By Sani Ibrahim Maitaya, Gusau

Wata Babbar kotun shari’ar Muslunci dake unguwar Yarima, a Gusau babban birmin jihar Zamfara ta yankewa wasu mata su ukku hukuncin daurin shekaru biyar da wata shidda, a gidan gyara hali, saboda samun su da laifin tozarta Alƙur’ani mai girma.

Da yake karanta jawabin yanke hukuncin, Alƙalin kotun mai Shari’a Garba Sahabi, ya ce an yanke masu hukuncin ne akan samun su da laifin haɗa baki wajen aikata laifi, da zindiƙanci, da tada hankalin jama’a, da kuma wulaƙanta wasu littattafan addinin musulunci, da suka haɗa da Alƙur’ani mai girma, da muwaɗɗa malik.

Alƙalin ya ce duka waɗannan laifukka ne da suka saɓawa kundin tsarin shari’ar Muslunci ta jahar Zamfara, sashe na 122, da 123, da 287, da kuma sashe na 400.

Waɗanda aka yankewa hukuncin sun haɗa da Rabi Bello, da Hazira Bello da kuma Hafsat Isa.

Mai Shari’a Garba Sahabi ya bayyana cewa, kotun ta yanke masu hukunci ne sakamakon kasa kare kan su daga dukkanin laifukkan da ake karar su da zargin suna aikatawa.

Ya kuma ƙara da cewa waɗanda ke gabatar da kara sun samu nasarar gabatar da cikakkun shedu waɗanda kuto ta gamsu da su.

Alƙalin ya ƙara da cewa zasu fuskanci waɗannan hukunce-hukunce daya-bayan-daya.

Da yake zantawa da manema labaru bayan fitowa daga kotun, lauyan dake kare waɗanda ake ƙara Barista Jamilu Ahmad, ya ce zasu ɗaukaka ƙara, domin a cewar shi masu shedu bangaren masu saka ƙara basu tabbatar da aikata laifi ga waɗanda ake karar ba.