Yanzu a yi haƙuri aɗan bani lokaci in tuntuɓi ƴan uwana da uwar ƴar da ita ƴar, duk abunda muka yanke zan zo har fadar Mai Unguwar in sanar muku.”  “To, ba damuwa. Muna jira, fatan ba za a ɗau lokaci mai tsawo ba?”  “Da ikon Allah.”  “To, Allah yasa mu ji alheri. Na barka lafiya. A gaida Iyalan da ita Abullen a ce mai unguwa yana miƙo gaisuwa.”

Naɗe tabarmar ya yi ya nufi cikin gida ranshi ɓace, tunda ya shiga gidan ma bai iya zama ba. Jingina ya yi da zanar da aka zagayeshi da ɗakin. Inno da ta fito daga daki hannunta ɗauke da tire na kwano, an jere kwano tuwo da miya na ci ka duba da kofin ruwa shima na ci ka duban akai tana ƙoƙarin ƙiran ƙanin Abulle ya zo ya kai ma Babansu waje ta ganshi tsaye ƙiƙam kamar wani soja.

Da sauri ta sunkuya ta a jiye kayan abinci ta matso ta ɗan rage tsawo tana tambayeshi “Lafiya kuwa Malam ka shigo ko ƴar gyaran muryar nan babu?”  Tsaki ya ja kafin ya bata amsa, murya cike da takaici  “Ina fa lafiya Inno?”  Karɓar tabarmar ta yi ta shimfida musu.  “Malam ka zauna.”  Zaman ya yi domin yana da buƙatar yin hakan, wannan baƙon al amarin da ya kawo mishi ziyarar bazata yasa ya ji jikinshi duk a mace ba wani kuzari. Ji ya ke yi ma kamar ba ƙasusuwa a jikinshi.

“Hankali dai Malam! Wannan irin zama haka kamar tumar ƴan bori ai sai ka ji rauni.”  “Yo, Inno ai na gode ma da na iya yin hakan. Gaba ɗaya fa ƙafafuwana yadda ki ka san an miƙe sanda haka na ke jinsu.”  Kare ma zaman da ya yi kallo ta yi, ya jingina bayan shi da bukkar ɗakin nasu, yayin da ya miƙe ƙafafuwan shi ƴan sirara masu kama da maburgin miya.

“Niko in ce Malam tsere ya yi da agaribar farin nan dai ko, ko in ce lisha i tunda lokaci ya yi, don ma wajen namu sai ai sallar ma mutum bai ji ba.”  “In da tseren na yi ai da na ji daɗi da wannan mummunan labari da ya riskeni a farkon dare.”  Gyara zama ta yi “Tofa! Wannan wani irin labari ne haka? Allah yasa dai ba Baffa Jafaru na burni cikin garin Jinjin ba ne ya riga mu gidan gaskiya?”  “Ji wani mugun alkaba i a nan? Wan nawa ki ke yi ma fatan mutuwa a wannan tsakani? To li ilafi tsakanin shi da ke.”  Tsuke baki ta yi ta koma gefe. Tsawon shuɗaɗun mintunan da ba su gaza goma ba ya ce “Habba! Ai hakan ma ba zai yiwu ba.” Bayan ya gama jero tsaki ya furta hakan.

“Malam wai me ke faruwa ne kam?”  “Me ke faruwa ku? Bayan turo ssrkin fada da mai Unguwa ya yi kan cewar idan ba a yi ma Abulle miji ba yana kamu.”  Zaro ido waje ta yi ta haɗa hannayenta biyu ta sauƙe su kan ƙirjinta da ƙarfi tana faɗin  “Na shiga uku! Wai wani Mai Unguwar?”  “Mai Unguwa namu dai na mai ludaya.”  “Da kanshi ko dai ma jikinshi ko ɗan shi?”  “To, wai Abuwa tamu ko dai Abu na gida Baba Ɗan Azumi da mijinta ya mutu kwanaki?”  “Kin ji ki da wani batu! Ita Abullen nawa ke garemu?”  “Ɗaya ke gare mu a gidan nan. Amma a dangi sun yi huɗu.”  “To, ta gidan nan yake magana.”  “Ji wani budurwar zuciya ana. Kuma shi tsofai-tsofai da shi, uban wane kakan wance ya rasa wa zai aura sai Abuwa?  Ince dai ba ka amsa mishi ba.”  “Ina fa, na dai ce su bani nan da mako guda zan sanar da ƴan uwana. Duk hukuncin da aka yanke zan sanar da shi.”  “Gara hakan ai. Kafin nan cikin manemanta ta cire gwani sai a ce musu an ba da ita kawai.”  “Yauwa, hakan za a yi. Ku zauna da ita ki ji waye gwanin nata.”  “To, Malam.”  “Barin je in yi sallar lisha i, har an ida a masallaci ina nan.”  “To, a dawo lafiya.”

Duk suka nufi gida rai bai so haka ba, don basu samu sun raba raini da Abulle ba. A cewarsu tsoro ta ji tunda har ta k’i zuwa dandalin.

Itama ta nufi gida rai b’ace na rashin samun biyar buk’atar ta, don ta gama tsara yadda za ta luguɗen tsuntsayen kan Karime, tunda ta gaggaya mata magana. Don tasan halin Karime da son gulma da neman shiga, duk yanda aka yi ta je ta sanar ma Indo abun da ya faru. Kuma tabbas tasan tare za su zo, gashi iya zaman da suka yi a hanyar zuwa dandali ba wak’iyarsu.

Haka ta nufi gidan rai b’ace, tana shiga ba tare da sallama ba ta yanki hanyar bukkar d’akinta.

“Ke Abulle zo nan.” Juyowa ta yi tana tura baki, ta dawo ta durƙusa kusa da Inno ba tare da ta ce komai ba. 

“Me ya haɗaki da Indo ‘yar gidan mai unguwa?”

“Ba komai.”

“K’arya ki ke yi, za ki gayamin ko sai na sassab’a miki.”

Sake turo baki gaba ta yi tana mai matsawa baya, don tasan abu mai sauk’ine Inno ta sauk’e mata wannan busheshshen hannun nata.

“Da gaske ba komai fa Inno.”

“Amma ai an ce kun je fad’a ne.”

“Lahhhh! In ji wani munafukin?”

“In ji ni.”

“A a!” Tana mai gyad’a kai.

“Ahir d’inki wallahi na kuma jin, ko a ce mun kin je gidan mai unguwa wallahi sai na tara miki gajiya. Ɓacemun da gani shashasha kawai.”

Wuf! Ta mik’e kamar tana jira, ta nufi d’aki zuciyarta fal tunanin me Inno take nufi da har zata hanata zuwa gidan mai unguwa? Kenan sun yi ban kwana da ‘yar sati kenan ko kuwa? Taɓ! Da sake wai an ma mai zani ɗaya sata.

Washegari Mai Unguwa da sarkin fada.

Bayan ‘yan zaman fadan sun watse ne mai unguwa ya ke tambayar Sarkin fadan.

“Kai! Wai yaya ne zancenmu?”

“Ai yallaɓai wannan fa inaga so yake ya hanamu. Bai wani bani k’wararren amsa ba, cewa ya yi in je zai zo har fadan idan sun zanta da shak’ik’anshi.”

Shafe fuskarshi ya yi, tare da tsefe gashin gemunshi da ya gama zamewa fari.

“Ba komai, mu bishi a hankali, kasan ‘yar shi ce. Mu da muke nema muke da hak’uri da k’ask’antar da kai. Yanzu dai abun da za a yi ita ‘yarinyar zaka yi k’ok’arin shawo mana kanta.”

“Yallaɓoi shi da ke k’ark’ashinmu ai shi zai bimu ba mu za mu bishi ba.”

“Kai! Wa ya fad’a maka? Ai inda aka san darajar goro, nan ake nema masa ganye. Mu jira dai muji me Baba Ilun zai ce.”

Cike da mamaki sarkin fada ya d’ago kanshi, ya kafe ‘yan k’ananan idanuwanshi ya sauk’esu kan mai unguwar ya ce,  “Am fad’o daga dabino, an fad’a rijiya. Yallaɓoi Ilune fa!”

“Eh, shi dai.”  “Ikon Allah! Wai na kwance ya fad’i.”

Cike da mamaki Mai Unguwa ya bishi da kallo yana fad’in,  “Wanda ya cika, ai ya mallakeka kai da iyalanka. Tunda naga d’iyar shi ina so ai dole in girmamashi.”

Yana karkad’a kai ya ce  “Um! Haka ne.”

Nan suka ci gaba da zantawa.

Tafe take hannunta rik’e da ganyen rama, ta sayo a kasuwa za ta gida, sai ga Sarkin fada.

Wangale baki ya yi yana fad’in,  “A a! Kaga manyan mata, kalan manyan mutane. Ina aka fito kuma?”

Cikin jin kunya ta durk’usa k’asa tana sunkuyar da kai, ta ce “Baba sarki ina wuni?”  “Lafiya lau Abulle. Abulle ta mai unguwa.”

Kunya ce ta sake kamata jin ya k’irata da Abulle ta Mai Unguwa, tasan tsokanar ta yake kan yadda aka ritsasu a fadar Mai Unguwa.

Mik’ewa ta yi za ta tafi, ya ce “Za a je gida ne?”  “Eh.”  “To, a gaida Malam Ilu kuma ki fad’a mishi ina tuni da sak’onnan.”  “To.” Kawai ta ce ta yi gaba.

“Kai Muntari, wai Ina Abulle ta yi ne tun ɗazu bata ɗau tallan Gyaɗar nan ta tafi dandali ba.”

“Inno, wata Abuwar? Sai dai ki tura mata da shi can. Don tun da aka ida sallar magariba suka fice ita da Saratun gidan Shawai wai za su dandali faɗa.”

“La ilaha illallahu! Faɗa dai? Ita da wa.”

“Da Indon gidan Mai Unguwa.”

“Na shiga magana! Yi maza ka je ka yo k’iranta tun kafin ta jawo mana magana a gari.”

A guje ya fice, ya d’au hanyar dandali.

Abulle ne da Saratu ke tsaye a kan hanyar zuwa dandali, jiran isowar Indo kawai suke yi, sai dai shiru har yanzun ba alamar zuwansu da tawagarta.

“Sarai! Anya ko Indo zata zo yau kuwa?”

“Yo, nima shi nake tunani, har yanzu banga ɓullowarsu ba.”

“To, ya za a yi?”

“Binta zamu yi har gida, mu yi kamar mun biyo mata zuwa dandali, idan ta fito mu tari mu tara mata gajiya, mu fitar mata da jini da majina, daga baka har hanci.”

“Ke! Kina hauka ko? To Yasin ba dani zaki je ba. Kin san wannan me sharb’eb’iyar dorinar idan ya rik’emu sai d’an burinmu.”

“Haka fa! To kawai mu yi jiranta.”

“Ke nifa ba Indon ce damuwata a yanzu ba.”

“Hamusu ko?”

“Hamusu? Hamuso. Ni baya gabana ma yanzu, don naga idonshi rawa ya ke yi, baya tsayuwa waje guda. Yaje can su k’arata da Indon.”

“Kuma don iskanci shine kika tsaidamu kan hanya kamar wasu ram-santi na cikin garin Jinjin.”

Dariya Abuwa ta tuntsire da shi, har da durk’usawa k’asa tana fad’in.

“Sarai meye kuma wani rafsanti?”

