SAQAR SO – QUEEN NISMERH


SAQAR SO

EPISODE 1 – At work
°°°°💗°°°°

Daga cikin bathtub na ji motsi, amma bazan iya ganin wanda ke ciki ba kasancewar akwai ruwa wane cotton daya lulleɓe guri gaba ɗaya, tsayawa nayi na ƙarewa toilet ɗin kallo, babba ne sosai girman ɗakin wata ne, komai tsaf yake, komai na toilet ɗin fari ne, hatta cottons ɗin dake liƙe a window fari ne, da wanda ya lulluɓe bathtub ɗin, nafi minti 40 a toilet ɗin amma wanda ke wanka be fito ba, ballantana nasan wanene a ciki, fitowa nayi daga toilet ɗin, na dawo ɗaki, masha Allah, a ɗakin ma komai fari ne, sannan akwai mudubi ko ina a ɗakin, dan wardrobe ɗin kanta duka madubi ce, sannan ga dressing mirror, komai na ɗakin a tsare yake, carpet ɗin ƙasa na kalla itama fara ce, idan ka kalle ta bazaka ce an taɓa taka ta ba.

Ina gurin ina kallon ikon Allah naji ƙarar buɗe toilet, da sauri na sauke ido na akan ƙafar wanda ke fitowa, wanda haka ya tabbatar min da macece, ƴan yatsun ta masu kyau ne sannan farace ita sosai, tun daga ƙafar ta nayo sama, hips ɗin ta sun fito sosai dan sun wuce ace musu coca cola shape, shape ɗin ya wuce misali, da alama zata ja hankalin mazan, dukiyar fulanin ta ma suna da girma amma ba sosai ba suma dai-dai, ba suyi yawa ba kuma ba suyi kaɗan ba, fuskar ta nake kallo, masu karatu wannan yarinya ta haɗu, sai dai mu ce tsarki ya tabbata ga ubangijin dukkan halitta, dan gaskiya gurin nan anyi halitta mai kyau, bakin ta bazaka ce mashi ƙarami ba, kuma ba zaka ce mishi babba ba, hancin ta dago ne sosai, idon ta dara-dara ne, ko yaushe a lumshe suke, amma idan ta gwale su zaka ƙara tabbatarwa ita ɗin mai kyau ce.

Gaban dressing mirror ta nufa, inda ta shiga shafa wancan ta shafa wancan, tashi tayi cikin tafiya ta ƙasaita tana motsa ko ina na jikin ta, wardrobe ta nufa , buɗe shi tayi ta ɗauko wata arniyar doguwar riga ta atampha wanda sai ka rantse ƴan kanti ne, dan ba zaka ce ɗinka su aka yi ba, saka wa tayi inda ɗinkin yayi matuƙar karɓar jikin ta, turare ta fesa kala-kala masu ɗaukar hankali, dan ƙamshin zai iya ruɗa mutane, fuskar ta ba wata kwalliya, sai kwallin da ta shafa kawai, murmushi tayi lokacin da ta ƙarewa kanta kallo gaban madubi, masu karatu fararen haƙoron ta suka bayyana masu ɗauke da haƙoran makka, sannan daga tsakan haƙoran akwai ƴar tazara kamar wushirya wadda ta ƙarawa haƙoran nata kyau, dimple ɗin ta na side chicks ya bayyana, gashin kanta ta naɗe wanda sai yanzu na lura dashi, dogo ne ga laushi da santsi, naɗe shi tayi sannan ta kawo ɗan kwali ta ɗaura, da alama gwana ce, dan ɗaurin yayi matuƙar yi mata kyau, gyale ta ɗauka medium size ta saka, sannan ta saka flat shoes kasancewar ita doguwa ce bata buƙatar high heels, jaka ta rataya, tafi minti uku tsaye gaban mirror tana murmushi, sannan ta ɗauki wani cin gum dake kan dressing table ɗin ta, ɗaya ta ɓalla ta saka a baki, ta fara taunawa a hankali, cin gum ɗin na strawberry, haka yasa duk numfashin da zata fitar ya zama na strawberry. Tafiya take yi cikin isa da ƙasaita, har ta sauko daga upstairs, dan tasan zuwa yanzu kowa yana parlor, wata matace zaune akan kujera, ta sanya wata doguwar riga ta atampha tayi matuƙar yin kyau, zuwa tayi ta rungume matar, “good morning Ummie na"ta faɗa tana mata peck a goshi, murmushi ya bayyana a fuskar wadda ta kira da Ummie, “Leesha kin tashi lafiya? "Ummie ta faɗa, “lafiya ƙalau Ummie na, ina Ishtar da Zaina suke? ", murmushi Ummie tayi tace “Ishtar da Zaina suna ɗaki, wai sun gaji da jiran ki shine suka wuce ɗaki ", murmushi Leesha tayi tace “Ummie ki cewa Ishtar waya damu dan bata jira shi ba, ita kuma autar ki ki faɗa mata yau bata da chocolate "ta faɗa tana tafiya da alama fita zata yi, “Leesha ina zaki baki ci abinci ba" Ummie ta faɗa, “Ummie bana jin yunwa, zan nemi abun motsa baki a hanya "ta faɗa tana wucewa, Ummie ta girgiza kai tace “har yanzu kina nan yadda kike da rashin son abinci".

A harabar gida kuwa, faɗa na sami tana yi “kai wani irin sakarai ne, tun yaushe na faɗa mata bada wannan zan fita ba, yau da farar mota zan fita “, “yi haƙuri Hajiya Leesha, itama farar an wanke ta ai” mutumin dake wanke mata mota ya faɗa, “to shikenan kira min Adamu “ta faɗa, da sauri Adamu ya taso, “gimbiyar mata Allah ya ƙara miki daraja” ya faɗa, “ya isa haka, ga mukullin mota muje “ta miƙa masa mukullin mota da alama drivern ta ne.

A gaban wata ma’aikata suka tsaya, ɗaga kaina sama nayi naga an rubuta ABEER GLOBAL COMPANY INTERPRICES, haɗe fuska tayi ta fito daga cikin mota, tafiya take yi kamar bata son taka ƙasa, amma haka bai hana gangar jikin ta motsawa ba, mutanen ma’aikatar sai kwasar gaisuwa suke yi, tafiya take yi har ta shiga ciki, wow masu karatu wajen bakomai bane idan aka haɗa da cikin, ko ina Ac ne, ga cc TV ta ko ina, cikin wani office ta shiga, babba ne gurin sosai, zama tayi kan kujera tare da aje jakar ta, files ta ɗauka ta fara signing, tana dubawa, knocking ƙofar aka fara yi, ɗago kanta tayi dake ƙasa tana kallon ƙofar, buɗewa aka yi, wata mata ta shigo sanye da gajeren skirt wanda ake kira da mini skirt, rigar ta fara ce, skirt ɗin kuma baƙi ne, kallon yarinyar tayi tace “Anita what’s ur problem? “(Anita minene matsalar ki?), “u have a visitor” (kina da baƙo) Anita ta faɗa, Leesha tace “tell him that am busy right now, let’s meet tomorrow by 1:30″(ki faɗa mishi ina aiki yanzu, mu haɗu gobe da misalin ƙarfe 1:30), “ohk ma “Anita ta faɗa tare da fita daga office ɗin.

Anita tana fita ta sami mutumin tsaye yana jiran ta, matsowa yayi, da saurin shi ya ɗauka yau an dace, dan zuwan shi office ɗin nan yafi sau biyar amma be haɗu da Leesha ba, kullum sai ace mishi tana aiki, “u are ask to come back tomorrow by 1:30″(an umarce ka da ka dawo gobe da misalin ƙarfe 1:30)Anita ta faɗa tana juyawa zuwa gurin da aka aje ta, shi kuwa ranshi a ɓace ya juga, wani mutumi ya ce “Omar Faruk ka samu ganin hajiyar “, cikin takaice da haɗiye takaice yace “a’a baba, wai ita wannan yarinyar dama haka take da wulaƙanta mutane?”, mutumin da ya kira da baba yace “a’a Omar, Leesha ta kasance mai mutunci, amma tabbas kam, tsawon shekarun da na ɗauka nan, na fahimci halin ta ɗaya da mahaifin ta Alhaji Abeer, mutum ne da baya so talaka ya raɓe sa, amma kuma suna da kyauta, da mutunci, zasu maka kyautar da har abada zaka daɗe kana jin daɗi, amma zasu maka wulaƙancin ds har ka mutu bazaka manta ba”baba mai gadi ya faɗa, Omar yace “to miye amfanin kyautar, bayan ba su daraja mutum ba “, baba mai gadi yace “su ko mai kuɗi idan suka ga dama wulaƙanta shi suke”, Omar yace “ni bansan inda zan samu taimako ba, dole na haƙura na dawo, ƙanwata Farrah tana buƙatar taimako, amma ni na tsane mutane masu irin halin ta, har abada bazan so ta ba “, dariya baba mai gadi yayi yace “yau naga mutum mai ƙarfin hali, to kai wayace maka Leesha zata so ka, kai dai kawai kayi biyayya ka samu abunda kake so a wuce gurin dan mai so shike nema”, gaɗa kai Omar yayi yace “to shikenan baba ni zan wuce sai gobe, in Allah ya yadda “.


EPISODE 2-HATRED
°°°°°°°°💗°°°°°°°°°

Bata bar Abeer global company interprices ba sai around 6:30, inda ta fito cikin takun ta na ƙasaita, Adamu direba ne ya buɗe mata mota ta shiga, a gaban babbab gate ɗin fita daga ma’aikatar suka tsaya , kuɗi ta ƙirgo ƴan dari-dari har guda ashirin ta miƙa ma Baba me gadi, da godiya ya karɓa “na gode Hajiya kinyi gadon kyauta, jinjina gare ki ƴar gidan Alhaji Abeer, shalelen Hajiya Aisha, Allah ya ƙara miki nasa da ɗaukaka ” da wannan kirarin suka wuce, rufe idonta tayi kamar me barci, a hankali ta buɗe bakin ta, tace “Adamu ka tsaya dani Abeer shopping mall, zan siyawa Zaina chocolate”, “an gama Hajiya “Adamu ya faɗa, yau yana so yayi surutu, amma yaga Leesha yau ƴan miskilancin ne a kanta.

ABEER SHOPPING MALL, naga an rubuta da manyan haruffa, lokacin da suka yi parking gaban wani haɗaɗɗen shago, fitowa tayi cikin taku na ƙasaita, cikin shagon ta shiga, inda ta shiga ɗaukar chocolate kala-kala, murmushi tayi lokacin da idon ta ya sauka kan wata teddy bear mai girma, hannun ta, ta kai kan teddy bear ɗin ta ɗauka, sannan ta cigaba da tura basket ɗin da ke hannun ta, sai da ta cika shi da different kind of chocolates da kuma biscuits , sannan ta nufi gurin da ake biyan kuɗin, kuɗin aka faɗa mata sannan ta biya, Adamu direba ne ya sanya su a cikin mota, sannan suka wuce.


A harabar gida ta samu Zaina tana wasa, “Adamu zan turo Angela ta shigo da kayan ciki, saura kace ban faɗa maka ba” wucewa tayi ba tare da ta jira me zai faɗa ba, da gudu Zaina ta ƙarso gabanta ta rungume ta, murmushi Leesha tayi sannan tace “ni fushi nake da ke”, Zaina tace “Aunty Leesha ba laifi na bane, yaya Ishtar ce tace mu tafi ɗaki “, Leesha tace “is ok nasan little sis ɗita ba za ta ƙi jira na ba sai da dalili”, cikin gida suka shiga a tare, Angela ce ta fito daga kitchen, durƙusawa tayi tace “you are welcome madam”, Leesha tace “Thank you Angela, ki je waje ki kwaso min kaya a mota “, wucewa tayi ɗaki, inda Zaina ta koma waje gurin wasa.


~~~~~~~~~~~~~~~~~
A ɓangaren Omar kuwa tun da ya koma gida ya sami Farrah a yanayin da ya barta sai ya ƙara jin ya tsani Leesha, miyasa masu kuɗi suke haka ne, “yaya Omar” wata kyakkyabar yarinyar ta faɗa wadda a ƙalla shekarun ta za su yi 20 a duniya, “Niesha me ya faru ” ya faɗa yana juyowa, murmushi ta sakar mishi, tace “Baba na kiran ka”, “ohk kice mishi ina zuwa “, fita tayi, Niesha bata yi minti shida da fita ba, Omar ya biyo bayanta, “Baba sannu da zuwa” Omar ya faɗa, tsohon da ke zaune kan tabarma yace “yauwa Omar, dafatan dai an dace “, murmushin da yafi kuka ciwo yayi yace “Baba tace na dawo gobe”, murmushi Baba yayi yace “kar ka damu, insha Allah za’a dace, kuma Farrah zata tashi a kan ƙafafun ta insha Allah “, “insha Allah” Omar ya faɗa.


©©©©©©©©©©©©©©©©©©©©©©©©
Washe gari da safe, ɗakin Leesha na shiga, amma da mamakina sai naga wannan ɗakin komai blue ne, amma kayan ɗakin iri ɗaya ne, kallon ko ina nake yi, mamaki ya cika ni, sai yanzu naga ashe mantawa nayi na shiga ɗakin da ba shi bane, ina tsaye na ji an fito daga toilet, juyowar da nayi sai naga Leesha, da kallo nake bin ta, ita ko ina zuwa ta ke? , ko kuwa dai ɗaki biyu gare ta, shiryawa tayi cikin wata doguwar riga light blue ta ƴan kanti, wani guntun hijab naga ta sanya black colour , jaka ta rataya baƙa, sannan ta sanya takalmi flat shoes baƙi, tafiya take yi ko ina na jikin ta na motsawa, parlor ta nufa, inda ba wanda ya fito, kasancewar ƙarfe 7:00 na safe, waje ta nufa inda ta kira malam Idris tace mishi fita zata yi, kai tsaye gaban babbar wata ma’aikata suka nufa, da sauri ta fito saboda tayi latti, ciki ta shiga, inda mutane gurin suka shiga nuna ta ga Leesha nan ƴar lelen Alhaji Abeer, kai babban gurin da ake labarai ta shiga, zamanta kenan, baƙon da suka gayyata ya shigo, nan ta fara mishi tambayoyi, awa ɗaya suka yi suna labarai, sannan suka yiwa masu sauraro sallama, yanzu na fahimta ita journalist ce, to ya take haɗa aiki biyu lokaci ɗaya, cikin sauri ta fito, sallama tayi wa mutanen gurin, sannan ta umarci Idris akan ya maida ta gida, dan yau tana so ta tsaya tare da Ummie gida, kwanannan bata samun lokacin ƴan uwanta.

NI KUWA NACE TO SHI OMAR FAROUQ YA ZA KIYI DA SHI? 🤔

Gida ta dawo, inda ta samu Ummie zaune a parlor, rungume ta tayi ta baya tare da rufe mata ido, hannun ta Ummie ta, taɓa tace “Leena har kin dawo”, “laaa Ummie ya aka yi kika gane ni “, Ummie tace “ke ki ji min ja’ira ya zan haife ki, kuma na gagara gane ki” Leesha da ke saukowa daga kan matakala na kalla, sai yanzu na ga asalin kamar da su ke yi ita da Leena kl, masu karatu kar ku ga laifi na dan ni kai na sai yanzu na fahimci wacce nake bi tun ɗazu ba Leesha bace, to wacece wannan Leena ɗin, gaskiya suna kama, har ƙamshin turaren su, da muryar su iri ɗaya ce, murmushi Leena tayi lokacin da taga Leesha, “Ummie ga rabin jiki nan ta tashi “, Ummie tace “Leesha sarkin barci”, da kallo Leesha ta bi su tace “me kuke tattauna “, Leena tace “gulmar ki nake yi”, “Ummie kin gan ta ko ” Leesha ta faɗa , Leena tace “Ummie bata ga komai ba”, Ummie tace “ai Leena bata laifi “, Ishtar ce ta shigo parlorn tace “Ummie ke kike shiga zancen tweens ku, kina nan za su baki kunya”, dariya suka sa su duka, “Ummie ina kwana “Leesha ta faɗa tana duba agogon ta, “lafiya ƙalau, ki zo kiyi breakfast”, “Ummie nayi latti fa”, Leena tace “muje nayi feeding ɗin ki a baki, za muyi sauri kin ji”, bata yi niyyar cin abinci ba amma saboda Leena tana so ba yadda ta iya, bazata iya jurar fushin Leena ba, sai yanzu na lura da kaya iri ɗaya suka saka, kuma komai nasu iri ɗaya, amma abunda ya bambanta su shine Leena tafi Leesha sakin fuska, amma kamar su ɗaya.

Abincin Leena ta zuba mata a plate tana bata a baki, har ta ƙoshi, sannan ta goge mata baki, gwanin sha’awa kamar su haɗe junan su suke ji dan so, ni kaina sai na ji ina ma yarana ne, daga nesa na hango Ummie tana murmushi, tana jin daɗin yadda Leesha da Leena ke son junan su, tun suna yara, kaya ma iri ɗaya suke sawa, dan duk ranar Sunday suke fitar da kayan da zasu saka na satin gaba ɗaya, kuma har zuwa yanzu da suka girma basu canza ba, dama tun can basa son kwana ɗaki ɗaya saboda a cewar Leesha idan suna kwana tare ɗaya bazata yadda ɗaya tayi aure ba, saboda yadda suke son junan su.

Bayan ta gama cin abinci ne ta fita zuwa gurin aiki inda Leena ta mata rakiya har mota suna labari, Adamu direba ne ya fito, Allah ya raya tagwayen Alhaji, murmushi suka yi, Leena tace “kasan Leesha bata son surutu, kaja motar ku tafi, ta makara”, murmushi Leesha tayi tace “take care my other half “murmushi Leena ta yi tace “insha Allah, and you to plss”, badan sun so ba suka rabu da juna.

Ƙarfe 11:30 dai-dai ta shiga ma’aikatar, inda ta fara aiki, yau bata samu zama sosai ba, kiran sallar Azahar yasa ta fito daga office inda ta nufi wani ɗaki, da yaji komai, toilet ta shiga tayi arwala sannan tayi sallah, bayan ta gama ne ta fita, cikin sauri take tafiya, Anita ce tazo ta same ta tace “ma someone is waiting for u at ur door “(wani yana jiran ki a ƙofar ki”, “tell him that i don’t have his time”(ki faɗa mishi bani da lokacin shi), wucewa Anita tayi da sauri ta isa bakin ƙofar ta faɗa ma wani tsoho dake tsaye gaban office ɗin Leesha, shi kuwa tsohon gani yake Anita ƙarya take mishi, dan haka ya ƙi ya motsa, can sai ga Leesha ta ƙaraso gurin, kallon tsohon tayi tace “me kake yi anan? “, “ke nake jira” tsohon ya faɗa, “ban faɗa maka bani da lokaci ba “Leesha ta faɗa a tsawace, “kiyi haƙuri amma taimakon gaggawa ne” ya faɗa, kuɗi ta ƙirgo ƴan dubu-dubu har naira dubu hamsin ta watsa mishi “ka tashi ka bar min ƙofar office ɗina kaji me na faɗa “ta faɗa, dai-dai lokacin Omar ya ƙaraso, kallon tsohon da ke gurin yayi, sai yaji duk tausayi ya kama shi, nan take yaji ya tsani Leesha, buɗe baki yayi ranshi a ɓace yace “Leesha…………..

—————————————————-

EPISODE 3:LOVE AT FIRST SIGHT
°°°°°°°°°°°°°°💗💗°°°°°°°°°°°°°°
“Leesha! “Omar ya faɗa da ƙarfi, cikin taku da isa ta juyo dan ganin, wanene wannan mai mata kiran mafarauta, karaf suka haɗa ido da shi lokacin da ta juyo, idon ta a tsai-tsaye suke, sannan kai tsaye take kallon shi, jin yadda zuciyar ta ke bugawa har tana mata barazanar faɗowa ya za me mata sabon yanayi, takowa yake yi, ba alamar tsoro ko girgiza a tare da shi, cikin jajircewa da dakiya, amma kafin ya ƙaraso ta juya zata tafi, Anita ce ta tare ta da magana “ma he’s the visitor that came here to meet u yesterday, and u ask him to come back today by 1:30″(ranki ya daɗe shine baƙon da ya zo jiya nan, kika ce ya dawo yau), Leesha tace “i don’t have his time as usual “(bani da lokacin shi, kamar ko yaushe dai), cikin jin haushi Omar ya yo kanta, dan tun da suka fara magana yana ji, “ke wace irin mutum ce, wacce bata san darajar ɗan adam ba?”, bata juyo ba kuma bata amsa shi ba, sai hannu ta saka cikin jakar ta, ta ɗauko bandir ɗin dubu-dubu har bandir biyu, wanda ya kama dubu ɗari, miƙa wa Anita kuɗin tayi sannan ta mata nuni da Omar, buɗe office ɗin tayi tare da rufe shi, ta ɗaura hannun ta akan ƙirjinta zuciyarta na matuƙar bugawa, fuskar Omar kawai take gani, wani yanayi take ji da bata taɓa ji ba, murmushi tayi a hankali ta furta “ i love his boldness “, guri ta zauna tana aiki.

A ɓangaren Omar, Anita ce ta nufo shi da kuɗi, miƙa mishi tayi, cikin takaici ya karɓa, tare ƙudurtawa a ranshi har abada bazai sake dawowa nan ba, yanzun ma ya karɓi kuɗin ne saboda lafiyar Farrah, autar gidan su kenan, Leesha kuwa aikin ma gagarar ta yayi, haka yasa ta haɗa kayan ta, da takaddun ta, ta nufi mota, Adamu ya ja mota, har su ka isa bata ce komai ba, idon ta a rufe yake tana tunanin Omar, tafiyar shi da yadda ya ke da taurin rai sune suka fi burge ta, gida suka nufa, a mota Adamu sai zuba surutu yake yi, wani bin ta amsa shi, wani bin tayi murmushi, wani gurin kuma ta gwashale shi, a haka har suka isa.


A parlor ta sami Leena zaune tana kallon Game of love, a tashar star life, faɗawa tayi cikinta, “kin dawo yanzu zaki sauke min gajiya a jiki” Leena ta faɗa tana shafa kan Leesha, murmushi Leesha tayi tare da lumshe idonta, tare suka yi kallon, Leesha kuwa tana ta imagining wannan rayuwar ita da Omar ce, Leena ta lura da yanayin Leesha, kuma ita kaɗai ce zata iya faɗan yanayin da Leesha take, kamar yadda Leesha zata iya faɗar nata, bayan su ba mai fahimtar su, ko Ummie da ta haife su tana wahala a fannin nan, kuma ƴan gidan su kawai zasu iya bambance kamannin su, dan kowacce a cikin su zata iya pretending a matsayi ɗaya, wanda in ba sun faɗa ba ba wanda zai yadda, “Leesha ” Leena ta faɗa, juyo Leesha tayi tace “Leena”, murmushi suka sakarwa juna a tare, sannan Leena tace “kin faɗa soyayya ne “, ko kaɗan Leesha bata yi mamaki ba dan ta san tabbas Leena zata gane, “ eh Leena, na fara son wanda nake ganin tsanata a idonshi, na fara son wanda baya so na, ya zan yi?”, murmushi Leena tayi tace “shine ya faɗa miki baya sonki? “, girgiza kai Leesha tayi alamun a’a, “to kisani shi ɗin nan zai so ki duk abunshi “, Leesha tayi murmushi tace “” ni ban damu ba, abunda kawai na sani ina son shi “, Leena tace “ni kuma abunda nake so shine ya so ki kamar yadda kike son shi “, Leesha tace “Allah yasa”, Leena tace “Ameen, yauwa Leesha kin ji wani abu, yau fa bayan na rakaki, a tv naga labarai wai Yusouf ya ɗaga company ɗin mahaifinshi, shine zai riƙa juya AYAZ COMPANY “, “wanene Yusouf?” Leesha ta tambaya, Leena tace “shine ɗan Alhaji Abdallah, ai kinsan mai company ɗin AYAZ, wanda suka taɓa samun saɓani da Pappy “, “ohhh an yi haka” Leesha ta faɗa cikin fahimtar zancen, Leena tace “amma kinsan Alhaji Abdallah ya gaza ɗaukaka Company ɗin sa, shi a dolen sa, so yake yafi Pappy arziki “, “kuma shi gani yake yanzu da ya ba ɗan shi aikin zai iya? ” Leesha ta tambaya, Leena tace “eh Yusouf ɗin ai jajirtacce ne a cewar mahaifin na sa, kuma wai ɗan na shi ya dawo daga Egypt ne karatu “, Leesha tayi dariya tace “to minene a cikin karatu Egypt? “, Leena tace “a gurin su abun alfahari ne” dariya suka sa su duka, nan suka canza fira, bayan sun gama fira ne kowa ta wuce ɗakin ta dan yin wanka, kasancewar yau Pappy zai dawo, wato Alhaji Abeer, ya ɗauki tsawon wata uku a India, wanka suka yi, wando da riga Leesha ta saka, tare da sakin gashin ta ya baje, ni kuwa ɗakin momy na wuce inda na same ta sanye da riga da zane na alfarma, ɗinkin na ta ya sha stone work, tayi matuƙar yin kyau, gashin ta dogo ta warware kasancewar Ummie buzawa yasa gashin ta ke da tsayi sosai, kuma yaran ta ma ita suka biyo, farincikin da ke fuskar ta baya ɓoyuwa kasancewar yau Pappy zai dawo, ƙofar ɗakin ta naga an turo, Leena da Leesha ne suka shigo a tare, na gagara bambance wacece Leesha, wacece Leena a cikin su, rungume Ummie suka yi ta baya, a tare suna kallon mirror, “you look so beautiful my babies “Ummie ta faɗa, “and you also look more beautiful than us” suka faɗa a tare, “Leesha miƙo min sarƙata a kan gado “Ummie ta faɗa, juyawa tayi zata ɗauko, Ummie tace “Leena bana son ja’iran ci, tunda naga kin shigo kina haɗe fuska nasan so kike ki rikita ni, ita kuma Leesha sai wani sakin fuska take dan ace kece, to ni bazaku hauka tani ba, sai dai ku shashantar da wanda be san ku ba” Ummie ta faɗa, dariya Leena tayi tace “kai Ummie akwai rigima wallahi “,“ba dole nayi rigima yara sai rainin hankali, wai ita harda wani barbaje gashi yadda kike yi a gida, ke kuma kika wani naɗe gashi yadda ta ke yi, to ni bazaku raina min wayo ba, bari Pappyn na ku ya dawo a kai ku gurin sheda a yanka goshin ɗaya”, dariya Leesha ta sa, tace“yo ana yanka goshin Leena nima zan yanka nawa “, haka suka dinga yi, suna wasa da dariya, farinciki fal ransu, Ummie tana ji da yaranta sosai, dai-dai gwargwado suna mata biyayya.

Da misalin ƙarfe biyar da rabi na yamma Pappy ya danno kanshi cikin gida, cike da farinciki da zamuɗin ganin ahalinshi, yayi matuƙa yin kewar su, a harabar gidan ya hango su, Leesha da Leena sun saka Ummie a tsakiya, Ishtar a gefen Leena, ita kuma Zaina a gefen Leesha, wayar shi ya ciro tun daga nesa ya fara ɗaukar su hoto, sannan ya ɗan matso, buɗe musu hannu yayi, da gudu su ka ƙaraso gaban shi suka rungume shi “ you are welcome Pappy “su ka faɗa a tare, murmushi yayi yace “thank you all”, Ummie ce ta ƙaraso ta rungume shi tace “ you are welcome Pappyn tweens “, murmushi yayi, yace “thank you Ummien tweens”, Leesha ta kama hannun shi tace “Pappy ka jima a can saura kaɗan na bika “, chicks ɗin ta ya ja yace “ tuffan ido na nayi matuƙar masifar yin kewar ki “ya faɗa har da yarfa hannu, dariya Zaina tayi tace “Pappy ya dowo yanzu zamu riƙa wasan ɓuya ni da shi”, dariya yayi yana ɗaga ta sama yace “my princess zamu yi wannan gobe ko “, gaɗa kai tayi alamar eh, Leena tace “Pappy ya dawo kowa zai fara damun shi muje na zuba maka abinci”, Leesha tace “ni ce zan bashi a baki sai dai ke ki zuba “, Ishtar tace “wayyo Ummie, kin haifi ƴan katsalanda, su barki ki samu lada amma ba za suyi ba, Pappy ni dai ka goya ni zuwa ciki”, Zaina tace “ni za’a goya fa”, Ummie tace “kun samin miji a gaba, ki bar shi ya yi wanka in yaso ku yi duk abunda za kuyi “, murmushi yayi yace “matata tasan abun da nake son yi”, “ laaaaa pappy “, suka faɗa a tare, tare suka shiga cikin gida, wanka ya fara yi, sannan Leena ta zuba mishi abinci, Leesha tayi feeding ɗin shi kamar yadda suka tsara, parlor ya dawo yana kallo, Leesha na mishi tausa a ƙafa, dan dama in dai yana gida zaka ga Leesha a gefen shi.
————————-


EPISODE 5 – CURE
°°°°°°°💗°°°°°°°°

Babbar asibitin da ke cikin garin Barno ta nufa da ita, Naesha kuwa sai kallon ikon Allah take yi, motar ta haɗu iya haɗuwa, ga wani ƙamshin daɗi dake bugun hancinta, Omar kuwa yana baya tare da Farrah, addu’a kawai yake kar a ce Farrah ta mutu, gate ɗin aka buɗe, ƙasa tayi da glass ɗin motar, wani jami’in tsaro ne ya miƙa mata wani kati, karɓa tayi sannan ta wuce, ganin wacce ta fito a motar tasa nurses suka yi gaggawar zuwa, da sauri suka zo, ɗaukar Farrah suka yi aka ɗaura akan gado, tura gadon suke yi da gudu, direct emergency room suka nufa da ita, nan take aka canza mata kaya, ɗakin da ake yin tiyata aka shiga da ita, office ɗin babban likitan Leesha ta nufa, jikinshi na rawa ya tashi, “ina wuni Hajiya “ya faɗa, “lafiya” ta amsa a taƙaice, “ya zan taimaka miki? ” likitan ya faɗa, Leesha tace “ na kawo patient, tana ɗakin tiyata, ina so a duba min ita”, likitan yace “subahanallah, mu je”, tare suka fita da likitan, da sauri yake tafiya, dan yasan halin Leesha yanzu zata fara mishi masifa, ita kuwa tafiya take yi cikin isa, shiga likitan yayi inda ake tiyata, ko da ya shiga an fara tiyatar, dan haka kayan jikin shi ya sauya zuwa kayan aiki, sannan ya sa face mask da safar hannu, ya kama aikin.

A ɓangaren Leesha kuwa ɗaki-ɗaki take shiga tana duba marasa lafiya, tare da yi musu kyauta, wani ɗaki ta shiga inda ta samu matar kwance tayi nisa da rashin lafiya, gashi ɗakin duk wari yake yi, a gurin take amai, tayi fitsari, da kashi duk a kwance, kuma basu da kuɗin siyen magani, hannunta ta sa ta rufe hancin ta, tare da cewa“minene matsalar ku da bazaku iya gyara mata jikin ta “, wata yarinya dake jinyarta tace “taɓ, ai bazan iya ba, ni fa ko zama ɗakin bana yi”, Leesha da mamaki ya gama cikawa tace“amma dai ba ita ta haife ki ba ko “, yarinyar tace “bangane ba mamata bace, to ni wazan zauna dashi a wannan yanayin in ba mamata ba, amma wallahi ban iya bauta”, Leesha da ranta yayi matuƙar ɓaci tace “amma ke sakaryace, baki san darajar mahaifiya ba “, juyawa tayi ta fita, wasu nurses ta kira, suna shigowa ɗakin da matar take, Leesha ta hau su da faɗa, “ku minene amfanin ku, baku aikin ku yadda ya kamata, idan baku ba mutane kulawa ya za’a yi su dawo gobe, baku da tunani ne ko kuma kawai wulaƙanci ne” ta faɗa, ɗaya daga cikin nurse ɗin tace“ ranki ya daɗe kiyi haƙuri, wallahi tun da suka zo asibitin nan basu bada kuɗi ba “, buɗe jakar ta Leesha tayi, dubu ɗari biyu ta watsa musu, sannan tace “ku tabbata nan da kwana uku matar nan ta warke, kuma ku gayawa doctor na biya kuɗi, idan basu isa ba a kira ni zan ƙara wasu” , dubu goma taba matar da bata da lafiya, sannan ta fito daga ɗakin, kai tsaye inda aka kai Farrah ta nufa, dai-dai lokacin Omar ya ƙaraso, zuciyarta ce ta shiga buguwa kamar zata fashe, amma sai ta basar, dan Leesha yarinya ce da indai ba ita ta nuna maka yanayin da take ciki ba, ko kaine sarkin masu fahimtar yanayi bazaka gane ba, Leena kawai ke fahimtar Leesha a wannan yanayin.


Omar kuwa sai cika yake yana batsewa, shi a dolen shi ya tsani Leesha, ita bata ma san yana yi ba, kallon wanni transparent glass window take yi, wanda zaka iya ganin duk abunda mutanen ciki ke yi, gani tayi har an gama ɗinki a cikin Farrah, haka ya tabbatar mata da angama aikin, idonta ta ɗaga sama domin tabbatar da ko numfashin Farrah na tafiya dai-dai ko a’a, murmushi tayi tare dan jan numfashi, aiki yayi kyau, domin numfashin ta ya dai-daita , matsawa tayi daga gurin ganin likita na shirin fitowa, fitowa likitan yayi, yana cire rigar da ke saman kayan aikin, murmushi yayi yace “Hajiya anyi nasarar aiki, zata farka nan da awa biyu “, kallon agogon tayi ganin yanzu har ƙarfe ɗaya tayi, tace “nagode likita mu je na biya ka”, wucewa tayi tare da likitan, bata ko kalli gefen da su Omar su ke ba, dan ita ba dan Omar tayi ba, tayi ne saboda rayuwar yarinyar na cikin hatsari, Leesha bata yadda a rasa rayuwa ba, matuƙar akwai mafita, duk da halinta na wulaƙanci bata wulaƙanta mara lafiya musamman wanda rayuwar shi ke gazgara da mutuwa, Leesha zata iya bada duk arzikin da ta mallaka dan kawai wani ya samu sauƙi, office suka shiga nan ta mishi transfer dubu ɗari shida a account ɗin su na asibiti, sannan ta bashi duhu ɗari hudu cash a hannu, tace“ ku riƙa aiki da kyau, sannan na shiga wani ɗaki room 108, bata da lafiya sosai ka tabbata ta warke, na baka dubu ɗari huɗu ne saboda ita, kuma naba nurse dubu ɗari biyu, ku kula da ita yadda ya dace, idan ba haka ba sai kun biya ni kuɗi na”, haƙora likitan ya shiga washewa saboda yasan kuɗin har sun wuce na duba mara lafiyar, ko kuɗin tiyata dubu ɗari ne amma gashi dubu ɗari shida ta bada, dan haka riƙe dubu ɗari huɗun zai yi, “insha Allah, baza mu kai ga haka ba ma, zata samu sauƙi “, Leesha tace “insha Allah”, tashi tayi ta fita, kai tsaye waje ta nufa, wata nurse ta gani, “ki biyo ni mota” Leesha ta faɗa, farinciki fal ran nurse ɗin nan dan tasan kakarta ta yanke saƙa, buɗe motar Leesha tayi tare da buɗe wani akwati dake gefen kujerar ta, dubu hamsin ta miƙa mata, “nagode sosai ranki ya daɗe, Allah ya ƙara buɗi “, “Ameen, sannan ga wannan ki kai wa Omar, saurayin da muka zo tare da shi, zan tambaye shi idan kin bashi” ta faɗa tana miƙa mata bandir ɗin ƴan dubu-dubu har guda shiga wanda suka kama dubu ɗari uku, “insha Allah zan kai mishi “, Leesha tasan zata kai shiyasa ta bata, juyawa nurse ɗin tayi zuwa ciki, Leesha kuwa jan motarta tayi , me gadin asibiti ta miƙawa katin da ya bata ɗazu, sannan ta basu dubu ɗari su raba su huɗu, murna fal ransu, kirari suka dinga mata da addu’o’i har ta ɓace musu da gani.

Ɓangaren Omar kuwa yana tsaye yana jiran Leesha ta dawo ya mata godiya, sai ga wata nurse ta zo, “gashi inji Hajiya Leesha, tace a baka “, kallon hannun matar yayi, bandir ɗin kuɗi ya gani har guda shida, gashi duku ƴan dubu-dubu ne, da kamar bazai karɓa ba, sai kuma ya canza ra’ayi ya karɓa, “tana ina?” ya tambaya, “ta wuce gida “ta faɗa tana wucewa, Naesha ce ta matso tace “kai yaya amma dai wannan mata akwai mutunci, ina ma ta zama ƙawata”,“ hmmmm” kawai ya iya cewa, dan shi ya tsani Leesha, Naesha tace “ni dama bari tayi muka mata godiya sannan “, Omar yace “ai sai kije ki mata”, Naesha tace “to yaya ina zan ganta, ai wannan tafi ƙarfi na”, “kije Abeer global company interprices, zaki ganta “ya faɗa yana tashi, “laaaaa ita ce wadda kaje neman taimako gurin ta” Naesha ta tambaya, Omar yace “eh”, Naesha tace “amma ji yadda take yi kamar bata san ka ba”, “ke ni dan Allah karki dame ni da surutu kina jina ko “ya faɗa cikin nuna gajiya da surutunta, nurse ɗin da aka sa ta tsare Farrah ce ta fito,“ina ƴan uwan mara lafiyar nan?” nurse ɗin ta tambaya, “gamu”, Naesha ta faɗa, Nurse ɗin tace “ ta farka “, da sauri suka shiga ɗaki, murmushi Farrah tayi, yarinyar kyakkyawa ce, duk da bata lafiya amma kyanta ya bayyana sosai, murmushi tayi tace “yaya Omar kai ne”, “eh ni ne Farrah, ya jiki “, washe haƙora tayi tace “ na warke”, kallon Naesha tayi tace “ kina fushi dani? “, girgiza kai Naesha tayi alamar a’a, tace “bazan iya fushi dake ba, ya jikinki?”, tunawa tayi ranar da Farrah ta kwanta rashin lafiya, sun gama faɗa ne da ita, sai tayi barci, shine ta tashi da ciwon ciki, dama Farrah na da appendix, Farrah tace “da na mutu, haka za’a ce mun yi faɗa kenan na kwanta rashin lafiya”, dariya Naesha tayi tace “ki bar wannan zancen, yanzu kin tashi ai “, murmushi su ka yi a tare, Omar kuwa yana zaune be ce komai ba.

°°°°°°°°°°°°°°°
Ɓangaren Leesha kuwa gida ta nufa, a hanyarta ta tafiya gida, ta tarar da taron mutane a kan titi, tsayawa tayi dan tambayar me ya faru, fitowa tayi daga motar, inda wata mata tayi saurin faɗa mata a jiki, hannunta tasa ta ture ta, tare da gyara zaman jakar ta, “miye haka zaki faɗa min a jiki? “Leesha ta tambaya cikin faɗa, dan duniya ta tsani a ɓata mata jiki, gashi matar duk ta shafa mata datti, wani mutum ne yace “kiyi haƙuri, mahaukaciya ce, tun ɗazu ta tara mana mutane a nan”, girgiza kai Leesha tayi, matar da aka kira da mahaukaciya, maƙare mutumin da ya kira ta da mahaukaciya tayi, da ƙyar aka kwace shi sumamme, rugawa tayi da gudu ta wuce, Leesha kuwa duk mamaki ya cika ta, mota ta shiga ta wuce zuwa gida.


~~~~~~~💞💞~~~~~~~
EPISODE 6 – NIGHTMARE
°°°°°°°°💗°°°°°°°°°
Ta isarta gida, kai tsaye ɗaki ta nufa, dan ko da ta dawo babu kowa a parlor, ɗakinta ta wuce, kayan jikinta ta rage, sannan ta ɗaura towel dan duk jikinta ciwo ya ke, toilet ta shiga, rufe bathtub ɗinta tayi kamar yadda ta saba ko yaushe, ta ɗauki awa ɗaya a toilet kafin ta gama wanka, tana fitowa ta zauna gaban dressing mirror, Nivea ta shafa, dan Leesha ba ta da wani mai da ya wuce Nivea, kasancewar man yana da kyau kuma yana gyaran fata, baya sa bleaching amma zai taimaka maka gurin maintaining skin ɗinka, ba ta shafa komai a fuskarta ba domin marece yayi, ba jimawa za’a yi magrib, riga ta saka silver, tayi matuƙar yin kyau cikin rigar, rigar kamar ta barci ce, sai ƙyalli ta ke, rigar ba ta kama jikin ta ba amma tayi mata kyau sosai, r har ƙasa ta ke, sannan kuma gaban rigar kamar aiki ne a jikinta, da ganin rigar kasan tsadaddiyar riga ce, kiran sallar da ta ji ne ya sa ta ɗaukar sallaya ta shimfiɗa sannan ta ɗauki hijab ta saka, ƙur’ani ta ɗauka, sannan ta zauna akan sallayar, karatu ta fara yi cikin natsuwa, muryarta na da sauti da daɗin sauraro, domin kuwa ana so makarancin  al-ƙur’ani a lokacin da ya ke karatun muryar shi ta zama mai sauti da daɗin sauraro, tana zaune a gurin har aka kira sallah, tashi tayi ta kabbarta sallah, dan dama ita ƙa’idar ta ce duk ta shiga toilet sai ta canza arwala, sallah tayi cikin jam’i domin tana iya jiyo ƙarar me sallah kasancewar masallacin na gidan su ne, (a ruwayar wasu malamai sun ce, idan dai zaka iya jiyo sautin mai sallah kuma masallacin a gaban gidanku yake ba bayan gidan ba to zaka iya bin jam’in sallah), bayan ta sallame sallar ne ta cigaba da yin karatun ta, da sauran addu’o’in, tana zaune a gurin har aka kira sallar isha’i, tana gama sallah ta ji wani irin barci ya saukar mata abunda ba ta saba yi ba, tashi ta yi ta cire rigar jikinta ta sauya zuwa kayan barci, kwanciya tayi, ko minti uku bata yi ba barci ya kwashe ta.

Leena ce ta fito daga ɗaki, parlor ta sauko inda dama duk ranar asabar da lahadi, ƙa’idar ƴan gidan kenan za su taru a parlor ayi fira, su Ummie ta samu a parlor, “Leena wai ina Leesha, ko dai bata dawo ba? “Ummie ta tambayi Leena da ke saukowa daga stairs, “ a’a ta dawo fa, naji shigowar ta ɗazu” Leena ta faɗa tana saukowa, “Ishtar je ki dubo ta” Ummie ta faɗa, Pappy yace “a’a bari na dubo ƴar lele na ” tashi yayi ya nufi ɗakinta, a hankali ya buɗe ɗakin ya shiga, kwance ta ke akan gado, gashinta ya sauko gaban fuskarta, dan bazaka iya ganin fuskarta ba, murmushi yayi, sannan ya matso gabanta, gyara mata kanta yayi sannan ya mata peck a goshi, bargon jikinta ya ƙara gyara mata sannan yace “Allah sarki jajirtacciyar ƴata, ta gaji “, rufe ɗakin yayi tare dawowa parlor, “Pappy ina Leesha?” Leena ta tambaya, “tana barci, yau ta gaji ” Pappy ya faɗa , Leena tace “barci kuma, anya dai lafiya, Leesha bata barci da wuri, bata taɓa barci kamar yanzu ba, Pappy kaima ka sani”, shiru Ummie ta yi dan ita ma abun ya tsorata ta, Ishtar tace “fatana ace ba rashin lafiya za ta yi ba ” Zaina tace “to Allah ya sa haka ni kam barci zan yi”, Leena ma sallama ta musu, ɗakin Leesha ta shiga don tabbatar da ko lafiya, kwance ta same ta tana barci, zaunawa tayi gefen Leesha, hannunta ta kai kan goshin Leesha ta ji jikinta yayi zafi sosai, kallon ta tayi a ɗan firgice tace “Leesha “tashin ta, ta shiga yi amma ina ta ƙi tashi, da sauri Leena ta nufi ɗakin Pappy, “Pappy!, Pappy!” ta shiga kiran sunan shi, da sauri ya buɗe ƙofar, “me ya faru? “ya tambaya ganin yadda Leena ta rikice, “Leesha ce………. “, be jira ta ƙarasa zance ba ya wuce ta, da gudu, ya nufi ɗakin Leesha, Ummie da fitowar ta kenan ta ga Pappy ya wuce, Leena ma ta bishi, bin su tayi ita ma, a ɗakin Leesha ta same su, Pappy sai ƙoƙarin tashinta ya ke amma ta ƙi tashi, wayarshi ya ɗauka ya kira family doctor ɗin su, cikin gaggawa likitan ya zo, dubata yayi yace “ina tunanin ta firgita ne saboda wani abu da ta gani, haka ne yasa jikinta yin zafi, kuma shine dalilin sumar da tayi “, Pappy yace “minene ta gani haka”, likitan yace “Allah ne ka ɗai ya sani, sai ita, tana iya yuyuwa a mafarki ta gani, tana iya yuyuwa a fili ta gani “, Leena tace “amma doctor me zai faru zata samu sauƙi?”, likitan yace “kar ki damu ba wani abu bane, zata samu sauƙi kawai tana buƙatar hutu ne, zan mata allura insha Allah gobe zata samu sauƙi “, ajiyar zuciya Ummie ta sauke, allurai likitan ya mata sannan ya tafi, Leena ta kwana da Leesha a ɗaki domin jinyar ta, hankalin Pappy duk ba a kwance ya ke ba, da ƙyar Ummie ta samu ya yadda zai kwanta, amma be yi barci ba har safe, saboda tsoro, ji ya ke ina ma a ce zai ɗaukewa Leesha duk wani ciwo da damuwa na rayuwa da zai yi haka.

Da safe Leesha bata farka ba sai ƙarfe 10:30, buɗe idonta ta shiga yi, da addu’a ɗauke da bakinta, ji tayi kamar a jikin Leena ta ke, dan wannan ƙamshin a jikin Leena kawai za ta iya jin shi, kuma ita kaɗai za ta iya jin wannan ƙamshin, kawai dai ikon ne na ubangiji da yasa haka a cikin rayuwar su, kuma ya ƙarfafa alaƙarsu tafi komai mahimmanci a gare su, a irin yanayin nan yana wahala ka samu ƴan uwa masu son juna yadda Leena da Leesha ke yi, ta shi tayi tace “Leena me kike yi nan”, Leena tace “taya kike tunanin zan je wani guri a lokacin da kike buƙatar wani “, shiru Leesha tayi dan sai yanzu ta tuna abunda ya faru da ita a mafarki, Leena tace “ zaki iya faɗawa ƴar uwarki me ya firgita ki haka”, Leesha tace “nima ban sani ba Leena, ban fahimce mafarkin da kyau ba, kuma bazan iya baki labari ba, na tuna nayi mummunan mafarki, amma ban tuna me mafarkin ya ƙunsa ba “ta ƙarasa maganar hawaye suna zubo mata a fuska, “shhhh, Leesha this is not the right time to cry, I can’t bear seeing you in this condition, plss calm down” (shhhh, Leesha yanzu ba shi ne lokacin da ya dace kiyi kuka ba, bazan iya jurar ganin hawayen ki ba, dan Allah ki natsu”Leena ta ƙarasa maganar muryarta ma rawa, Leesha tace “but Leena am confuse”(amma Leena ba rikice) ta faɗa, Leena tace “koma minene ya wuce, be ma kamata kina yadda da mafarki ba, manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace “idan kayi mummunan mafarki to daga sheɗan ne “dan haka be kamata ki damu ba”, Leesha tace “eh haka ne, but Leena this is different(amma Leena wannan daban ne) dole na damu “, Leena tace “ki yawaita maimaita kalmar hasbunallahu wani’imal wakil, la’ilaha illa antas-subahanaka inni kuntu minaz-zalimin, Leesha koma minene zai zo da sauƙi”, Leesha tace “Leena ina yi sai dai na ƙara, nagode miki yanzu ya kamata kije kiyi wanka ki kwanta, nasan jiya baki yi barci ba, saboda ni, kiyi haƙuri kinji ƴar uwa, ni yanzu zan fita kinsan duk irin yau ina zuwa gidan marayu “ta faɗa tana tashi daga kan gado, Leena tace “bazan kwanta ba, tare zamu fita”, Leesha tace “kin fiye taurin kai wallahi, nace ki kwanta amma kin ƙi “, Leena tace “ba lokacin barci bane, ko kin fita hankali na bazai kwanta ba har sai naga kin dawo lafiya”, Leesha tace “amma Leena mafarki ne kawai “, “ni ban damu ba, abunda kawai na sani shi ne na baki kariya, na tabbata ko kece haka za kiyi to dan Allah kar ki hanani kula da ƴar uwata”, badan Leesha ta so ba, dole ta haƙura.

Tare suka shirya , suka sauko parlor, zaune ta sami Pappy yana cin abinci, murmushi ya bayyana a fuskar shi yace “Alhamdulillah, tun ɗazu nake so na duba ki amma Ummien ku ta hana, wai saina ci abinci tukunna “, murmushi Leesha tayi tace “yayi kyau, Ummie tana kular min da Pappy na, gara haka ai, am now healthy (yanzu na samu sauƙi)”, “really (dagaske) “pappy ya faɗa yana tashi daga kujerar dan ya riga ya gama cin abinci, murmushi Leena tayi tace “yes pappy, fita ma zata yi”, Pappy yace “ a’a Leesha baki da lafiya fa “, turo bakin ta tayi tare da ɗaura kanta a kafaɗar shi tace “trust me Pappy (ka yadda dani pappy) bazan jima ba zan dawo, nayiwa yaran alƙawari cewa yau zan dawo”, Leena tace “ shiyasa ma zan bi ta, Pappy kasan Leesha da marayu “, Leesha tace “Pappy su ma yarana ne, kasan ina ji da su, ina ƙoƙari ma da nake yin sati ban je ba”, Ummie tace “ka barta taje mana, tunda ka ga sun matsa, bayan haka ha tare da Leena zasu “, Pappy yace “ohk ba damuwa amma kar ku jima”, a tare suka furta “that’s our favorite man “kiss suka mishi a gefen kumatu su ka fita tare.


Gudu take shararawa akan titin, minti 30 ya kaisu gidan marayu, a gaban gate ɗin naga an rubuta, LEESHA URPAN HOME, da alama ita ta gina shi, buɗe mata gate aka yi, wow masu karatu zan so kuga yadda gurin yayi ya haɗu, bazaka ce gidan marayu ba ne, wasu yara ne a harabar gidan, da gudu su ka zo, “oyoyo Mammy ” suka faɗa da gudu suka rungume ta, “I miss you my kids” ta faɗa, “we also miss you (mu ma munyi kewar ki) “, su ka faɗa, “Aunty Leena” su ka faɗa tare da rungume Leena da ke tsaye gefen Leesha, tare su ka shiga ciki, ko ina da part ɗin shi, ko wane ɗaki mutum biyu, part ɗaya yana da ɗakuna hamsin, , ɗayan part ɗin jarirai ne aka kula da su, ɗayan part ɗin kuma yara ne daga shekara biyu zuwa sama, kuma duk suka girma za’a ƙara buɗe wani ɓangaren, gidan yana da part goma, tun Leesha tana ƙarama ta ke da jin ƙan marayu, komi ta ke da shi zata iya hana kanta dan maraya yaji daɗi, haka yasa tun da ta fara aiki a Abeer global company interprices bata taɓa riƙe ko nera ba, sai da ta kammala ginin wannan gidan marayun, kuma tunda ta zuba yara a ciki, wani bai taɓa kukan rashi a gidan ba, tana son su, ji ta ke yi kamar ita ta haife su, wani lokacin ma ita take zubar musu da hawaye saboda tausayi, a gurin nan suna da bambanci ra’ayi ita da Leena, Leena bazata iya jigilar kula da yara ba, sannan ma bazata iya yiwa kowa kyauta ba, idan kika ga Leena na kyauta to tabbas Leesha zata ba, ko su Ishtar, bayan su bazaki ga ta ba kowa komai ba, Leena bazata iya sadaukarwa saboda wani ba, amma Leesha zata iya saka kanta ƙunci dan kawai ta kyautata wa marayu, so dayawa ta sha zama bata da kuɗi kuma tana buƙatar su, amma bata taɓa bari gidan marayu wani ya rasa abinci ko sha ba, kayan kwaɗayi da sauran su, yadda zata ci mai kyau ta sha mai kyau haka suma yaran za suyi, shi ne yasa yaran suke matuƙar son Leesha, su ma zasu iya yin komai dan ita, ganin son da Leesha ke yiwa yaran yasa Pappy ya zuba kuɗi masu yawan gaske dan kula da yaran, da kuma siyen kayan ɗaki, wanda duk bayan shekara uku ake canza musu kayan ɗaki da fentin gida, maganar sutura kuwa, kai tsaye daga Abeer global company interprices ake basu kyautar kaya, abincin kuwa cikin albashin Leesha ake cirewa.

GASKIYA LEESHA JARUMA CE, DA SAMUN IRIN TA ZAI YI WAHALA, ANCE ƊAN ADAM TARA NE BE CIKA GOMA BA.

%d bloggers like this: