Gwamnatin Jihar Zamfara ta Umurchi Kungiyar ‘Yan Jarida ta Kasa Reshen jihar Zamfara da su Dakatar da Zaben Kungiyar ta aka shirya Yi a cikin watannan saboda Rashin Tsaro.

Bayanin hakan na Kunshe ne a cikin wata Takarda wadda Mai Dauke da sa hannun Babban Sakatare a Ma’aikatar Yada labarai ta jihar Zamfara, Barr Sani Nasarawa, Wanda yace ranar da aka zaba domin yin Zaben ba su gamsu da ita ba saboda shawarwarin Jami’an Tsaro

Barr Nasarawa Wanda ya rubuta takardar a bisa umurnin Kwamishinan labarai na jihar, Ibrahim Magaji Dosara, yace ba suda masaniya akan sauya ranar Zaben zuwa 12 ga watan Maris na wannan Shekara wadda yace suna kokarin bada Kariya ne lafiya da rayukan Yan Jaridar a saboda haka ba za su bari a Yi Zaben ba jar sai sun gamsu da sha’anin Tsaron domin kaucewa Matsala.

Takardar wadda aka Baiwa hukumomin Tsaro Kofin ta don suma su shaida, tace Ma’aikatar Yada labarai ce keda alhakin kula da shirya Zaben lamarin da yaci karo da kudin tsarin mulkin Kungiyar kamar yada wasu Yayan Kungiyar suka bayyana.

Har ila yau ma’aikatar ta bayyana damuwar ta akan rashin sanarda ita sauyin ranar gudanar da Zaben.

Sakatare. Kwamitin Shirya Zaben, Malam Dahiru Samaila Mafara ya shaida ma ‘Smarts News’ cewa, tuni suka bi umurnin uwar Kungiyar ta Kasa, “kasantuwar lamarin ya shafi Tsaro, ba bu wani zabi face a Dakatar da Zaben har sai Kuma mun samu wani Umurni”

Yanzu haka dai Mambobin Kungiyar ta NUJ na cigaba da furta albarkacin bakin su akan lamarin, inda wasu ke zargin Gomnatin Zamida yin Katsalandan ga sha’anin Kungiyar ta Yan Jarida, wasu na kallon lamarin a matsayin wani shishshigi da son kawo Cikas ga lamurran Aikin Yan Jarida a Zamfara.

Wani daga cikin Manyan Yan Jaridar Wanda ya nemi a sakaya Sunan shi, yace abun takaici ne irin yadda gomnatin Zamfara ke fakewa da sha’anin tsaro wajen biyan wasu bukatun ta. Yana Mai cewar Kila ma “shi Gwamnan Zamfara Bello Muhammad Matawalle baida masaniya akan lamarin, saboda Karamchin yayi yawa” inji shi.