🔱 ṨÄQÄŔ ṨÖ🔱🔱
              ⚜️🗝️  ( _love cub_ ) 🗝️⚜️

Mallakin :Queen Nasmerh
Marubuciyar 👇
1:Ayisherh
2:Mrs Bilal
3:Mrs Bilal continuation
4:Barrister Muhammad
5:Wani hanin ga Allah
6: Fayroz
7:Hajna

And now 8:SAQAR SO.
🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER’S ASSOCIATION🌙✨*

*”’We are the moonlight writers we shine all over the world.”🌍’* ✍️✍️

بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

EPISODE 9-MIE AMORE
°°°°°°°°°°💗°°°°°°°°°°

Kimanin sati ɗaya kenan da aka rufe Leesha, Pappy ya ɗauko manya-manyan lauyoyi da jami’an bincike, amma har yanzu ba’a gano komai ba, idan ku ka ga yadda Leesha ta canza, wani ko ance itace bazai yadda ba, fuskarta duk ta faffashe, amma har yanzu ƙarfin halinta be canza ba, Pappy kuwa abubuwa sai yin ƙasa su ke yi kullum da matsalar da ke faruwa a Abeer company, haka yasa aka rufe gurin har a komai ya daidaita, ɓangaren marayu kuwa kullum addu’ar su Allah ya toni asirin waɗanda su ka yiwa Leesha haka, duk wanda ya ga Leesha a yanzu in dai kana da imani dole sai ka zubar mata da hawaye.

   Kamar kullum yau ma dukan ta ake yi, zuwa yanzu Leesha ta saba da dukan da ake mata, dan sun bata horo yadda baku tsammani, “sau nawa zan faɗa muku ban san yadda wannan abun ya faru ba, bani da masaniya akan yadda abun nan ya shigo jaka ta, in taƙaice maku magana ni ba ma’abociyar son shan magani bace, ballanta wannan “ta ƙarasa maganar cikin dakiya da ƙarfin hali, wata ƙatuwar sanda ya buga mata a tsakiyar baya, wanda yayi dai-dai da zubuwar jini daga bayan, cikin kuka ta miƙe, faɗuwa tayi ba shiri, “ka kashe ni kawai na huta, ka kashe ni!” ta faɗa da iya ƙarfinta tare da ɗaura kanta a guiwa ta cigaba da kuka, shi kuwa  ko kaɗan ba imani a ranshi ya hau dukanta ta ko ina na jikinta, bata ɗago ba kuma bata fasa yin kuka ba, sai da ya mata liƙis sannan ya sake tambayar ta “yanzu kin shirya faɗin gaskiya “, cikin takaice ta ɗago, ta buɗe bakinta da ke zubar da jini tace “saboda kawai mun tsone muku ido shiyasa kuke tsaurara komai akan mu”, hannunshi ya ɗaga ya watsa mata wani mahaukacin mari, duk da tabon da ke fuskarta be hanani ganin kwanciyar ƴan yatsun shi a fuskarta ba, gaskiya Leesha ta faɗa, duk garin nan ba wanda su ka tsana irin Alhaji Abeer da ƴar shi Leesha, shiyasa kowa burin shi su yi laifi , domin hukuncin su bazai zo da sauƙi ba, kuma haka yayiwa wasu mutane daɗi, domin kuwa Leesha itace raunin ahalin Abeer, idan kana so kaga tashin hankali to ka taɓa Leesha, a lokacin ne Alhaji Abeer zai nuna muku asalin shi, “girman kan ki bazai bari ki faɗi gaskiya ba ko “, shiru tayi bata ce komai ba, sai ma kallon shi ta ke yi a tsats-tsaye kamar ta kashe shi tsabar haushi, wani wawan mari ya sake sakar mata, “bazaki ce komai ba” ya faɗa, “to me zance ka ɗauka yadda kake so “.

   Jirgi ne ya sauka a filin jirgi, mutane sai fitowa su ke yi, sai da kowa ya gama fitowa sai  ga wani saurayi kyakkyawa, ni dai a rayuwata ban taɓa ganin mutum kyakkyawa irin shi ba, yana da faffaɗan ƙirji, fuskarshi kuwa komai ya ji, hancin shi har baka, lips ɗin shi sunyi matuƙar yin kyau, maganar gaskiya idon shi irin sexy eyes ɗin nan ne waɗanda da ya sauke su a cikin idon ki ƴar uwa ki sa ranki dole ki faɗa son shi, amma mutum ne da baya bari a haɗa ido dashi, bai cika son magana ba, sannan shi ɗin haɗaɗɗe ne yadda baku yi tunani ba, tsayawa faɗa muku yadda ya haɗu ɓata lokacin ne dan yanzu ma na fara gani, saukowa yake yi cikin takun shi irin na jaruman mazan nan, sanye yake da kaki fari, kayan sun yi matuƙar amsar shi, a kan rigar naga an rubuta CAPTAIN AAFTAB da manyan haruffa.

   Tafiya yake yi yayin da yake sa mutane yin tuntuɓe, wasu ƴan mata sai faman kallonshi su ke yi, Aaftab mutum ne mai kwarjini da ƙarfin izza, mutum ne da duk lokacin da ya zo guri zai warware matsalar da ke gurin, buɗe mishi mota aka yi, kai tsaye gidan horon sojoji su ka nufa.

   Wayar shi ce tayi ringing “hello Pappyn Leesha, na iso “ya faɗa kamar bashi ke maganar ba, Pappy yace “nagode sosai Aaftab”, be ƙara cewa komai ba, Pappy kuma bai damu da rashin maganar ba, dan yasan Aaftab mutum ne mai kwarjini, duk yadda kake jin kanka idan Aaftab yayi magana to tabbas zaka saurare ta, masu karatu in taƙaice muku bayani Aaftab idan zai yi magana sai ya tabbatar ta zo a yadda duk min doloncinka da rashin fahimtar zance mutane to zaka gane inda maganar shi ta nufa.

  Dai-dai ofishin ya tsaya, a hankali ya ziro ƙafar shi tare natsuwa ya fito daga motar, ba abunda yake burin gani irin MIE AMORE(my love-masoyina / masoyiyata ) , yayi matuƙar kewar ta be manta ba, tun ranar da su ka yi faɗa da ita bai sake kiranta ba, itama  ɗin tun ranar bata sake neman shi ba, yasan halin kayan shi tun ba yau ba haka take, gashi ko sallama be mata ba lokacin da zai wuce India, yanzu shekara 5 kenan, tun da yaje karatu a akan tuƙin jirgi (Pilot), gashi ya dawo, addu’a ya ke Allah yasa Mie Amore ta saurare shi, murmushi yayi a hankali ya furta “Leesha kenan, rigimammiyar masoyiyata”.

  Ciki ya nufa kai tsaye babban ofishin da ke gurin ya nufa, wanda nan shugaban sojoji ya ke, buɗe ƙofar yayi tare da shiga ciki, da sauri shugaban ya tashi ganin Captain Aaftab, matuƙin jirgin da ƙasar India ke alfahari da shi, kuma ƙasashe da dama suna son yin aiki da shi, “sannu da zuwa Captain “shugaban sojojin ya faɗa yana miƙawa Aaftab hannu, kallon shi kawai Aaftab yayi ko murmushi babu a fuskar shi, ballantana yayi tunanin zai bashi hannu, dan haka ya sauke hannun shi tare da faɗin “ ya zan taimaka maka”, gyara zama Aaftab yayi, kamar bazai yi magana ba sai yace “ me zaka faɗa idan ka ɗauki Leesha Abeer ka miƙa a kotu? “, “zan ce mun kamata da powder iblis ne” shugaban sojojin wato Ɗan Ladi ya faɗa, Aaftab yace “idan lauyanta ya maka tambaya akan case nawa ka kama irin haka kuma baka miƙasu kotu ba, me zaka ce? “, shiru Ɗan Ladi yayi, Aaftab yace “shin kana da hujja ne a kanta?, wai in tambaye ka ma idan Leesha bata da laifi da wane ido zaka kalli ahalinta, da duniya, haƙƙin da aka ɗaura maka na neman gaskiya bai da amfani, baku amfani da hankalinku kuyi bincike sai dai kawai ku yi hukunci, shine rantsuwar da kayi na kare haƙƙin mara laifi da hukunta mai laifi a ranar da aka baka wannan aikin ko kuwa dai ka canza ra’ayi ne ta hanyar cin zalun, da yin abunda kake so, ta hanyar ba mai gaskiya laifi, idan kuna haka ta ya zaku gano gaskiya? , baka da ikon kama Leesha har sai kayi bincike ka tabbatar da gaskiya zargi ne kawai, bayan haka ma inda ƴarka ce zaka yadda a mata haka, a kan idon ku aka ci zarafin Alhaji Abeer a nan offishin, shin miyasa baku kare shi ba?, aikin ku ne ku ba kowane mutum kariya, amma kuna gani aka dake Leena Abeer, wanda haka yayi silar kwanciyar ta asibti, akan me duk haka ke faruwa” Aaftab ya ƙarasa maganar yana kallon  Ɗan Ladi, “kayi haƙuri yallaɓai, ya kamata muyi bincike kafin yanke hukunci, yanzu zamu baka belin ta, har a gama bincike, idan mun gano ita mai gaskiya ce zamu watsar da ƙarar ta hanyar saka mai laifin ƙara, idan kuma mun gano ita mai laif…….., bai samu damar ƙarasa maganar ba sanadiyyar wani mugun kallo da Aaftab ya bishi da shi.

    Umurni aka bada akan a fiddo Leesha Abeer, za’a bada belin ta akan na’ira dubu ɗari, Aaftab ne ya biya kuɗin, sannan ya saka hannu, ba tare da yace komai ba ya miƙe tsaye, wanda haka yayi dai-dai da shigowa Leesha da ko tafiya ma bin bango take yi, ita kaɗai ta san irin raɗaɗin da take ji, cikin sauri ya isa gurin ta, riƙe hannun ta biyu yayi yana kallonta, duk jikinta tabo ne, sannan ko ina na jikinta yayi ja, ga cizon sauro ga duka, ga rashin barci, idonta duk sun faɗa, gashin kanta duk ya watse, rungume ta yayi da sauri wanda yayi dai-dai da zubowar hawayenta, “Mie Amore, har yanzu baki daina fushi dani ba “, ba tace komai ba, taɓa jikinta yayi yaji yayi zafi sosai, koda ya ɗago fuskarta da niyar tambayar ta bata lafiya, ganin idonta yayi a rufe, girgiza ta ya shiga yi, amma inaa ta suma, juyowa yayi ya kalli Ɗan Ladi yace “idan wani abu ya same ta duk ma’aikatan da ke gurin nan har da kai ma zan tabbatar an sauke ku “, be jira me Ɗan Ladi zai faɗa ba ya fita da sauri, ɗauke da Leesha a hannun shi, babbar asibitin da ke garin barno ya isa, cikin gaggawa aka karɓi Leesha ganin yanayin da take ciki, Aaftab kiran su Pappy yayi ya sanar da su suna asibiti da Leesha, inda likitoci suka bata taimakon gaggawa.

  Ba’a ɗauki lokaci ba su Pappy suka ƙaraso asibiti, “Aaftab ina Leesha “Ummie ta faɗa cikin kuka, Aaftab nuni kawai ya mata da ɗakin da aka aje Leesha, da sauri Ummie da Leena suka isa gurin bakin ƙofar suka tsaya, ta ƙofar zaka iya ganin komai, oxygen ne a hancinta dan bata iya numfashi, ƙoƙari bata taimakon gaggawa su ke yi, Leena kuwa faɗuwa tayi gurin ƙasa, ta shiga yin kuka, “wayyo Leesha, Allah ya saka miki, insha Allah gaskiya zata bayyana “ta ƙarasa maganar cikin ƙunci, cikin takun shi na ƙasaita ya iso gabanta ɗaga ta yayi yace “ki kwantar da hankalinki Leena”, juyowa tayi ta kalli Aaftab kamar ba shi yayi maganar ba, a fuskar shi zaka iya ganin tashin hankali da takaici, haɗe da fargaba duk a tattare da shi, fargaban shi be wuce rasa Leesha ba, Leena ta sani sarai sai dai ta nuna wa Aaftab tare aka haife su da Leesha, amma bazata nuna mishi son Leesha ba, dan idan ba Leesha ba ba wanda zai shiga damuwa irin wannan Aaftab ya baro aikin shi ya dawo, son Leesha halitta ne a zuciyar shi, Leena bata ce da shi komai ba sai wucewa da tayi ta samu guri ta zauna, juyawa yayi ya koma daga can gefe ya tsaya, Pappy ne ya dafa kafaɗun shi yace “nagode Aaftab, tabbas tun Leesha na ƙarama kake saka mata, ta hanyoyi daban-daban, tabbas ka nuna mata so, ina godiya sosai “, gaɗa kawai yayi a ranshi bai ga wani abun godiya ba, saboda aikin shi ne ya kare ta, bayan haka ma ita ɗin jinin shi ce.

    Suna tsaye likita ya fito “kai ne ka kawo mara lafiya ko” ya faɗa yana nuni da Aaftab, gaɗa Aaftab yayi alamar eh, “to ka biyo ni office ɗina za muyi magana”, bin shi yayi, guri ya samu ya zauna yana fuskantar likitan, “ina jinka likita” ya faɗa cikin natsuwa, “Leesha Abeer ta samu kariya biyu a hannunta, ɗaya a kafaɗarta, ɗaya a agogon hannunta, sannan ta samu buguwa a kai wanda ba lallai ta gane ku ba idan ta farfaɗo, sannan ta samu kariya a ƙafarta”, dafe kai Aaftab yayi yace “ohh Allah na, yanzu tsawon wane lokaci zata ɗauka a haka?” likitanp yace “ a gaskiya zata ɗauki lokaci bata dawo hankalinta ba, amma idan ta daɗe shekara ɗaya, amma idan kunyi sa’a nan da wata biyar zuwa shida zata dawo”, shiru Aaftab yayi sai can yace “amma likita zamu iya komawa gida da ita, zamu ɗauko mai kula da ita “, likita yace “eh ba matsala, amma duk sati zaku riƙa zuwa da ita asibiti ana duba ta”, “ohk likita mun gode “Aaftab ya faɗa, tare da fitowa, a wajen office ya samu pappy da alama ya ji duk abunda likitan ya faɗa, domin kuwa idon shi sun yi ja alamar kuka yayi, da kallo ya ke bin pappy, Pappy yace “ haka na nufin jajirtacciyar ƴata bazata iya tunani ba”, Aaftab yace “ komai zai wuce kuma insha Allah zata tuna ka “ya faɗa tare da wucewa, su Ummie ya sa ma a ƙofar ɗakin da Leesha take, nan yace su zo su wuce, duk yadda Ummie ta so sanin me likita ya faɗa Aaftab be bata fuskar da zata tambaya ba, Leena ma bata damu ta tambaya ba dan tasan da akwai matsala Aaftab zai faɗa.Anan zan dasa aya……………………… ✍️

Ni ɗinnan na rubuta wannan littafin da dukkan nin zuciyata, a yaushe zan iya kawo muku abunda ba kuyi tunani ba..

Ina matuƙar alfahari da ku masoya na, kun nuna min soyayya yadda banyi tunani ba, a wannan littafin nasan asalin abunda ake cewa masoyan gaskiya, kun ƙarfafa min guiwa yadda banyi tunani ba, bazan ce na sa duka baiwa ta anan ba amma dai na kwatanta hakan saboda soyayyata ma littafin, na ɗauki lokaci ina tsara labari, tun shekarar da ta wuce, tun a lokacin na ji ina son littafin, ban yi tunanin zai karɓu a gare ku ba, amma alhamdulillah kun nuna min soyayya, kuma kun min bazata ta hanyar karɓar labarin nan fiye da yadda banyi tunani ba, da badan ku ba da bazan rubuta ba, dan haka nake godiya gare ku.

Kar ku manta Queen Nasmerh taku ce har abada.

Ina sonku da zuciya ɗaya.

Mu haɗu a next episode dan jin yadda zata kaya.


ALQALAMINA✍️YAFI KOWANE TAKOBI ⚔️KAIFI