Tsaki ta ja tana hararar Abuwar,  “Matsalata da ke k’auyanci. Ram-santi ake cewa dallah. Lokacin zuwanmu cikin garin Jinjin bikin ‘yar gidan Baffana Tallene muka wuce wasu da kayan sarki tsaye a kan kwalta suna bincike, dana tambayi su kuma su waye? nagansu da kaya daban ba irin na holis d’in da suke zuwa kama mai laifi bane a garin Mai ludaya ba. Shine aka ce mun wai Ram-santi sunansu.”

Cike da mamaki Abuwa ta ce,

“Yo shi cikin Jinjin ai komai gani ake, Allah dai ya kai ni nima inga yarda take.”

“Amin dai, inda kuna da dangi a can.”

Kallon sama da k’asa gami da yatsina fusa ta bita da shi, “Mu a suwa da zamu yi dangi a birni? Ku da ke da dangi ai shiyasa naga kullum k’afarku na can, dad’in abun dai k’auye dai tushen birni ne, idan aka bi diddigi su Baffa a cikin k’auyen mai ludaya za a bankad’osu.” Ta k’arashe maganar tana mai d’auke kanta daga kan Saratun.

“Ikon Allah! Daga magana kuma sai cibi ya zama k’ari? To, Allah ya baki hak’uri. Kinga tafiyata.” Ta k’arashe maganar tana kunce mayafinta da ta d’aure a k’ugunta shirin fad’a.

“Sauk’a lafiya, agaida na gaba.”

Sak’e-sak’e tashiga ya azuciyarta, na takoma gida ne? Ko tawuce dandali? Idan kuma ta je dandalin ba wani burgewa abun za ta gani  ba.

Har ta juya zata yi gida, sai kuma ta sake juyowa ta nufi hanyar dandalin.

Tana gab da isa ne ta ji an k’wala mata k’ira, ko bata juyo ba ta shaida muryar mai k’iran nata.

Juyowa ta yi don ganin dalilin k’iran nata.

Hasken farin watan da ya haskaka duniya ne, ya hasko mata fuskar Muntari da yake ta zuba haki dalilin gudun da ya ci.

Tsaki ta ja kafin ta ce, “Lafiya ka ke k’wala min uwar k’ira a daren nan?”

“Inno ce ta ce in zo in k’iraki, na manta na tsaya yin Langa dasu Sabitu. Sai da naga wucewar Saratu na tuna Aradu.”  

“Jeka da Allah ina zuwa.”

Ta juya zata tafi.

“Alk’ur an ta ce ki zo yanzu-yanzu.”

Juyowa ta yi ta zabga mishi harara sannan ta d’au hanyar gida.

Indo da Karime da k’awayensu guda biyu da suka iso Dandalin tun da magribar fari suna jiran zuwan Abulle shiru ba labarinta, yasa suka fara taraddadin zuwan nata.

“Karime anya ko Abulle zata zo?”

“Tsaf zata zo in dai Abulle ce, kinsanta bata fashin zuwa dandali sai da dalili mai k’arfi, balle kuma yau a cike take, mu jira muga zuwanta.”

“Ke nifa tunda kika zo gida ki ka gayan zancen nan nake tsuma, Allah-Allah nake ta iso. Aradu in sunkuya na kwashi k’afarta ku bita da duka.”

“Ke, ni kayan tallana nake tunani a gidanku.”

“Yanzu kika tuno da tallan naki?” Inji d’aya k’awar tasu.

“Lantana ai ina nan hankalina na can ne, tun fa rana dana fita ban koma gida ba.”

“Ni fa kunga tafiyata ma zan yi.”

“Ke Sahura ai dama ruwan ciki ne da ke.”

“Hu umm! Ku ji Indon nan? Kuma dare ya yi sai in yi ta zaman jiran gawon shanu ko? To, ba da ni ba. Sai kun zo.”  Ta juya ta yi tafiyar ta.

Karime ta ce

“Kai, mu tafinku muna, gobe za ta fito ne, sai mun kwashi ‘yan kallo.”

Duk suka amsa da, “Mu je.”

Da dare, Abulle suna zaune a kan tabarmar da suka shimfiɗa a ƙarƙashin barandar ɗakin Inno, suna cikin tuwon dare.

Wani kafcecen loma Abullen ta yanko, ta iza shi cikin bakinta, ji ka ke ya ba da sautin “Muƙutt!” Sanadiyar haɗiyar da ta yi masa ba tare da ta tsaya taunawa ba.

Haka ta yi ta wurga lomomin nan, tana haɗiɗɗiyar su, ba tare da ta tsaya ɓata lokaci wajen taune su ba.

Ga zufar da ta gama wanke mata fuska, wanda har ɗiga ya ke a ƙasa.

Inno da ke can gefe kan kujerar tsuguno, ta ɗago fitilar ƙwan da ke gefen ta ta haska fuskar Abullen, a daidai lokacin da ta yanko wani tiƙeken loma ta zazzaro idanuwanta waje masu kama da ƙwan zabbi, tana shirin wurgashi baka, ganin hasken fitilar yasa ta tsagaitawa tana mai kallon Innon da ta saki baki tana binta da idanuwanta kafin ta ce.

“Ikon Allah! Wai ke a rayuwarki ba ki iya cin abinci cikin nutsuwa ba ne? Ki duba dai ki gani, ke ɗaya ke ci amma Allah-Allah ki ke ya ƙare, kamar wata mai warwaso kina tsoron kada a ƙwashe a barki hannu rabbana.”

Turo baki ta yi gaba ta yi tana faɗin,

“Inno! Nifa a hankali na ke cikin abincina.”

“Hoɗijam! A hakan?” Ta tambayeta.

“Eh.” Ta bata amsa a taƙaice gami da wurga lomar da ta ke ta juya shi a  hannunta.

“Ummmhh! Lallai da aiki. Da alama gidan Sarkin noma za a wurgaki, domin wannan irin ci naki ba dai gidan rago ba.”

Ta faɗa a lokacin da ta ke ajiye fitilar da ke hannunta a ƙasa.

“Shiyasa kullum ki ke ta hawa kamar farashi ai, daidai da sakan guda ba ki fatan bakin ki ya zauna shiru, ko da yaushe yana cikin motsi hayayam-hayayam. Ki sama ma kan ki lafiya tun wuri ina gaya miki, ba ko wani namiji ne zai iya da wannan cin naki ba ina gaya miki.”

Ta ƙarashe maganar tana mai ci gaba da saƙar hular da ta ke yi da ƙwarashi.

“Inno! Shima fa cin nan lafiya ne aradu, idan mutum ba ya lafiya ina ya ga wani bakin cikin abinci, Allah duk randa aka kai ni gidan da ba abinci kullum gida zan riƙa turo da ƙwarya ta ana yi mun zubi, gara ma tun da wuri kada ku cire ƙwaryata ku barni a layi.” Tana maganar ne tana lashe hannunta da ta gama damalmale shi da miya, tana gamawa ta kuma rarumo kwanon tuwon ta hau suɗewa.

Inno ta ce, “Wannan ai an yi, ba a yi ba kenan. An sai da akuya, ta dawo kuma tana ci mana danga.”

Ba ta kula ta ba sai ma ci gaba da ta yi da suɗe kwanon, wanda baya buƙatar wani ruwa da omo wajen wanke shi, domin yawun Abullen ya wanke shi tas.

“Ko da yake shi gwanin naki ma Hamusu rago ne, tunda tun zamanin ƙuruciya da aka bashi gwaji a kan kaza ya gaza riƙe ta, duk da yake ita ɗin dabba ce, ina kuma ga an bashi ɗan mutum?”

“Taɓ! To ni me ruwana da wani Hamusu kuma? Can, su ƙarata da Indo ƴar gidan mai unguwa ni na wuce ajinsa”

“Iyee! Zamani. Kukam dai yaran yau sai dai abarku, kina gabana ko kunya ba ki ji.”

“Yo, to Inno naga dai zancen nan ke ki ka fara yowa ita, ni ko na ɗora.”

“Uhmmm! Haka ne.”

“Inno shi kiwon kazar kuma ta me cece ne da na ji kin ce an ba shi Hamusun ya kasa riƙon ta?”

Kallon ta ta yi, kafin ta ce,  “Ita wannan kazar da ki ka ga ana ba duk wani ɗa namiji da ke wannan ƙauyen kiwo, ana bashi ne don gwajin yadda zai iya riƙe iyali. Idan aka ga yana kula da ita wannan kazar sosai, to a hankali za a bashi tunkiya, kinsan ita tunkiya uwar tamɓele ce, idan nan ma aka ga ba laifi, sai a yi mishi canji zuwa rago, da haka dai har zuwa kan saniya, idan aka ga ya iya kiwo to anan ne za a bashi mata. Idan kuma shiririta ya sa a gaba to sai dai a wurgashi gona kuma ya yi ta fama.”

Baki ta saki tana jin jawabin Inno har ta dire, ita ma ta jefo mata tambaya da faɗin, ” Kuma Inno shi wannan gwagwarmayar duk mutum ɗin na ƙarami ne zai yi shi? Kuma dama ba su noma ne sai sun gaza riƙon dabba?”

“Suna yi mana, idan yaro ya kai munzali kuma sai a yi mishi auren ladan noma.” Cewar Inno.

Keɓe baki Abullen ta yi ta ce,

“Hu’umm! Sun ji daɗinsu.”

Shigowa gidan ya yi, ba ko sallama sai ma bambamin faɗa da ya ke ta yi har ya iso inda suke zaune, ya ja ya tsaya.

Bayan shi ya yi ma masauƙi da garun ginin jar ƙasar da ke bayan shi, yana huci da huro iska daga cikin bakin shi, ya harɗe hannayeshi bisa ƙirjinshi yayin da ya ɗago ƙafarshi ɗaya ya dogare ta jikin garun, ɗayar kuma tana ajiye a ƙasa.

“Barka da shigowa Malam! Yanzu na ke neman Muntari ya kai muku abincinku waje, baya nan, ina ga ya fita dandali wasa ne.”

Tsaki ya ja, ya ce, “Wa ke batun abinci kuma.”

   “To, mai kuma ya faru? Na ji ka shigo kana ta bambamin faɗa.”

   “Sarkin fada ne ya bi duk ya matsamin da zancen auren nan wallahi, ba dama ya ganni, duk  ya bi ya hanani sukuni.”

  Jin an ambaci Sarkin fada yasa Abulle ta zaburo tana faɗin,  “Walle ɗazu ma ya aikoni, wai ko yana maka tuni ko me na dai manta.”

Inno ta galla mata harara, “Ina kuka haɗu da shi? Ko binshi fadar ki ka yi?”

Zaro ido ta yi alamar tsoro, “Walle Inno a hanya muka haɗu, da na je sayo rama a kasuwa ina dawowa.”

“To, dama da kin ganshi kafin ya hangoki, ki maza ki sake hanya, kin ji na faɗa miki.”

   “Inno!”

      “Innon gidanku.” Ta yi mata daƙuwa da yatsunta biyar.

“To, Malam yanzu meye abun yi?”

Ƙarasowa ya yi, ya zauna a gefen tabarmar da Abullen ke zaune.

  Da sauri ta tashi ta koma ƙasa ta zauna.

“Ni kaina na rasa ta cewa, da ina tunanin in ce mata cikin manemanta ta fidda gwani kawai, idan na je sai in sanar musu tana da gwaninta dama a hannu.”

  Cewar Ilun mahaifin Abulle.

“Hakan ma ya yi, ke cikin maneman naki waye gwaninki?” Ta jefa ma Abulle tambayar.

    “Ni… Ni… Ba kowa.”

“Ba kowa ki kace?”

    “Ba kowa Inno.”

          “Umm! To kaji Malam. Da alama rabon mai unguwar ne.”

“Ke Inno! Hauka nake zan ɗau Abulle in ba sa ar kakana?”

     “To Malam, idan rabon shi ce fa?”

           “Bama rabon shi ba ne.”

      “U um fa Malam! Kasan fa rabo ajali ne, ba mu san me Allah ke nufi kan hakan ba. Idan dai ita Abullen tana so ai shikennan.”

Jinjina kai ya yi, kafin ya ce,  “Kuma fa kin kashen jiki, kince Allah a lamarin dole in saduda tunda ita ɗin ma bata da wani tsayayye.”

“Ke Abulle! Mai Unguwa ne ya turo Sarkin fada cewar yana son aurenki, me kika ce?”

Sai yanzu ta gane kan wa suke zancen su, domin da duk a baibai take fuskantar zancen nasu.

‘Wai yau ni Mai Unguwa ke son aure? Lallai ina da sa a.’

    Zancen zuciyarta kenan, kafin ta sake dulmuya wata duniyar tunanin.

Hangota ta yi a gidan Mai Unguwa, an dire mata wani ƙaton kwanon kaya shaƙe da dafaffiyar shinkafa ‘yar gwamnati mai santsi da miyar ja, ga kuma ƙatuwar kaza a kai, gefe kuma ga babban kwanon sha cike da sassanyar ruwan ranar ƙasa.

Sake kallon ƙeta ta yi ma hinkahwar a karo na ba adadi, tana kuma tuna irin cin walaƙancin da  za ta yi mishi.

  Sake ware ɗaurin zaninta ta yi don yayi sako-sako gudun kada cikin nata ya yi saurin cika, ta kalmashe ƙafafunta waje guda, ta zura hannunta ciki ta gauraya gefe guda, ta ciko hannunta ta kai shi zuwa bakinta.

“Kingani ko Inno! Na gaya miki yarinyar nan ba son auren nan za ta yi ba, gashi ko amsa bata bamu ba.”

Maganar da mahaifinta ya yi, shi ya hanata jin ɗanɗanon hinkahwar da ta shaƙe hannunta da shi, maganar ce kuma ta yi silar dawo da ita daga duniyar tunanin da ta afka.

  Ta ji takaicin rashin ɗanɗana girkin, sai dai duk ranar da Allah ya kai damo ga harawa ba ƙaramin ɓarna za ta tafka ba, cin huce haushi za ta yi mishi.

Murmushi ta yi, wanda sautinshi ya fito,  “Kin gani ko Inno? Kuka fa ta ke yi, gara a janye maganar nan idan yaso a jira har ta samu gwani.”

  Cewar Malam Ilu.

Salallami Inno ta sanya tare da tafa hannayenta, ta iza ɗaya a haɓarta ɗayan kuma ta ɗago fitilar dake ajiye ta haska fuskar Abullen da shi.

   Kallo suka bita da shi, fuskokinsu fal mamaki.

Madadin suga hawaye ya wanke fuskarta, murmushi ne ke ta bayyana a fuskarta, idanunta kuma a rufe.

“Ke Abulle! Lafiyar ki kuwa?”

Inno ta tambayeta.

Da sauri ta buɗe idon ta sunkuyar da kai alamar kunya ganin yadda iyayen nata suka tsatstsareta da ido.

A guje ta bar wajen ta nufi ɗakin kwananta, zuciyarta cike da farin cikin nesa ta kusan zuwa kusa.

“Shikennan ai Malam, abu ya zo gidan sauƙi, alamu sun nuna ta yi na am da zancen. Sai ka yi maza ka sanar da su kai ma ka sami lafiya.”

  “Ai kamar yanzu ma kuwa ba sai an kai gobe ba.”

  “Sai kuma mu toshe kunnuwanmu, don za mu sha surutu gurin jama ar garin nan.”

  “Yo Inno! Idan sun yi ma ai za su bari, da yardar yarinya ai aka yi, ba dole aka yi mata ba.”

  “Haka ne kam.”

Ya miƙe yana faɗin, “Barin je in sanar ma Sarkin fadan.”

   “To, a dawo lafiya.”

Tunda aka sanar ma Sarkin fada bai yi wata-wata ba, a daren ya isar ma Mai Unguwa.

   Washegari Mai Unguwa ya turo wakilanshi neman auren Abulle, da sadakinta dubu ɗari. Take aka  sallama musu aka kuma sanya musu mako biyu mai zuwa aure.

Kafin kyaftu da Bismillah, zance ya karaɗe illahirin unguwar su Abulle, ya karaɗe garin mai ludaya da ƙauyukan dake maƙwaftaka da su.

  Tsegumi ne kawai ke yawo ta ko ina, ga uwar Indo ma ta ɗaga hankali a gidan Mai Unguwa.

“Kai  dai ba ka taɓa rabo da abun kunya, ka rasa wacce za ka aura sai ɗiyar cikinka. Allah wadai wallahi, girma dai ya faɗi.”

Cewar Tabawa.

Kallo Mai Unguwa ya bita da shi, kafin ya ce  “Abun kunya? Ai mu gaba muka bashi ba baya ba, in dai ta nan hanyar ne. Yaya ina ƙoƙarin raya sunnar Ma aiki Rasulullahi, kuma ki ke neman jifata da wasu kalaman da basu dace ba?”

Harara ta zabga mishi,

“Wani raya sunnar? Ka rasa lokacin da zaka rayar sai da duk furfura ta gama baibaye ka, mutuwa  yau ko gobe, amma ka ke wani ƙiran raya sunna.”

“Kai Tabawa! Ni da ke ba wanda ya san gawan fari, har yau ba za ki rage kishi ba. Yarinyar nan dai naga ƙarama ce, ba ruwanta, bata san komai ba. Don Allah ki sassauta kishin nan naki a kanta, kinga Lami kam ko a jikinta, bata wani nuna damuwar ta ba.”

 Gyara zama ta yi ta ce,  “Lami daban Tabawa daban. Yo ita dama ɗaga hankalin me za ta yi? Taga jiya taga yau, abu tun zamanin ƙuruciya kuke tare, tun auren saurayi da budurwa, ta riga ta ci lokacinta ai, tunda ko ni nan ma ta haifeni few da aniya, balle kuma wata can wai ita Abuwa. Har ka ke wani ƙirinta da yarinya, ƙarshen yarinta inga Inno ta sanya majanyi ta goyata a baya, ta kuma ɗauki bulumboti ta liƙa mata a baki sai in yarda.”

Ganin da gaske take, zancen nata ba na ƙare ba, yasa ya miƙe yana gyara zaman rawaninshi ya saiti hanyar fita yana faɗin,

 “Ni dai na faɗa miki, ki sa ma ranki salama ki yi fatan a zauna lafiya kawai don kin san bani son fitina a gidana.”  Yana kaiwa nan yasa kai ya fice.

Tana huci tana faɗin,

“Za ma ka dawo ne ka samen, da rawani kamar an naɗa gammo.”

Yana fita Indo ta faɗo ɗakin kamar wacce aka hankaɗo.

Gallamata harara Tabawa ta yi tana faɗin, “Ba ki iya tafiya a hankali ba ko? Kin wani faɗomin ɗaki kamar wacce kare ya biyo.”

   “Yi haƙuri Tabawa! Mutane ne suka ishen a gari, wai me yasa za a bar Baba ya auri waccar yarinyar? Wasu sunce don yana mai unguwa ne ya sa zai yi musu fin ƙarfi, wasu suce sayen ta yi yi, wasu ma cewa suke wa…”

Tsawa ta daka mata,  “Koma me suka ce, ba ke kike jajiɓo ta ba? Inda ba ki talla mishi ita ba ina zai ganta? Na ji kuma ance saurayinta da suka daɗe tare ya yi ƙaura ya dawo wajenki, kinga da ta tashi huce haushin ta sai ta huce kan mahaifinki. Kinga nan da kwanaki goma ta zama kihiyar uwarki kenan. Sai ki shirya tarbar sabuwar uwa.”

  Ranta ɓace ta ce, “Allah ya satura! Ko rabin-rabin uwata ba ta kai ba, na san kuma kwaɗayin hinkahwa ne zai kawo ta Yasin za ta ga walaƙanci.”

Masifa ta rufeta da shi har bakin da ya gama rinewa da goro yana fidda kumfa, inda ana bada aron baki, da ba abun da zai hana Tabawa ta yo aro yau.

Haushin kaza kenan.

“Yi maza ki je gidan Goshi ta baki daddawar nan, kafin ki dawo na gama daka kukar sai a haɗa musu waje guda ki tafi, kinga rana na tafiya, kada dare ya riskeku, ga hanyar ba kyau ne da ita ba.”  Cewar Inno da take ta tiƙar busheshshen ganyen kukan da ta zuba a turmi, babban burin ta ta mai dashi gari.

“To Inno!”

Ta fice daga gidan ta nufi gidan Goshi mai Daddawa.

“Abulle! Abulle!! Abulle!!!”

Tun daga nesa yake ta ƙwala mata ƙira, sosai ta jishi ta ƙi juyawa  Ganin ƙiran nashi ba na ƙare ba ne, yasa ta juyo a fusace tana hararar shi.

“Wai lafiya kake yi min irin wannan ƙira kamar wani tsohon makaho ko wacce ta sace maka ɗan taure?”

Ƙarasowa ya yi yana dariya ya ce,

“Yo Abulle don na ƙwala miƙi ƙira haka ai ba laifi ba ne, tun ranar nake so mu haɗu mu tattauna amma kin ƙi kulani.”

Kallonshi take mai haɗe da harara,

“Kam me zan saurareka? Cemaka aka yi ina da lokacinka? Ka dai san ni ba sa arka ba ce ko?”

Cike da mamaki ya hangame baki kamar wani gaɓo yana kallonta kafin ya ce,

“Nine fa”

Ta yatsina fuska tana faɗin”Kaine wa?”

“Hamusu rabun ran Abulle.”

Ya ƙarashe maganar cikin yanayin shauƙin so, har yana wani jijjiga jiki irin na jin daɗin nan.

“Hamusun Indo dai! Ai ni yanzu na wuci saninka.”

“Ni ɗin?”

“Kai ɗin fa.”

Ta juya ta fara tafiya, ko mai ta tuno sai kuma ta juyo ta yi mishi kallon sama da ƙasa.

“A je a bi wani sarkin, ba da ni ba, auren talaka.”

Ta juya ta yi gaba.

“Dakata! Kada ki yi ƙoƙarin jifana da duwatsu, ina mai shawartarki da ki adanasu ki gina gida da su domin nasan duk daren daɗewa zai yi miki amfani. Sannan kada ki yi kuskuren ƙonani da wuta domin da shi muke kunna fitilun da ke haskaka duk wani gida da ke faɗin kyauyen nan. Duk ranar da ki ka kuskura ki ka yi wannan gangancin ina mai tabbatar miki da cewar za ki dawwama cikin duhu.”

Yana kaiwa nan ya juya cikin ɓacin rai,

“Matsalar ka ce wannan kuma, mayaudari kawai.”

Ta ja dogon tsaki ta wuce aikanta.

“Kinsan da tafiya a gabanki amma ki ka sami waje ki ka zauna ko Abulle?”

“Inno da na same ta a gida ai ba zan zauna ba, hegiyar yawo ne da Goshin nan kamar wacce ta ci ƙafar kare.”

“Ni tafi ki je ki shirya, shegen iyayin tsiya, kin san hanyar Mai Rangwangwan ba kyau ne da shi ba. Idan ku ka yi dare ku kuka sani, don ma mai babur ɗin ɗan garin ne da ya sauƙeki gida zai wuce da sai dai ki zauna sai gobe kuma.”

“Inno to a bari mana gobon na tafi.”

“Ungo nan.”

Ta watso mata yatsun hannunta biyar.

  “An ƙi a barwa goben. Dududu bikin saura kwana goma ne, idan kin je gidan Kawun naku Talle ki ka dawo Jinjin za mu tafi can gidan Kawun ku na burni, nan ma ki kwana biyu ki zo ki bi gidajen dangi na kurkusa suma ki musu sallama.”

Murna ne ya rufeta da ta ji batun tafiya Jinjin, itama za ta je burni ta ga yadda yake.

Ruwa ta dauka a bokiti ta je ta watsa, tana fitowa ta sa kaya, yau ba batun kwalliya, kayanta kulle a cikin ɗankwali, sai wani ƙaramin buhu da aka sa mata dankalin hausa, kuka da daddawa.

Sallama ta yi ma Inno, bayan ta gargaɗeta ta kuma ja mata kunnen ta kula ta kuma dawo akan lokaci.

Muntari ya ɗaukar mata buhun kukan, suka nufi tasha wajen mai mashin ɗin da aka jima da yi mishi magana.

Tana isa ba ɓata lokaci ya suri Abulle da wata mata suka ɗau hanya.

Gam Abulle ta riƙe ƙarfen jikin mashin ɗin, domin idan ba haka ba a yadda suke cafke a kan hanyar nan za a iya tsintota a ƙasa idan aka daka wani tsallen.

Taimakon ta ɗaya a tsakiya take, ba don haka ba, abun ba dama ne.

Kwananta biyu a Mai Rangwangwan ta dawo, cike da ɗoki da murnar zuwa birni.  Har gida ta je ta sanar ma Sarai itama za ta birni gidan Baffanta Jafaru don haka gara a daina yi musu yanga, don ba a fi su tsumma ba, balle a baɗa musu ƙwarƙwata.

Kwananta ɗaya a Mai ludaya washe gari suka ɗau haramar barin gari zuwa babban birnin Jinjin.

Tsarabar ‘yan Maraya daban da ta ƙauye, domin su ba daddawa ba kuka.

Kabeji ce da kayan miya, sai kuma manyan kaji guda biyu.

“Inno! Su mutanen Jinjin ɗin ba su cin kuka da daddawa ne? Naga nasu tsarabar daban da ta Mai Rangwangwan.”

Abulle ta tambayi Inno, ganin yadda aka bambanta tsarabarsu

“Ke, tuwon girma ai miyarsa nama. Su can me za su yi da wani kuka da daddawa? Tuwon ma ai sai su shafe mako huɗu ma ko fiye da hakan ba su yi shi ba.”

Cikin mamaki da sakin baki ta ce,

“To Inno me suke ci kuma?”

“Ohho! Idan mun je kya gani.”

Tsuke bakinta ta yi har suka tattari shirginsu suka ɗau wanya.

Kalle-kalle kam Abulle ta yi shi, mussaman ma da suka fara shigowa cikin birnin, ga kwalta shimfiɗe kamar tabarma, ƙarafunan wutar layi a tsaye kan hanya, jere reras kamar an dasa bishiyoyi.

“Ikon Allah! Kayan burni daban da na ƙauye.”

Abulle ta faɗa a bayyane.

Kallo wasu daga cikin mutanen cikin motan suka bita da shi, don daga dukkan alamu ita ɗin sabon shiga ce a zuwa Maraya.

Amai ko ta yi shi yafi sau biyar, tun tana wanke jikinta da shi har aka bata tallafin leda.

Har cikin tasha aka sauƙesu, anan ne fa taga tarin jama a, sai kaiwa da komowa a ke yi, kowa na sabgar gabanshi.  Abulle kam banda kallo ba abun da ta sa a gaba.

Idan Inno ta yi gaba, sai ta sake dawowa baya ta jawo hannun Abulle idan ta ga wani abun. Wani lokacin ma tuntuɓe take yi ko ta yi karo da wani abun tsabar kallo. Haka dai har suka tsare adaidaita zuwa unguwar su Baffa Jafarun.

Nan ma dai mamakin ne cike da Abulle ganin mashin mai ƙafa uku, ga kuma gidaje harda masu hawa-hawa.

Wani akan wani.

‘Ikon Allah! Na zaune bai ga gari ba.’

Zancen da Abulle ta yi a zuciyarta kenan.

Tafiya dai-tafiya dai, har suka iso inda za su, suka biya mai adaidaita, ya ƙara wuta.

Buga get ɗin ƙofar gidan suka yi, da sauri mai gadin ya zo ya buɗe musu ƙofar. Ganin Inno da ya yi ne yasa shi wangale baki yana faɗin,

  “Maraba lale da mutanen Mai ludaya. Yau kune a garin namu?”

“Maraba dai Ɗayyabu! Gamu kamar an jefomu.”

“Sannunku, ku shiga mana.”

Ya faɗa yana ɗaukar wasu daga cikin kayan da suka zo da shi ya yi gaba.

“Inno kin san shi ne?”

“Farin sani ma kuwa, a Mai ludaya yake shima, ɗan gidan Malam Datta mai katako.”

“Au! Na ɗauka ai tsabar zuwan da kike ne ya sanki.”

“Yo ni yaushe ma nake zuwa? Rabon da garin nan tun ina goyon Muntari da muka zo yi ma Baffanku barka da dawowa daga Makka.”

Haka suka ƙarasa har cikin gidan Inno na yi mata bayani, ita kam inda za a shaƙeta ma ba ta san ɓaɓatun da Inno take yi ba, don gaba ɗaya hankalinta ya tafi ga kallon tsari da haɗuwar da gidan ya yi.

Zuciyarta ke yi mata tambayar,

‘Wai dama suna da dangi masu kuɗi kuma ‘yan burni shine ba su taɓa zuwa ba?’

Ita dai a saninta da wayonta sau biyu ma ta taɓa ganin Baffan nata a ƙauyensu, sai dai Babanta ya zo ko kuma ya yi musu aike daga nan.

Suna ƙoƙarin shiga falon, Ɗayyabu kuma na fitowa. Ya ce,

“Inno wannan kamar Abuwa?”

“Ita ce.”

“Ikon Allah! Girma dai ba wuya, ta girma abunta.”

Ya faɗa yana riƙe haɓa.

“Girma kam ai ba wuya Ɗayyabu, musamman ma na ‘ya mace. Yanzu ma sallamar Baffanni take zata gidan aure.”

“Ikon Allah! Ashe dai zamu Mai ludaya kwanan nan.”

Ya wuce yane ‘yan zantuttuka, su kuma suka shiga.

Sanyi da ƙamhi ne ya ziyarci sassan jikinsu da hancinsu.

Abu guda ne ya faɗo ma Abulle, tunowa da ta yi da ɗakin Inno mai tsamin ƙuli.

Tunowa da tayi da ɗakin Inno mai ɗankaren tsamin ƙuli da wasu tarkace.

Da sallama suka ƙarasa cikin falon, Hajiya da yaranta biyu suna zaune kan kujera suna kallo.

Da fara a Hajiya Sabuwa ke yi musu Maraba da zuwa, a ƙasa ƙaramar kafet ɗin da aka ɗaura kan tayis ɗin falon suka zube. Inno na amsa maraban da take yi musu yayin da imanin Abulle ya gama tafiya ga kallon kayan alantun da ke falon.

‘Yan gaishe-gaishe suka yi, nan Hajiya Sabuwa ta shiga tambayar jama ar gida.

Dungurin Abulle ta yi tana faɗin,

“Kekam mene ne haka? Saki iya gaisuwa ba ne?”

A firgice ta dawo hayyacinta, tana faɗin,

“Ina kwana?”

“Ita kika gani ma, ai ga manyan masu hankalin da suka fita ma basu iya gaisuwar ba balle kuma ita.”

Kallon su Inno suka yi suna mai daɗin,

“Sannunku da zuwa. Kun zo lafiya?”

Daga nan basu kuma ɗorawa ba, suka cigaba da abun da suke yi. Don su a zatonsu irin baƙi masu zuwa neman aikin nanne ne suka zo.

“Ke Lubna! Tafi ki kawo ma baƙi ruwa, Kai kuma Afreen ka ɗauko musu lemo.”

Kowa ya tafi ɗauko abun da aka aike shi.

‘Lubina! Ji wani suna kamar na makarai don Allah, ga wani ma wai a firij. Idan kana raye a duniya dai kaga abu.’

Zancen zucin Abulle.

“Inno ina fatan dai anan za a bar min ɗiyata ta kwana biyu ko?”

 Hajiya Sabuwa ta tambaya.

“Hajiya ai itace silar zuwan tawa ma, nan zan barta ta kwana biyu, ni yau zan koma. Bikinta ya zo saura mako guda tazo yi muku sallama.”

“Amma ko kin kyauta wallahi, dama ba ta taɓa zuwa nan ba.”

“Hajiya, kuma ai ba zuwan kuke yi ba, ko yaran nan ma ku ɗan riƙa kai su suga dangi abun ya gagara, tayaya za su yi zumunci a tsakansu?”

“Wallahi ni kaina ina son su je, sai dai makaranta ba su da lokaci, ga kuma halin Alhaji bayaso su matsa ko ina.”

“Makaranta ko ai ba zai hana su zumunci ba, naga ai suna ɗan samun hutu, ko mako guda suka je suka yi ai za su ga danginsu. Alhaji kam kada a yi mishi sharri, don kin san halin mazan namu idan ba ke mace kin sasu a hanya ba ba yadda za a yi su ce miki jeki, ke mace ke ya kamata ki riƙa yi masa nuni da hakan tunda ki ga shi ba mazauni ba ne.”

“Haka ne kam wallahi, don idan ka biye tasu zumuncin ma ba za a yi shi ba.”

“A to, gara dai a riƙa ƙoƙartawa. Kada wataran a  haɗu a hanya ba a san juna ba.”

Dariya suka sa.

“Inno ai ba za a yi haka ba ma, ga biki ya zo, sati za muyi a Mai ludaya da yaddar Allah.”

“Allah ya yaddar mana.”

“Amin dan na biyur Rahmanti.”

Ruwan gora mai sanyi aka kawo musu da kofi, ga kuma lemon kwalba, guda biyu mai ja da baƙi.

“Ke Lubna zo ki zuba musu mana kin ja kin zauna, wannan ƙanwarki ce Zainab ‘yar gidan Baffanku Ilu da mahaifiyarta.”

Hajiya ta ke gabatar ma yaran nata da su Abuwa.

Kallo yarinyar ta bisu da shi, tana mai taɓe baki, na ganin yadda suke a jigace kuma wai ace danginsu, danginma na kut da kut! Ƙanin mahaifinta.”

Ruwan ta zuba musu a kofi, lemon kuma ta buɗe musu murafen ta koma ta zauna.

Tunda aka dire musu, Abulle ke Allah-Allah lemon kwalbar nan ya ziyarci bakinta ya gangara maƙoshinta har ya zuwa tumbinta, don tana ganin mutane ranar kasuwan garinsu suna sha da burodi ko da bisko ko fanke.

Ana buɗewa kuwa ta kai ma baƙin nan sura, kai kawai ta kafa ta fara kwanƙwaɗa.

Zirrrr! Shine sautin da ta ji a kan harshenta, da sauri ta cire a bakin nata, sai da ta ɗan tsaya kafin ta kuma kwankwaɗa, ai ke ta cire a bakinta.

Wani gyatsane ya taho mai haɗe da iska, gaba ɗaya ta yamutse fuska tamkar tsohuwar da ta shekara dari a duniya.

Idanunta ya ciko da ƙwalla, azabar gas ya ratsa har cikin ƙwaƙwalwar kanta.

“Wayyo Allah na shiga uku! Inno kaina, hancina.”

Shine abunda Abulle ke faɗi.

“Sannu Zainab! Ai coke gas ce da ita, ba a yi mata shan garaje.”

Faɗin Hajiya Sabuwa, lokacin da ta taso tana riƙe Abuwar.

Sauran yaran kuwa dariya suke ta zabga mata, Inno dake gefe sai jero mata sannu take.

Wani sabon gyatsa ta sake yi mai tafe da hawaye, ta ce,

“Yau naga bone! Inno wannan ko ba itace giyar nan da ake faɗa ba kuwa?”

Gaba ɗaya suka sake sa dariya, idan ka ɗauke Inno daga cikin masu dariyar, don ita ta taɓa shan jar sau biyu a rayuwarta.

“Ke wa ya faɗamiki wannan ne giyar? Tataccen lemo ne aka haɗa shi da wasu sinadaran.”

Lubna ta bata amsa.

“Taɓ! To nikam ba zan kuma sha ba alƙur an. Wannan abun sai ta iya yin ajalin mutum. Fuuuuuu! Fa na ji ta hauro min aka.”

Duk suka sake sanya dariya.

“Inno amma dai za ki yi sallar azahar ki ci abinci kafin ki tafi ko?”

“Eh, kinsan motar garin namu ƙarfe biyu take tashi, kafin na yi sallan sai in wuce.”

“To, Allah ya kai mu.”

“Amin.”

Nan suka ci gaba da hirarsu, Afrin, Lubna da Abulle kuwa duk imanimsu na ga tibi.

Ƙiran sallar azahar yasa duk suka watse daga falon, ɗakin sauƙar baƙi aka kai su Inno.

Nan suka yi sallah, Abulle ko addu ar kirki babu ta miƙe ta nufi falon, don dama bata so aka dagata kan kallon ba.

Ba kowa a falon, sai ƙaton tibin da ke ta faman aiki. Zama ta yi, ta kuma baza idanunta, kan kwalbar. Tashar turawa take kallo, wani tsamurarren bature sai zabga surutu yake, ita dai ba ji take ba nata ido.

A hankali-a hankali taga yana ta tahowa yana kuma nuni da hannunshi tamkar mai nunata.

Ganin yana shirin faso kwalbar ya fito ne yasa Abulle fasa wani uban ƙara. A kiɗime ta zabura, duk ta gigice ta rasa ina ta dosa? Ta ma rasa inda za ta gudu ta tsira kafin aljanin tibin ya gama fitowa ya risketa.

Shiko gadan-gadan yake ƙara matsowa, a waige-waigen da take na neman yanyar tsira ne ta hango hanyar da zai sadata da ɗakunan gida.

A guje ta ɗiba, yayin da mutanen gidan suma suka fito a guje don ganin ihun me take yi?

Karo suka yi da Hajiya, take ta sake sake ihu ta hau roƙo da magiya gami da bada haƙuri.

“Ke wai lafiyarki ne?”

Hajiyar ta tambayeta, karkarwa ta shiga yi tana magiyar kada ya cutar da ita tasan shi namiji ne ya koma muryar mata, ta tuba ya mata rai, yau ma zata bar gidan ta fasa yin kwana biyun.

Cike da mamaki Hajiya ta ce,

“Abin Allah! Budurwa da ciki; Gwauro da yaye. Inno ‘yar taki na tare da ƙwanƙwamai ne?”

Ihu ta sake kurmawa tana faɗin,

“Don Allah kada ku cutar da Inno! Tare za mu tattara duk mu tafi. Mun tuba ku yi mana rai, har abada ba zamu kuma Jinjin ba.”

Duk suka yi tsuru-tsuru suna kallon ikon Allah.

“Ina fa wani ƙwanƙwamai! Rashin kunya ne kawai, mace ta auri mace.”

“Na shiga uku! Muryar Innon ma ɗaukewa ku ka yi.” Ta sake zabura.

Janyota Inno ta yi tana faɗin,

“Wai wani iya shege ne haka ƙauri da kare? Mu ne zaki mayar aljannu? Zaki buɗe idanuwan ko sai na kwakwkwaɗa miki mari?”

Da sauri ta ware idanunta, taga jama an gidan duk tsaye suna kallon ikon Allah.

Juyawa ta yi ta kuma kallon tibin, sai taga wasu masu jajayen kunnuwane ke ta tiƙar rawa.

‘Ikon Allah! Wai na kwance ya faɗi. Ko ina ma mutumin ya nufa ne ohho.’

Ta tamabiyi zuciyarta.

“Tambayar ki ake, me ya faru kike kurma mana ihu a cikin gida?”

In ji Inno.

“Wani mutumi na gani yana ta ƙoƙarin fitowa a cikin kwalbar can, yana ta zuwa inda nake.”

Duk suka sa dariyar ƙauyancin Abulle.

“Kedai akwai shashanci, tayaya mutum zai fito daga cikin tibi har yakamaki? Sai kace wani almara? Allah ya shiryeki. Inno muje ku ci abinci kada ki rasa moto tunda kinƙi kwana, kuma kince ba za ki jira Alhajin ba.”

“Gaskiya kam!”

Duk suka nufi wajen da aka tanadar musu abincin.

‘Ikon Allah! Shima wajen cin abincin har da wajenshi? To ko dai nan ne aljannar duniyar?’

Tana daɗi a zuciyarta tana ƙare ma wajen kallo.

Tunda Abulle ta yi ido biyu da shinkafar da ke cikin kulan da ake ta zuzzubashi kan faranti take haɗiyar yawu, inda tare yawun nan ake a ƙiyasi zai iya kaiwa durom biyu.

Iya zaƙuwa ta yi shi, sai dai sam Lubna bata lura da hakan ba, sai wani yanga take wajen zuba abincin, wani abun mamakin ma sai ɗigashi take tamkar za a ba yaron goye. Domin duka-duka baya wuce rabin farantin.

Ganin abun nata ba na ƙare ba ne, yasa Abulle hangame baki alamar hamma.

“To mai cikin zani! Idan kika haƙura yanzu za ki ci.”

Kallon Innon ta yi, ta kuma maida hankalinta kan ƙwaryar shinkafar, tana kuma jin kamar ta wafce kular ta afka miya ta hau loda ma cikin ta.

“Ka ji Inno! Ai ta ma yi ƙoƙari, tun karin safe gashi har wajen daya da rabi ace bata buƙaci abinci ba? A kinsan da kamar wuya, idan ke kin iya daurewa ai ita da yaranta ba za ta iya ba.”

Kallon Lubna ta yi ta ce,

“Ke ki yi ki ba mutane abinci da Allah. Kina abu kamar mai karyayyen hannu.”

Ta gama zubawa ta zuba miya da ya sha namar kaji, ga kuma ruwan lemo a kofuna da kuma ruwan gora duk a wajen.

“Ina kos lo ɗin kuma? Ko gaya za mu ci abincin?

Hajiya ta watso mata tambaya.

Da sauri ta miƙe ta nufi hanyar kicin.

‘Gosulo? Gaya? To duk wannan miya da ya rufe hinkahwar ta mene ne da za a ƙirashi da gaya? Mene ne kuma gosulon Ohho!’

Abulle ta gama tunanin zuci, lokacin da ta kai hannunta cikin farantin abincin tana shirin gauraya.

“A a, Zainab! Ba ga cokali a cikin abincin ba?”

Hajiya ta tambayeta.

“Hajiya da hannun yafi ɗebuwa ne, tattara ɗaya za ka yi ya cike hannu, cokali kuwa sai ka yi ta fafutukar tattarowa. Idan ma akai rashin sa a wajen juyewa a baki, duk sai ya zube, kinga ai gara in sa hannuna da Allah ya min ba hannun bature ba.”

Ta faɗa tana afa shinkafar a bakinta.

“To, ki jira a kawo kos lo ɗin mana, ai ya fi daɗin ci da shi.”

‘Uhmm! Ke kika ma san wani gosulo. Ni burina in gama a ƙaramin.’

Ta faɗa a zuciyarta.

A fili kuma ta yi yaƙe, ta tsame hannu a farantin tana zaman jiran zuwan gosulo.

Takaici ne ya rufe Abulle lokacin da gosuln ya iso.

‘Shegen sanabe! A ƙira abu da kwaɗon kabeji an wani lauyance masa suna wai gosulo. Koda yake ma naga an yi haɗe-haɗe, barin ji shi kuma ya yake, don in shiga gidan Mai Unguwa da sabon salo da sabon tsari. Na shigo Jinjin na waye.’

Wani murmushi ta yi, da ta tuno da gidan Sahibi Mai Unguwa.

“Nikam in ce ko dai Abulle ta ƙoshi ne? Kin bar abinci kin tafi karanto wasiƙar jaki.”

Kallon Inno ta yi ba tare da ta amsa ta ba, ta hau laftar shinkafa da gosulo.

Sosai ta ci, don abun ya kai mata karo. Ya mata daɗi sosai, sai da kowa ya tashi ya bar Abulle a wajen tana ta lodar abinci kamar jaka.

Salamar da Inno suke yi da Hajiya Sabuwa ce ta ankarar da ita, ashe har tafiyar Innon ya tashi.

Ba shiri ta baro wajen cin abincin ta taho gun su Innon.

“Hajiya don Allah kada ku bar Abulle ta wuce sati biyu don akwai gidajen da za ta je sallama idan ta dawo.”

“In Sha Allahu ba za ta wuce kwanakin ba. Lado direba zai kawota har gida.”

“Allah ya kai mu lokacin.”

“To, Allah ya tsare hanya ya kaiku lafiya, sai mun zo kenan.”

Inno ta amsa da amin.

Sai da suka iso bakin get, Ɗayyabu ya ɗauki kayan da Hajiyar ta sallameta da shi suka nufi bakin hanya neman abun hawar da zai kai ta tashe.

Tana ta addu ar samun abun hawa don biyu ma ta wuce har da minti ishirin.

Allah kiyaye ya yi mata, tare da alƙawarin zuwa ɗaurin Abulle idan lokacin ya zo. A lokacin da ta shige cikin adaidaita bayan ta mishi bayanin inda zai kai ta.

Sai daf! Magriba Inno suka isa Mai Ludaya.

Mai mashin na sauƙeta a ƙofar gida,  yara na ganinta rugo da gudu, suna  ihu da murnar dawowar Inno kamar wacce ta shekara da tafiya.

2019

Tura ƙofar gidan ta yi, yaran suka ɗebi kayan da ta zo da shi suka shigar ciki.

“Inno! Inno!! Inno!!!”

Da sauri ta ɗago daga sunkuyon da ta yi da niyyar cire ɗan kwaɗon da aka maƙala a jikin ƙofar.

“Wannan wani irin ƙirane Muntari? Na hanaka irin hakan amma ba ka ji ko?”

Ƙarasowa ya yi yana haki ya ce,

“Inno kin san meye?”

Bai jira amssrta ba ya ci gaba da faɗin,

“Wai Hamusu ne ya ɓata, yau kwana uku kenan ba a ganshi ba.”

“Ya ɓata!”

Ta faɗa cikin mamaki.

“Ya ɓata fa ka ce?”

“Eh, an nemeshi ba a sameshi ba.”

“Yo allura ne shi da za ai ɓata a rasashi? Wataƙila dai ya yi tafiya ne ba a sani ba dai ko?”

“Wallahi ɓata ya yi Inno, Baba Marka ma fa yau sau biyu tana zuwa gidan nan bata samun kowa, ta ce idan kika dawo za ta zo.”

Cikin yanayi na jimami da zancen Muntari ta buɗe ƙofar ta shiga ɗakin, zuciyarta na ta tufka da warwara.

Kaya kawai ta ajiye, ta fito ta nufi ɗakin girki don haɗa musu abincin dare, duk da kasancewar dare ya yi.

Tana tsaka da haɗa wuta a murhu ta ji ƙarar buɗe ƙofar gidan tare da sallama.

Fitowa ta yi, tare da amsawa.

“Inna Talle ke ce tafe?”

Inno ta tambaye tana mai isa gurin da tabarma ke jingine ta shimfida musu.

Wacce aka ƙira da Inna Tallen ta amsa da,

“Gani tafe, na taki sa a. Zuwana sau uku yau bakyanan wai kin je Jinjin.”

Ta faɗa tana ƙara dogara sandar da ke riƙe a hannunta na dama, na hagun kuma riƙe da kafaɗar yaron da ya rakota.

“Bismillah Inna! ku zauna. Na je raka yarinyar nan ne gidan Baffanta, kinsan abun ya matso.”

Hawayen da ya gangaro a idanunta da ke rufe ta sanya hannunta na hagu ta goge.

“Iro je ka yi wasa wajen yara, idan na gama zan yi ƙiranka mu koma.”

Ta faɗa ma ɗan jagoran tana, lokacin da ta zauna akan tabarmar.

A guje ya ɗiba kamar dama jira yake yi.

Zama Inno ta yi daga can gefe ta gaida Inna Tallen.

Shiru ne ya ratsa wajen na ɗan lokaci kafin ta ce,

“Sai kuma kika ji ɓatan Hamusu?”

“I, ɗazu ina dawowa Muntari yake faɗamin. Na ɗauka ma shirmene kawai irin na yara.”

Sake share hawayen tayi,

“Na rasa Hamusu! Na rasa shi, shine mun ɗa daya tilo da ke ɗawainiya da ni. Tunda aka ba Mai Unguwa yarinyar nan hankalinshi ya tashi, ya kasa sukuni.”

Ta tsagaita tana mai jan zuciya, da alamar jin ciwon lamarin.

“Hamusu ya kasa samun nutsuwa, kullum cikin kuka yake. Babbar ma abum da ya dameshi ya ce sam Abulle ta ƙi ta tsaya ta saurareshi ya yi mata cikakken bayanin dalilil zuwanshi gurin ‘yar gidan Mai Unguwa.”

Sake dakatawa ta yi, tana sheshsheƙar kuka.

“Tun lokacin da ya zo min da zancen samun saɓaninsu da ita, da kuma ƙin saurareshi na ce ya bari in zo in yi muku bayani, amma ya hanani. Ya ce, yasan halin Abulle, fushi kawai ta ke yi, nan ba da jimawa ba za ta sauƙo.”

Shiru ta yi, da alama hutawa take yi, gami da jimamin lamarin.

“Ikon Allah! Amma kuma Inna duk an bincika yanda ya kamata kuwa?”

Bata bata amsar tambayar ta ba, sai ma ci gaba da ta yi da zancen ta.

“Haka muka haƙura zuwa hucewar tata. Duk da haka yana ci-gaba da bibiyarta da bata haƙuri a duk inda suka haɗu. Ba mu kwatsam sai muka ji labarin cewar anba Mai Unguwa Abulle.”

Tunowa da ta yi na halin da ɗan nata ya shiga ne ya sanya ta kuma tsagaitawa.

***

Tunda aka yi mata bayanin cewar ba wani mutumin da zai fito ta cikin akwatin talabijin ɗin ta saduda, don har hannunta aka iza bisa ƙwalbar don ta tabbatar.

Idanunta da duk wani imani nata ta tattara ta bar ma kwalbar, masu jajayen kunnuwane ke ta kaiwa da komowa daga mazan har matan.

Ita dai mamaki take yi, ganin kowa tsaf-tsaf! Tambayar kanta ma take anya ko suna yin dotti kuwa? Daga jikinsu har cikin garin nasu ba wani dauɗa kamar na garinsu.

Zabura ta yi kamar an tsikareta, yayin da cikinta ya sake murɗawa a karo na ba adadi.

Zuwa yanzu kam, ta kai magaryar tiƙewa domin kuwa ba abinda take buƙata baya ga kai ma banɗaki ziyara.

A guje ta miƙe ta nufi ɗakin da aka saƙesu da Inno ɗazu, ta shige banɗaki.

Yadda Allah ya taimaketa ma, ɗazu kafin tafiyar Inno ta gwada mata randar kashi, ba don haka ba, da sai dai ta sauƙeshi a ƙasa.

Tana shiga ko kamar an buɗe bakin famfo, ga azabar murɗewar ciki.

A iya tunaninta dai tasan ba ta ci komai ba.

A wahale ta fito, hannunta na dama riƙe da ciki, na hagun kuma riƙe da ƙwanƙwasonta.

Zuwa yanzu duk ta gama laushi, don ta zaga ba adadi. Tun tana tafiya da ƙafafunta har ta dawo yi a durƙushe, ta sake dawowa da rarrafe. Ƙarshe ma mazauni kawai ta nema a cikin banɗakin domin abun ya ci tura.

Jin shirun ya yi yawa ne yasa Hajiya Sabuwa ta tura Lubna ta dubota.

Tun daga ƙofar ɗakin ta ji iska ya canza, tana kutsa kai ta ji hanjin cikinta ya fara hautsinewa, take zuciyarta ta tashi da gudu ta fice tana yunƙirin amai.

 Fallon ta dawo tana faɗin,

“Mami! Kin ji ɗakin baƙin can kuwa? Wallahi wari kamar mushen jaki.”

Kallonta ta yi tana faɗin,

“Me ya mutu a ciki to? Ina ita Zainab ɗin take.”

“Nikam ban ganta a ciki ba, ina sa kai na fito don wallahi mutum ya ɗauki tsawon lokaci a ciki zai iya tsintar kanshi a gadon asibiti.”

“Ungo nan.”

Ta ware yatsun hannunta alamar zagi.

“Kuma shine ba za ki shiga ki duba ko lafiya ba, kin ji yanayin wajen amma ki ka barta anan?”

Tsaki ta ja, ta miƙe.

“Baki da hankali.”

Ɗakin ta nufa, tana kunna kai itama ta ci karo da baƙon al’amari.

Ba shiri ta ware ɗankwalin da ke kanta ta toshe hancinta hannu bibbiyu.

Ba Abulle babi dalilinta.

‘Ina ta shiga? Warin meye haka a ɗakin nan?’

Ta tambayi kanta.

Har ta juya za ta fita sai kuma ta nufi banɗaki ko za ta ji motsinta.

Jin shiru ba alamar motsin mutum yasa Hajiya kai hannu ta ƙwanƙwasa ƙofar. Shiru ta ji ba magana, ta sake ƙwanƙwasa shiru, kawai sai ta tura.

 Abulle ta hango  zaune kan randar ta, duk jiki ba ƙwari.

Yafutota ta yi da hannu, da yake idanunta na jikin ƙofar, duk bugawar nan da take tana jin ta, kawai kuzari ne bata da shi, duk gwuiwoyinta sun mutu.

Da ƙyar ta samu ta iya miƙewa, da taimakon bango ta samu isowa kusa da Hajiyar.

Riƙeta ta yi suka fito daga ɗakin gaba ɗaya, don tanason ta yi mata magana tana tsoron buɗe bakinta ta shaƙo wari, yanzun ma ba don ƙamshin turaren da ke jikin ɗankwalin ba da abun ba dama ne.

Tana jin warin, amma ba can ba.

Suna barin wajen ta buɗe hancin, ta ja wani dogon numfashi ta shaƙi iska mai ni’ima.

“Sannu Zainab! Me ya sameki haka, lokaci ɗaya duk kin fita hayyacinki?”

Suna tafiya tana tambayarta.

Ba bakin magana Abulle, gayu yau ansha wuya, an yi ma gosulo ɗiban karen mahaukaciya shi kuma ya yi mata lalata.

Kan kujerar falon ta yi mata masauƙi, tana yi mata sannu.

“Hajiya wannan yarinyar anya ba asibiti za a kai ta ba kuwa? Dubi yadda idanunta ya dawo kamar na kifin nan Kafi zuru lokaci ɗaya.”

Cewar Afreen.

“Ai banma san me ke damunta ba, daga zuwa yau kuma sai ciwo? Me ke damunki Zainab? Ki yi magana idan na zuwa asibiti ne sai a tafi.”

Hajiya ta tambayeta.

“Mami! Anya ba Salad ɗin da ta ci bane da yawa wa ɓata mata ciki?”

Kallo Abulle ta bi Lubna da shi mai haɗe da harara, da ƙyar take faɗin,

“Ni…kuma? Yaushe na ci wani salati? Wancan wancan kwaɗon da kuka cikashi da wasu shirgin ya waren ciki. “

Dariya suka sa dukansu.

Iya wuya ta kai don haushi, wato ma ba tsusaya mata za su yi ba, dariya za su yi mata don rashin tausayi.

Juya kai ta yi ta a basu baya.

” Wai salati?”

Ta sa dariya.

“Salad fa aka ce miki, ba salati ba.”

‘Koma dai mene ne ku kusa sani.’

“Ke Lubna ya isheki! Yanzu me ke damunki Zainab?”

“Ba komai.”

Ta faɗa ba tare da ta juyo ba.

“Riƙeta Lubna ku je ɗakinki, ta yi wanka, Afreen ya kaiku Jinjin sifeshiyal hosfitan ko ruwa ne sai su ɗaura mata su bata magani ko zata ɗan ji ƙarfin jikinta.”

“Mami! Ɗakina kuma? Kada ta je ta…”

“Zan ɗaura miki mari. Riƙeta ku je. Kai ƙaramin Asabe ta je ta tsaftace can ɗakin.”

Haka ta kamata tana yatsina fuska suka tafi.

***

Inna Talle ta cigaba da magana.

“Ya shiga tashin hankali mara iyaka, haka na yi ta bashi baki ina bashi haƙuri kan cewar idan Allah ya nufa Abulle matarshi ce sai ƙaddara ta bashi ita, idan kuma ba matarshi bace ya yi haƙuri tun can haka Allah ya nufa, ya yi addu’ar zaɓi na gari. Ganin yadda nima na shiga damuwa a ‘yan tsakanin nan ne yasa ya daina tunƙarata da zancen, ganin haka yasa nima na kwantar da hankali na.”

Shiru ya sake ratsa tsakani.

Inno kan na tsugunne kan ƙafafunta da suka gama yi mata tsami, ta kasa magana sai sauraro kawai.

“Lokacin da Abulle ta fara zaga gidajen sallamar tafiya gidan aure lokacin ne muka tabbatar da ta fita rabonmu. Ranar ya zo ya ce mun sun haɗu da Abulle ta faɗa mishi maganganu marasa daɗi, ya kuma samu labarin tafiyarta Rangwangwan a ranar tunda ya fita ban ƙara jin motsin shi ba har yau, duk wanda na tambaya sai ya ce ya ganshi da kaya a leda ya ce za shi garin Dagal aike wajen kawunshi. Ashe tafiyar kenan…”

Kuka ya ci ƙarfinta.

“Shi ɗaya ke gareni, shike tallafamin saboda lalurata ta rashin ido, yau anwayi gari na rasashi, kukuma taku ɗiyar tana tare da ku…”

Ta sake rushewa da kuka.

Hamusu ya yi hijira a soyayya.

“Inna Talle ki yi haƙuri! Bansan komai game da wannan lamari ba, kwanaki dai Muntari ya faɗamin Abulle sun tafi faɗa a dandali ita da Indo, tun a lokacin na sa aka ƙirata na haneta da hakan. Ta kuma yi min bayanin dalilin faɗan cewar shi Hamusun yana zuwa gurinta, tun daga lokacin ban kuma bi ta kan zancen ba. Ko auren nan da za a yi mata da amincewar ta ba wai dole za a yi mata ba.”

Sharce majina Inna Talle ta yi daga hancinta, bakin zaninta ta sa ta goggoge hancin kafin ta ce,

“Allah ya sauwaƙe wahala, tsohuwa taga kwananta ya yi kusa. Ba nema tsakanin Indo da Hamusu, shi ɗin dai wakili ne kawai. Wanda aka cuta, ai shi ake ba haƙuri.

Haƙuri kam ai ya zama dole.”

“Wakili? Na wa kenan Inna?”

“Ɗan gidan kawunshi Saluhu dake Dagal ne ya ganta yake kamu, to shine fa shi Hamusun ke isar mata da saƙo idan ya je garin. Ya yi ƙoƙarin ya sanar ma ita Abullen amma ta ƙi sauraronshi.”

Haɓa Inno ta kama cike da mamaki da saurin yanke hukunci irin na Abullen.

“Amma ko Abulle ta yi wauta! Ban san dalilinta na ƙin tsayawa ta saurari jawabin Hamusun ba.”

“Mai hankali ai shi kan ba kaza ruwa da damina.”

“Karuwa ai bata kiwon kaza. Ki yi haƙuri za mu magantu da mahaifin nata idan ya dawo, da yardar Allah kuma za mu tayaki cigiyarshi. Ko ba Abulle ai Hamusu ɗa ne a wajenmu.”

Sandarta ta fara lalube, tana ɗauka ta muƙe tana faɗin,

“Uhmmm! Allah ya jishshemu alheri.”

“Amun.

Inno ta amsa.

Har ƙofar gida ta yi ma Inna Talle jagora, anan ta ƙira ɗan rakiyar nata ya zo suka tafi, itama ta koma ta cigaba da aikinta.

Ba dare bayan dawowar Malam Ilu, ya yi mata banganjiya da tambayar yadda ta baro mutanen Jinjin da Yayanshi, ta sanar da shi duk suna lafiya, amma basu gamu da Yayan ba ya tafi aiki. Ta faɗa mishi irin sha tara ta arziƙin da Hajiya ta yi mata.

Godiya ya yi gami da yaba ma matar Yayan nashi na halin ƙwarai da son kyautata ma jama’a.

“Ohh! Niko Malam ka ji wani batu kuma?”

Ta faɗa tana kama haɓa.

Kallonta ya yi, ya ce,

“Batu akan me fa?”

“Batun ɓatan Hamusu ɗan gidan Inna Talle jikan Yawale mai Gurguzu.”

“I, wallahi, duk gari ya ɗauka. Ko ina ka gifta zancen ake.”

“Allah sarki! Na tausaya ma halin da Inna ke ciki. Ɗazu bayan dawowata har ta ɗan ɗau lokaci ma anan muna magana kan Abulle da shi Hamusun.”

“Allah sarki! Abun ai akwai al ajabi, yaro dare ɗaya ya ɓace ɓat! Kamar wanda aka yi ma kurciya? Wannan abu da mamaki.”

“Wallahi kuwa, ta sanar mun da komai, ashe shi Hamusun ba neman ‘yar gidan Mai Unguwa yake ba, ɗan gidan kawunshi yake zuwa ma aike wurinta, da Abulle tagansu tare shine fa ta hau dokin zuciya, ya yi ƙoƙarin sanar da ita gaskiyar magana ta ƙi bashi haɗin kai. Da ya bita ta ƙi sauraronshi shine ya gudu wai ba zai iya ganin auren Abulle da wani ba.”

“Ka ji shirmen banza! Duk tarin matan garin nan na Mai Ludaya ba zai zaɓi wata ba sai Abuwa? Wannan ai shashanci ne, dama can ya yi niyyar shiga bariki ne kawai. Ba wai rashin auren nata ba. Bana ma son sake jin zancen daga bakinki, tun wuri ki haƙa rami anan ki birne shi, kafin gari ya ɗauka.”

“To, amma Malam maihaifiyar shi yaron fa?  Tana cikin wani…”

“Dakata don Allah!”

Ya faɗa yana daga mata hannu.

“Na faɗa miki ki yi gum da bakinki, ki tayata da addu’a Allah ya bayyanashi kawai. Domin matuƙar zancen nan ya baza gari to, ina mai tabbatar miki fita ma sai ya gagaremu, ki barmu dai mu ji da wanda ake yi mana yanzun muka toshe kunnuwanmu.”

Cikin marairaice fuska ta ce,

“Shi ke nan. Allah ya bayyana shi, ya yi mishi zaɓi da mafi alkairi.”

“Faƙat! Amin.”

Ya kaɗe ‘yar shararshi ya fice daga gidan.

****

_Fadar Mai Unguwa_

“Sarkin fada! Yanzu ya kake ganin za a tsara lamarin bikin nan? So nake a yi biki na kece raini.”

Kallon Mai Unguwa ya yi, da yake ta mamula gole a bakinshi.

“Ranka shi daɗe! Ai kasa a je cikin garin Jinjin a lafto shinkafa a zo a dafa a bi gida-gida ana rabashi, matuƙar akayi hakan to fa ina mai tabbatar maka da cewar wannan biki zai kafa tarihi matuƙa a cikin garin nan da kewayenshi.”

Wangale baki ya yi, irin a dole yana dariya ɗin nan, ga haƙoran gaba, sama da ƙasa guda huɗu duk babu.

“Sarkin fada shi yasa nake son zama da kai. Ga ka ƙarami sai  iya tsari wallahi.”

“Ai Ranka shi daɗe, na fi kowa san kasance a zaman fadar nan.”

Murmushi Mai Unguwa ya yi, ya ce,

“Zama waje uku suna da amfani. Zama a makaranta, zama a mahauta, da zama a fada. Zama a makaranta ko ba ka yi karatu ba, idan ak yi abun addini ka ji. A mahauta in an fiɗa, ko fince ka yi. A fada kuwa za ka ƙaru da maganar tsofaffi don nan ne matattarar magana.”

“Gaskiya ne! Ina ƙaruwa kam sosai a fadar nan.”

Nan suka ci gaba da tattaunawa.

Leda biyu na ruwa Abulle ta sha  da kuma allurai biyu bayan dogun artabu da akasha wajen sa mata ruwan da tsira mata alluran.

Ba kunya ba tsoron Allah ta zage ta yi ta zabga kururuwa tamkar wacce za a zare ma rai.

Sai wajen ƙarfe ɗaya saura na dare aka sallemesu. Shima dalilin matsawar da Lubna ta yi ma likitan, don ba zata iya kwana a asibitin ba.

Itama Abulle tunda ruwa ya ratsata, jijiyoyin jikinta ya saki, ta ji ta ƙagu su koma gida, don ta gaji da kwanciya a gado mai tafiya. Ko yaya aka ɗan muskuta sai kaga gadon ya matsa.

Kamar ba ita ce ɗazu aka sha gwagwarmaya wajen sanya ruwan ba.

Gari ya yi shiru, kai ka ce ba wani ɗan adam da ya wuni yana zirga-zirga a wajen.

Tituna ma ɗai-ɗaikun ababen hawa ne ke giftawa.

Ba ka jin motsin komai sai kukan kwaɗi da wasu ƙwarin.

Ƙofofin gidaje ma a rufe, haka ma shaguna, sai dai a wasu ƙofofin gidajen da yake mallakin gidan almajirai, zaka iya hangosu shimfiɗe kan tabarma suna ta sheƙa barci. Wasu kuma a ƙofar shagunan mutane.

Tunda suka fara tafiya waje ɗaya ne kawai suka ga mai shayi, da wasu tsirarun mutane da basu wuce uku ba.

Dare kenan! Mahutar bawa.

Kowa ya bar gida-gida ya barshi.

Hakan ce ta kasance.

Hamusu ma yana ɗaya daga cikin mutanen da ke ƙawance  a ƙofar wani shago, a tsakiyar bencin da aka tokare ƙofar shagon bayan an rufeshi da kwaɗo.

***

Tun ranar da suka yi sa’insa da Abulle ya tattara kayanshi ya bar mahaifarshi, ya fita neman kuɗi don huce takaicin abunda Abulle ta yi mishi.

Yana da yaƙinin kuɗi ta bi, shi yasa ta amince da auren Mai Unguwa. Inda yana da su da yanzu suna tare.

Ya shigo cikin garin Jinjin ba tare da yasan kowa ba, hasalima karo na farko kenan a tarihin rayuwarshi da ya taɓa zuwa.

Sosai yaga bambanci da garinsu. Kowa a nan harƙar gabanshi yake yi, idan zaka wuni baka sami ɗigon ruwa ka jiƙa maƙoshinka ba, ba mai baka, basu damu da kai ɗin baƙo ba ne, ya saba gani a garinsu idan aka yi baƙo an rinƙa ina asaka da shi kenan.

Kwananshi biyu yana garari a cikin tasha, ganin ‘yan kuɗaɗenshi na shirin gangarawa su barshi, yasa ya nemi mafita daga wajen wani da suke kwana kullum a tsakiyar motocin da ake ajesu idan dare ya yi.

Gauta yake kasawa a tire ya yi ta yawo kan tituna yana sayarwa.

Shine sana ar da Hamusu ya fara yi.

Yau kwananshi biyu kenan da fara sana ar, sai dai yanzu ya bar cikin tasha ya dawo kwana ƙofar wani shago.

Har ya fara tunanin canza sana ar, domin yau ba ƙaramin galabaita ya yi da zafin rana ba.

Sai dai kuma ba ya da wani ishashshen jarin da zai kama wani sana ar.

Juyi kawai yake yi, sam! Barci ya ƙi ya ɗaukeshi sai ma wasiƙar jakin da yake ta karanta.

“Allah sarki Inna ta! Ko yanzu a wani hali kike? Ki yi haƙuri na tafi na barki ba tare da izininki ba, na tafi na barki ba tare da tunanin lalular makanta da kike fama da shi ba. Ban yi hakan domin in sanya ki a damuwa ba, sai don sama wa zuciyata mafita, Inna ba zan iya zama cikin Mai ludaya a ɗaura wa macen da nake so aure da wani ba, zuciyata ba zata gaza ganin hakan ba Inna! Ki fahimceni, zan dawo gareki nan ba da daɗewa ba, zan dawo, zan dawo…”

Maganar da yake yi kenan a hankali cikin sautin kuka, zuciyarshi kuma na ƙuna.

***

Barci sosai Abulle ta sha akan lafiyyayen gadon da ya sha shimfiɗi, ba kamar gadonta da aka yi shi da yayi aka ɗinkeshi da buhu ba.

“Ke wai ba za ki tashi ba ne?”

Lubna ta faɗa tana ɗaka mata duka a sangalalin ƙafafunta.

Tashi ta yi tana miƙa, tana hararar Lubnan da gefen ido, don ba ta so tashi yanzu ba.

“Lafiya kika tsareni da ido? Ko baki gama warwarewa ba ne?”

‘Wannan baiwar Allah akwai buhun masifa! Inaga da ita ke da gidan ma ko wuni ɗaya ba zan yi ba.’

Ta faɗa a zuciyarta, a fili kuma ta ce,

“Ras nake! Allah na tuba ma ai inaga na fiki lafiya.”

Ta ƙarashe maganar tana sauƙa daga kan gadon.

Zaro ido Lubna ta yi,

“Me kika ce?”

Ta tambayeta.

“Cewa na yi, ai yanzu ko garin nan aka ce in zagaye da gudu zan iya.”

Tsaki ta yi, ta koma ta kwanta a cikin kujerar da ke cikin ɗakin.

“Ina kuma za ki je? Banɗaki za ki shiga, akwai sabon  burosh da makilin na ajiye miki.”

‘Buroshi? Makel? Su kuma suwaye hakan?’

Ta tambayi zuciyarta yayin da ta nufi ƙofar banɗakin.

Duk dube-dubenta ta yi bata fahimci komai ba, don banɗakin cike yake da shirgi.

Taɓe baki ta yi, ta ce,

“Shima banɗaki sai an yi mishi jere tsabar samun waje. Wannan kwalayen idan na samu na jeresu a kan sif ɗina ba ƙaramin kyauwu za su yi ba.”

Ta ƙarashe maganar tana murmushi.

“Ce miki a kayi ana magana a toilet ne kam.”

Daga can ta ji Lubna na mata magani.

“Ohho miki kuma! Ni na san wani tulat ne.”

Ta faɗa a hankali, sannan ta ɗauro alwala ta fito.

“Kawai ki goge baki ki yi alwala shine ki ka zauna surutu?”

Turo baki ta yi da yatsina fuska, haɗe da hararar ta ta gefe don ta tsani masifa, da alama wannan mai farar fuska kamar shinkafar ba za su zauna inuwa ɗaya da ita ba.

“Yo, naga dai alwalar haɗe take da wanke baki, kuma duk na yi. Sallah zan yi yanzu.”

“Kina nufin ba ki yi burosh ɗin ba?”

Yadda ta zaburo kai ka ce ashariya Abullen ta yi mata

“Magana ta gaskiya ma ni ban sansu ba.”

Ta bata amsa tana sanya hijabin da ta gani kan sallayar ta tada iƙama.

Shiru ta yi ganin ta fara sallah, zuciyarta cike da tunanin wai ba tasan man goge baki ba. To su da me suke wanke bakin?

“Ina kwana?”

Shine kalmar da ya katse mata tunanin.

Kallonta ta yi, tana naɗe hijabin.

“Ba dai kin idar da sallar ba ne?”

Itama kallon ta ta yi,

“Na idar mana.”

“Malam raka a biyu fa za ki yi, ba ɗaya ba.”

Kallon rashin fahimta ta yi mata.

“To, ai biyun na yi.”

“A hakan? Kafin kiftawar ido da buɗewa har kin dungura kin tashi! Da aiki. Wannan shi ake ƙira ‘yar mubi ba yawa sai lada.”

Yatsina fuska ta yi,

‘Koma ‘yar waye ke kika sani.’

Ƙofa ta nufa da niyyar fita, tambayar da ta jefo mata yasa ta tsayawa.

“Na ce ina za ki je.”

Ta sake maimaita mata tambayar.

“Zuwa gaida masu gidan, in kuma ci abinci.”

“Ba ki goge bakin ba ne za ki ci abinci?”

Cikin jin haushi yasa ta ce,

“Wani burushi da makel da kike faɗa ma ni ban sansu ba.”

Fuska cike da mamaki da kuma don darawa da sunan da ta ƙira abun goge bakin  ta ce,

“To, da me kuke wanke bakin a can?”

“Gawayi da gihiri muke dangwala a jikin soson buhu mu yi ta gogawa a haƙoran. Nan gidan ko ban ga alamar murhu ba balle in samu.”

Bata ce komai ba ta miƙe ta nufi banɗakin, sai da ta kai ƙofa sannan ta sa hannu ta yafutota.

Makilin ɗin ta matsa a jikin burunshin ta miƙa mata,

“Ki dirje duk wani lungu da saƙo na cikin bakinki har kan harshenki.”

Tana gamawa ta fice ta bar Abulle a banɗakin.

“Wannan akwai shegen iyayi, in da ita ke da gidan inaga ko wuni guda ba zan yi ba za ta korani gi…”

“Wai waya faɗa miki ana magana a banɗaki.”

Shiru ta yi, ba amsa.

Ta ɗau tsawon lokaci tana tunanin yadda za ta zura wannan abun cikin bakinta, tsoro ma take kada kifiyoyin robar su caccake mata dadashi.

Lakatar man goge haƙoran ta yi, wani yaji-yaji, zaƙi-zaƙi ne ya gauraye mata baki.

Tas ta shanye makilin ɗin kan burushin ta sake ɗauko, gudar makilin ɗin ta rinƙa matsowa tana sha tana jan yaji, idan ta ja sai ta ji iska mai sanyi yana hura mata cikin baki.

“Mazauni kika samu a ciki ne kam?”

Lubna ta watso mata tambaya daga can.

Zabura ta yi,

“Gani zuwa.”

Da sauri ta zura magogin cikin bakinta.

Ta dai yi yadda ya samu ta ɗauraye bakin ta sake tatso man ta lashe kafin ta fito.

“Au! Duk wannan zaman naki ba wanka kike yi ba?”

“Wanka kuma da sassafen nan kamar wacce ta yi fitsarin kwance? Jiya ma ai na yi wanka kafin mu taho nan.”

“Ikon Allah! Kenan acan ba kullum kuke wanka ba?”

‘Wanka kullum! Wa yaga ƙwaɗi.’

A fili kuma ta ce,

“Ina muka ga ruwan da za mu yi wanka kullum.”

“Uhmmm! Je ki.”

Ta fice, don dama ta gaji da yawan tambayoyin nan kamar a gaban alƙali.

Ta jima zaune a falon ba kowa sai  Lantana mai aiki da ke share-share da goge-goge da kuma tibi da ke ta aiki shi ɗayanshi.

Gajiya da zaman ta yi, ga kuma yunwa da ya dameta.

“Baba! Don Allah an gama abun karyawa ne?”

Ta tambayi Lantana dake goge tibi.

“Abinci a yanzu ƙarfe takwas da rabi? Ai da sauran lokaci ‘yannan, da yake yau duk suna gida sai ƙarfe goma ko sha ɗaya za su fito karyawa. Ki koma ki kwanta ko ki je ɗakin girki ki samu wani abun ki ɗan taɓa.”

Langwabar da kai ta yi, ta kwantar kan hannun kujerar tana faɗin,

“Na shiga uku! Wallahi zan iya mutuwa da yunwa idan na kai wannan lokacin.”

Kallo Lantana ta bita da shi, ta ce,

“Ki shiga ki sami Saude mai girki ta baki ko ruwan shayi mana.”

To, kawai ta ce, ta miƙe jiki ba ƙarfi.

“Sannu da aiki Inna!”

Juyowa ta yi ta kalli mai yi mata sannun.

“A’a! Baƙuwarmu har kin tashi ne?”

“Uhmmm! Ina kwana.”

“Lafiya, yaya jikinki?”

“Da sauƙi. Dan Allah akwai abinci? Yunwa nake ji.”

Ta faɗa kamar zata yi kuka.

“Wai! Gashi yanzu nake ɗaurawa. Ko in haɗa miki shayi ne?”

“Eh.”

Ta amsa da sauri.

Tana tsaye a wajen ta haɗa mata a wani ƙaramin kofi ta miƙo mata.

Karɓa ta yi tana godiya a fili, a zuciyarta kuma haushi ne ya gama rufeta.

‘Wannan ne wai abunda zai riƙe ni har wani lokaci? Alƙur’an fitsari ɗaya zan yi in zubar da shi.’

Kafa kai ta yi ta kurɓe.

‘Da wannan gara ruwa ma wallahi, ban ji komai ba nikam.’

“Ga kofin na gode.”

Ta fito tana tunano ɗumamen tuwon dawa da kokon Inno! Da yanzu a gida take da ta manta da ta karya, da yanzu a gidansu ne miyar tuwon rana ne a kan wuta.

Amma anan wai yanzu ne ma ake ɗaura girkin safe, ba za ta iya ba.

Gara ma goben ta yi ta koma gida, kafin yunwa ya mata illah.

Falon ta koma ta zauna ta fara kallo, sai dai sam bata jin daɗin kallon.

Ɗaki ta nufa, ta tarar da Lubna har ta yi barci.

Tsaki ta ja a hankali, a zuci kuma ta ce.

‘Barcin asara.’

Ganin ba abunda za ta yi yasa ta koma kan kujerar cikin ɗakin ta kwanta, hannunta riƙe da ciki.

Juyi kawai take na rashin sabo da kwanciyar, ga kuma uwar yunwa.

Ji take kamar ta ƙwala ihu ko duk mutanen gidan zasu tashi.

Idan ba iskanci ba, ace duk barcin da aka yi da dare bai ishe mutum ba, sai ya sake komawa.

Ba ta fatan ma tayi dogon zama a irin wannan wajen da yunwa zai yi ajalinta.

Turo ƙofar ɗakin aka yi, Hajiya ce ta sha ado kamar zata gidan biki.

Jin buɗe ƙofar yasa Abulle ɗagowa.

“A’a! Ashe ɗiyar tawa ta tashi? Yaya jikin naki?”

“Na jima da tashi, na ji sauƙi. Ina kwana?”

“Lafiya, yaya ƙarfin jikin naki?”

“Da sauƙi.” Ta bata amsa a fili.

A zuci kuma ta ce,

‘Ina wani ƙarfin jiki, ban sanya ma ciki komai ba.’

“Allah ya ƙara sauƙi.”

“Amin.”

Har ta juya zata fita, ta juyo ta ce,

“Ki tashi Auntynki ku zo ku ci abinci, ga Babanki ma ki zo ku gaisa, jiya mun je asibiti da shi kina barci.”

“To.”

Ta bata amsa, ta je har gaban gadon ta miƙa hannu ta bubbuga ƙafafunta.

Idanuwanta ta buɗe, ganin ta tashi yasa ta faɗa mata saƙon Hajiya.

“Na ji ta. Ki je sai na yi wanka.”

‘Sannu kifi.’

Ta miƙe tabar ɗakin.

Fitowarta ma ba kowa a falon.

Tunani take ina shi mai gidan yake da zata gaisheshi? Ita ba ko ina ta sani a cikin gidan ba.

Kicin ta shiga ta tambayi su Lantana, ita ta fito ta nuna mata wani ƙofa da zai kaita har ɓangaren Alhajin.

Dogon lungune da ya sha sumuntin bature, (Tayis) samɓal ta miƙe ta fara tafiya tana kalle-kalle zuciyarta fal tunanin irin kayan more rayuwa da ke gidan, su kuma suna can cikin karmami.

Ba tayi aune ba, sai ji ta yi santsi ya kwasheta ya timata da kasa, take ta baje a wajen ta yi zaman ‘yan biri, sakamakon goge wajen da aka yi bai gama bushewa ba.