SAQAR SO 8 – QUEEN NISMERH


SAQAR SO – 8

🔱ṨÄQÄŔ ṨÖ🔱🔱
              ⚜️🗝️  ( love cub ) 🗝️⚜️

Mallakin :Queen Nasmerh
Marubuciyar 👇
1:Ayisherh
2:Mrs Bilal
3:Mrs Bilal continuation
4:Barrister Muhammad
5:Wani hanin ga Allah
6: Fayroz
7:Hajna

And now 8:SAQAR SO.

بِسم الله الرحمن الرحيم
~💞💞~

EPISODE 8- IN PAIN
°°°°°°°°°°°💗°°°°°°°°°°
Sauro duk ya cije ta, abun ku da farar fata duk jikinta yayi ja, gashi bata samu tayi barci idonta sun yi ja sosai, tun da safe aka zo, sai ji kawai tayi an buga mata abu akai, dafe kai tayi lokacin da jini ya fara zubo mata, “za ki faɗi gaskiya ko kuwa “, ɗago idonta tayi da har yanzu a tsats-tsaye suke, tace “mi kuke so na faɗa muku”, mutumin da ya buga mata kulki yace “ina kike siyen maganin shaye-shaye? “, “wallahi yallaɓai bani na sa shi cikin jaka ta ba, a taƙaice ma ban san yadda aka yi ya shigo cikin jaka ta ba”, ƙumm taji ya ƙara buga mata kulki a kai, wanda yasa wasu hawaye masu zafi su ka fara bin kuncinta, dukan ta aka fara yi ta ko ina, wasu ƙattin mazaje ne masu ƙarfi a jiki, dukan ta su ke yi kamar Allah ya aiko su, “ku dakata “mutum da ya tambayi Leesha ya faɗa, “kin shirya faɗan gaskiya” ya tambayi Leesha da ke kwance cikin jini, duk ta galabaita, “iya gaskiyar kenan “ta faɗa hawaye na bin fuskarta da ta fashe ko ina duk jini, umurni ya bada akan a cigaba da bata horo har sai ta faɗi gaskiya. Leena kuwa tun da safe take roƙon a barta taga Leesha amma su ka ƙi barin ta, daga ƙarshe hukuncin komawa gida ta yanke, idan ta je sai su dawo tare da su Pappy.


ABEER GLOBAL COMPANY INTERPRICES

A yau su ke kai kaya shagunan da ake siye, wanda dama duk Litinin su ke yin haka, suna cikin tafiya suka ga cunkoson mutane, sai hayaniya ake yi, haka yasa suka fito daga motar, wanda haka ya ɗauke su awa biyar a wajen suna daidaita matsalar, bayan an daidaita ne suka shiga mota su ka nufi inda zasu, kowane shago su ka kai musu kayan da su ke buƙatar. Pappy na zaune a parlor yayi shiru ya rasa abunda ke mishi daɗi, Ummie kuma tana kan ɗayar kujerar banda kuka ba abunda ta ke yi, Zaina kuma abun ka da ƙuruciya tayi barci, Ishtar tana zaune ƙasan carpet sai tunani ta ke, wannan ba halin Leesha bane, yau da cewa aka yi Leesha ta yi ma wani rashin kunya baza su yi musu ba, amma maganar ace Leesha ta ga maraya ta share shi, ta ga mara lafiya bata kula shi ba, ko kuma tana shaye-shaye ko bin maza ba wanda zai yadda dan Leesha bata yadda da irin halin nan ba, masu irin halin ma basa burge ta, ta yadda ace tayi wulaƙanci dan wannan yanayi ne na rayuwa kuma halitta ce, amma bata yadda da rashin jin ƙai ba, Leena ce ta shigo, da sauri Pappy ya tare ta, “Leena ina Leesha ", “ba su barni na ganta ba", Ummie tace “yi sauri ki yi wanka ", Leena tace “bazan iya wanka a irin yanayin nan ba Ummie, ina ƙonewa ne a cikin jikina, ji na ke kamar ni ce a yanayin nan, jikina yana bani Leesha na wahala yanzu haka", rungume ta Ummie tayi, ita kanta Ummie ba ta yi wanka ba, duk gidan ba wanda yayi wanka, maganar cin abinci ma bata taso ba ga tv na aiki amma babu wanda ya bi ta kanta. Wani ne ya faɗi ƙasa gaban wani shago kafin kice me ya fara fitar da kumfa daga bakin shi, mutanen da ke kusa da shagon ne su ka yo kanshi, da sauri aka yi rushing ɗin shi zuwa asibiti, mamaki ya kama su yanzu fa ya gama shan chocolate ɗin Abeer global company interprices, assibti su ka nufa, in da aka haɗu da mutane sun cika asibitin ta ko ina, sai kawo mutane ake yi kumfa na fita a bakin su, nan likitoci su ka shiga aiki, in da aka gano mutanen sun ci guba iri ɗaya ne, nan take aka dinga mutuwa a asibitin, mutane su ka fara tattaunawa, akan yadda aka yi mutune za su sha guba iri ɗaya ina suka same ta, nan ƴan uwan waɗanda suka mutu su ka fara magana, wasu su ce shinkafar Abeer company su ka ci wasu kuma su ce lemu, kowa da abunda ya ci, daga ƙarshe dai aka gane company ɗin ne su ka sa guba a cikin kayan abinci nan hayaniya ta hargitse, kamar daga sama sai ga ƴan jarida suna shigowa, tambayoyi ake yiwa mutane, nan aka fara tambayar wani “me zaka ce game da wannan abun da ya faru ", mutum yace “ai ba abunda wannan yarinyar bazata yi ba, yadda ta tsani talakawa zata iya kashe mu ma", ɗan jaridar yace “wace yarinya kenan ", mutumin yace “Leesha Abeer mana, mai kula da company ɗin, bayan haka ma an kama ta da powder iblis", ɗan jaridar yace “ahh haba mu bamu da labari ai ", mutumin yace “ai tana gidan horon sojoji da ke cikin garin nan, idan kuna so ku je ku ɗauko rahoto", duk abun nan da ake yi akan idon su Pappy da tunda aka fara labarai su ka mai da hankalin su, ba ƙaramin tashin hankali su ka shiga ba lokacin da su ka ga gawar mutane, an rasa rayuka sosai har mutum 150, agidan marayun Leesha ma yara 7 sun mutu da jarirai uku, wanda in an haɗa da shi rayuka 160 aka rasa.

Da sauri Pappy ya tashi “Aisha ta shi mu tafi ba muga ta zama ba, wannan laifin duka Leesha za a ɗaura ma shi “, tashi su ka yi, har da Leena da su Zaina, mota ɗaya suka ja, malam Adamu ya ja su, yau duk son surutun Adamu sai da yayi shiru, dan shi kan shi ne ji daɗi ba, hawan su kan babban titi yayi dai-dai da zuwa dandazon mutane, tarasss! Kake ji ƙarar jifa, jifar su a ke yi, ba abunda ke tashi sai muryar mutane “Allah ya isa macuci azzalumi, ka cuce mu ka raba mu da masoyan mu, ina munafukar ƴar taka ta fito In bamu kashe ta ba “, kowa haka yake faɗa, sai jifar su ake yi, har gidan horo, duk motar ta fashe, Ummie sai kuka ta ke yi, Leena kuwa ta ƙule, ji take ina ma a barta ta fita a matsayin Leesha in kashe ta za su yi sai a huta. A harabar gurin suka aje mota, su kuma mutanen ganin an iso gurin sojoji yasa su ka dakatar da jifar da su ke yi, “ke bamu Leesha mu kashe ta, mu ma mu ɗau fansa " su ke faɗa, Leena da ta riga ta kai muƙura, idonta sun kaɗa sun dawo kalar ja, ta juyo fuskar nan haɗe, tace “gani ku kashe ni", ai kuwa mutane su ka yi cikin ta dan duk tunanin su Leesha ce, dukanta su ke yi ta ko ina, da sauri Pappy ya yo cikin su, “ku dakata, wannan Leena ce ba Leesha ba, ke Leena baki da hankali ne ko me " ya faɗa yana share hawayen shi, “Pappy ka bar su, su kashe ni, ni na gaji da jin wannan abun, ku kashe ni a maimako Leesha!" ta faɗa da ƙarfi, wanda yayi sanadiyyar zubowar hawayen ta, cikin kuka ta ke magana “ya ishe ni haka Pappy, kasan irin ciwon da na ke ji, ina ji ina ma na mutu kafin yau, ban taɓa tunanin Leesha zata faɗa cikin irin yanayin nan ba", wani saurayi yace “ƴar uwarki bata hali, shaiɗan ce a cikin suffar mutum, bata san darajar rayuwa ba, wannan shine dai-dai da ita, kuma.........., “ya isa! Sakaran banza dabba kawai "Leena ta katse shi da wannan maganar, miƙewa tayi tace “baka da hurumin da zaka tunkari Leesha da baƙaƙen maganganu, shekara nawa company ɗin Abeer su ka ɗauka suna kyautata muku, suna sarrafa abubuwa, ba'a taɓa kashe kowa ba, sai yanzu, saboda irin butulcin ku shine kuke jifar mu, ku bari shari'a tayi hukuncinta"ta ƙarasa maganar suna shigewa ciki.

Leesha kuwa ta yi liƙis, ko tashi bata iyayi, gashi labarin abunda ya faru yau a garin barno ya zo kunnenta, dan saboda shi ne aka sake naɗa mata duka, tana cikin zafi da ƙunar rai, tabbas wannan shine yanayi mafi tsauri a gare ta, rayuwar ta da martabar ahalinta ta ruguje, Abeer global company interprices ya durƙushe, ba abunda ya rage mata yanzu, gashi gidan marayu ma an rasa rayuwa, duk wa yake wannan ne? .

Ganin yadda aka ma Leesha duka yasa Ummie fashewa da kuka, ko tashi bata iya yi, tana ganin su amma bazata iya tashi ba, sannan ko idon ta bata iya buɗewa da kyau, “Leesha! “Leena ta faɗa tana fashewa da kuka, ɗaga hannu kawai Leesha ta iya yi, tana murmushi mai haɗe da ƙuna, da hawaye, kuka kawai su ke yi, hawaye ke kai kawo a kuncin Pappy, yau ne karo na farko da ya ji ya tsani duniya, duka kuka su ke yi, Ummie tace “idan su ka cigaba da dukanta zasu iya kashe ta fa, Alhaji ka yi wani abu “, “Aisha kinsan nan gurin basu karɓar cin hanci ya kike so nayi, dole ne mu samu hujjoji, kuma bamu da su ko kaɗan, ya kike so nayi, kin fi kowa sanin yadda na ke so Leesha, ji na ke dama nine a gurin nan”.

A ɓangaren Yousuf kuwa, waya ya ke yi cikin kwanciyar hankali, “yes that’s very good na ji daɗin aikin nan, kowa zai samu kaso mai tsoka, ku zo gobe ku same ni, a office “, kashe wayar yayi yana mai sakin wani shu’umin murmushi, “ke ba kince mara kunya bace, to ga dai-dai ke kin haɗu da shi, wayyo Leesha, na so ace kin san wanene Yuosuf Abdallah, amma kar ki damu yanzu kin fara sanin wanene ni Yuosuf, wasan yanzu aka fara” ya ƙarasa maganar yana fashewa da wata muguwar dariya.

Ni kuwan nace oh Allah na mutane, mutane na tukane, tukane na fashewa 😂😂

Muguwar miya bata ƙarewa cikin tukunya dai.

Anan zan dasa aya………… ✍️

ALQALAMINA✍️YAFI KO WANE TAKOBI ⚔️KAIFI

%d bloggers like this: